Farko.

13.4K 557 13
                                    

Assalamu Alaikum!

Thanks for following me in brothers and sisters of the same generation!

READ VERY IMPORTANT.

Before this trip began, I've an important confession to do. Actually, I'm not in any way a professional writer, kawai dai ina dan rubuta shirmen cikin kwakwalwata ne duk lokacin dana sami dama cox I tynk it's fun, so I wont be updating daily, or weekly like many writers here, because I'm still working on the story and i don't have it all written down so updating ya danganta da lokacin dana dan sami crazy ideas dina, plx don't expect mush...!

Komai nisan dare, labari ne da ya faru a zamani irin na da, mai dauke da rayuwar sarauta, mulki, soyayya da kuma sihiri irin na wancan lokacin. Zamu iya saka shi a layin "Romance and Adventure" na Hausa. Ina fatan zaku ji dadinsa.

Vote and comment please!

"kyau ko dukiya basa bada soyayyar mutane ta gaskiya, hali na gari shine ja gaba a komai."-Huzail.

HALMAN.

Iska ce mai sanyi ke kadawa tana wasa da gashin kanta dake jingene a jikin wani dutse, ta rufe idanunta a hankali yayin da take jin karar tekun dake ambaliya a gabanta tamkar busar sarewa mai dadi, duk da cewar a tsugunne take amma a haka wani nauyayyan bacci yayi awon gaba da ita cikin abinda baifi dakika ba, ta janyo hannunta dake cikin kwandon audugar dake gabanta, ta dunkule shi a kirjinta cike da jin dadin baccin da ba kullum take samunsa ba, sau da yawa sai dai ta rarraba shi a tsai-tsaye cikin tarin ayyukan da suka zame mata dole.

Sai dai, da ace ana sabo da wuya, da ya isa tsawon shekara guda da tayi a kurkuku yasa ta saba da rashin bacci taki biyewa daddadar iskar dake shiga koina a jikinta.

Iskar ta kara karfi har ya zamo tana iya daga gashinta daga jikin dutsen tana wasa dashi a sama. Bakinta ya motsa cikin murmushi lokacin data hangi fuskar wata 'yar dattijuwa cikin baccin nata.

"Yalla Rayyana, jeki taro mahaifinki."

Dattijuwar tace da wata 'yar yarinya dake wasa da 'yan tukwanen k'asa daga gefen inda take tura wuta a cikin wani madaidaicin daki mai cike da tarkace.

'Yar yarinyar ta dago da sauri ta ruga zuwa wata kofa ta katako, ta fita da gudu zuwa barandar gidan inda ta hango mahaifin nata tafe daga nesa akan jakinsa, kamar koyaushe, ya lodo tarin ciyawa daga bayan jakin, tun daga nesan yake dago mata hannu yayin da ita kuma ta hau tsalle cikin murna iska na wasa da dogon gashinta har yana kokarin rufe fuskarta.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now