45.aiki kam tubarkallah anyishi lafiya angama lafiya kowa yamanta da maganan fake aminu. Anata lafiyan afrah da ahmed ne . Washegari akabarsu suka shiga don sugansu. Haryanxu basu farfadoba. Sai likitan ya umurci dasu barsu tukun sugama samun dadin jikinsu . Adda salma tarikice sosai daga ita har mijinta daganan kadai zakasan yadda takeson yartata.lokacin data farfado salati tayi tare da kiran sunan ahmed. Shikuwa ahmed sunanta ne abakinsa tun yanabacci harya farka . Sumbatun sunanta yake. Adda salma takalli hajiya babba kasancewar su biyune adakin. Tace don Allah hajiya kiroki baba. Yataimaka wa yarannan. Wlh sunason junansu. Hajiya tace kojiya inanan ina rokonshi insha Allah zai yadda. Nandai sukadan tattauna kafin likitan yashigo sukamasa bayanin farkawansu nan yace ansamu nasara komai yayi daidai. Yanxu dai afrah ta kiyaye lafiyanta. Shima ahmed haka gudun kar dayan dayarage mada yasamu matsala.satinsu uku a ka sallamesu. Alhamdulilah sunsami sauki sosai.mutane kuwa kaman me kowa naxuwa gaysuwa dana Allah da annabi dana yan gulma. Alokacin aka tado maganan fake aminu. . Galadima yasa asakosa tare da umurtarsa yasaki afrah. Yajuya yacr shifa yanason matarsa bawanda ya isa yasashi sakinta. Galadima yace inbaka saketa don Allah bama zaka saketa don wahala. Nan yasa aka mayar dashi ana ganamishi azaba. Gashi kuwa sai surutu yake. Ahaka harya fadi abinda yayiwa danuwansa aminu yabayyana gaskiya. Da hanzari akaje dubo inda yayi kwatance akasamu Allah yadau ransa. Tunda dama yana biyan wasune suna mika mishi abinci. To tun randa yashiga prison sukuwa basu kara leka aminuba. Satinsa uku ba ruwa ba abinci. Anma abun mamaki yana sujjada suka tarar dashi. Dasuka motsashi ne suka tabbatar ya mutu. Aikuwa maganan ya birkita kuka. Babban yaya yace haba! Abun zai damen ince mutumin dakeson afrah tayaya zaina misbehaving akan wani zai bata . Namfa aka daukaka case. Karshe kotu akeson shiga dashi. Don duk axaba yaki sakin afrah. Ga uwa uba kisan da aka tarar yayi. Wannan kenan!