30

1.3K 84 0
                                    

30.Aikuwa tashirya tsaf. Batayi wani kwaliya ba. Dogon riga tasa tayi nadin kanta. Tashafa lipglow tafito. Ta isa gun daidai karfe 3:40  tako ci saa yana zaune agun. Kyakyawan saurayi. Ga glass dinshi na likitoci. Tana hangon fararen idanunsa. Namiji mai cikan kamala. Son kowace mace kin wacce tarasa.takaraso cikin takunta na kasaita taja kujera tazauna . Tana kallon yatsunta. Ina wuni tace dashi yayi murmushi sosai sannan yace lafiya affy. Tadago takalleshi don dai tasan affy kam ahmed ne kecemata  . Saitace ya aiki. Lafiya lao. Yadan murmusa sannan yace jiya nagagara bacci inata tunaninki. Dakuma dokin yau taxo ko zanyi tozali dake. Tayi murmushi sannan tace gashi Allah ya kawomu ai  . Nan ya gyra zama sannan yace. Afrah sunana  aminu ibrahim barde  . Daga billiri nake. Zaki iya bani labarin rayuwanki?. Tace  no kaidai kabani naka. Yakalleta sannan yace ai tarihin rayuwata nahade danakine. Takalleshi sosai. Takura mishi ido. A karo nafarko dataga alamun tasan fuskanshi awani guri anma tamanta. Tadan juya sannan tace ni daka ganninan. Banda wani tarihi wanda zai amfaneka. Yayi murmushi yace to ni barin baki lbrn rayuwanki. Nafarko kimayar da rayuwanki shekara goma sha uku dasuka wuce.. zaki iya tuna gun wata inna mai siyar da abinci kina mata wanke wanke?. Harwataran mai rake yaganki yaxo yatafi dake gydansu?. Bakiji dadin zaman gydanba anma sanadin haka ya kwasheki yanema miki aiki a gydan galadima?. Sai alokacin yadago yakalleta. Ya tsorata da yanayin daya ganta kuka takeyi sosai bakadanba. Hakan yasa yafara bata hkr. Kiyi hakuri afrah i neva mean to hurt u. Anma ina afrah tayi nisa tadau akalla minti talatin tanata kukanta baihanataba. Shima yazauna yayita zubar danashi kwalan. Yana tunanin yadda rayuwa zata kasance musu. Can ta nisa tace. Hakika ya aminu bazan taba mantawa dakai arayuwataba. Akullum nayi sallah nakan roki Allah yabaka abunda kakeso yakareka. Kaine sanadin rayuwan danake ciki. Bayan mundawonan. Nasamu duk suna sona bansamu matsala dasuba. Harnayi makaranta nagama. Inasamun gata daidai da yanda yar gydan zata samu. Wannan bayin Allah. Bansan dame zan saka musuba. Yace to ya akayi aka kawomin ke asibiti?. Sannan wanene ahmed G agunki. Tadan nisa kafin tace shine lokaci na farko dawasu yanuwansu sukamin gori. Hakanne yahaddasamin bacin rai sosai  kasancewar nasa abun araina. Yayan amana kuma shine wanda zan aura. Wani bakin ciki yarufeshi  shikam idan yarasa afrah to tabbas zaiyi bankwana da rayuwa. Sama da shekara sha uku yana kiwon soyayyanta. Har yau baida budurwa  tace ban labarin bayan rabuwa. Yadan nisa kafin yace bayan tafiyanki. Munyi asara sosai. Don jarin inna yakare . Nima raken nawa bajari. Hakan yasa wani baffanmu anan abuja yakwashemu yadawo damunan. Yasani nacigaba da makaranta. Ba yanda banyiba kozan sami unguwan dakike. Anma bansamu damaba. Ina shekarata ta karshe inna tarasu. Saura bilki ne kawai. Nan afrah ta tausaya masa sosai ba uwa ba uba. Fatanta Allah yahadashi da mata nagari.. kozata debe masa kewansu

KECE GUDALLIYA (2013)Where stories live. Discover now