SHA HUDU.

1.6K 152 5
                                    

Vote and comment please!

"Abin da na tsana a duniya guda uku ne, kaskantar da kaina a gaban mutane, bada hakuri lokacin da banyi laifi ba, da daukaka mutanen da basu dace ba a cikin rayuwata."-Zafreen.

--------

Karar bugun zuciyarta ya k'aru kamar wadda tayi tseren ceton ranta, wani dunkulen abu ya tsaya mata a makwogwaro, ta rinka jin tamkar an toshe wurin fitar numfashinta ne k'irjinta yayi mata nauyi, ta kasa janye idanunta daga yadda suka had'e da nasa tsukakku, jira kawai take taga abinda zai biyo baya.

Huzail dake tsaye a gabanta, ya had'e girarsa cikin mamaki shima yana kallonta.

A lokaci daya fararen idanunta suka juye masa zuwa irin wadanda ya taba sani a baya, idanun da ya kasa mantawa dasu tsawon shekara guda, sai dai wadancan masu dauke da tsoro ne wadannan kuma cike suke da fushi, wadancan masu dauke da roko ne, wadannan kuma cike suke da rudani.

Amma yadda take faman kiftasu, haka wadancan ma suka dinga kiftawa ba kakkautawa, kuwwa da iface ifacen mutanen wancan lokacin suka dawo cikin kunnensa, ya dinga jin kamar zai ga gilmawar itatuwan wutarsu lokacin da take manne a jikinsa daga bayan wasu manyan darurruka.

Ba zai iya kwatanta kamannin wannnan da kuma ta baya ba, don a wancan lokacin idanunta ne kawai a bude, fuskarta rufe take da wani bakin abu da iya zirin idanunta kawai ake gani, amma a yanzu siririyar girarta, dogon hanci da kuma d'an bakinta gabadaya a fili suke, dukkaninsu a tsuke kamar suna jiran abinda zai ce.

Abinda zai ce. Hakan yayi saurin dawo dashi daga tunanin da ya tafi, yayi gyaran murya sanda idonsa ya hango masa wani dutse dake gefe, ya matsa ya janyo shi zuwa saitinta sannan ya zauna yana fuskantarta sosai.

Ta fahimci kallonsa, kallo ne na rashin yarda, kamar yana shirin karasar da zargin da ta gani tun farko cikin idanunsa, ta sauke gashin idanunta kasa yayin da zuciyarta ta shiga tsere, bata son ko kadan ya gane ta, hakan shine abu na karshe da take fatan ya same ta a yanzu, amma ta san me zata yi, zata nuna masa banbancin halayenta da waccan don ta juyar da tunaninsa, kwarai hakan zata yi, Ta shiga gyara zama hannunta na dama na lalube cikin yashin wajen, koda zata sami wani abu da zai taimaka mata a matsayin makami, in bukatar hakan ta taso.

Ya sake yin gyaran murya sannan yayi shiru, kamar ba zaiyi magana ba, sai kuma taji yace.

"Na dade a wajen nan, har nayi duk abinda zanyi, baki ma san nazo ba."

Abinda take jira ya fada kenan, amma bata san me yasa ba, sai taji kamar wani abin daban ya fada, ko don yadda muryarsa take da zurfi ne? Ko kuma yadda ya fidda kowanne harafi a hankali.

"Kin tabbbata nan ne a rubuce jikin takardarki?"

Har cikin zuciyarsa yaso ta amsa da akasin hakan don tun lokacin daya dauko takardar data banbanta da ta faris, yake fatan a hada shi da wanda zai fahimce shi, don a yadda tsarin yake, babu abinda mutum daya zai iya a gasar gabadaya ba tare da abokin tafiyarsa ba. Hakan yasa tun lokacin da ya karaso wajen ya ganta yake tunanin yadda komai zai tafi masa ba tare da an samu matsala ba.

Zafreen ta cigaba da kallon yatsunta, ba tayi magana ba. Me yasa zata yi shiru? Ita da take shirin nuna akasin halayenta, kamata yayi tace shi yakamata ta tambaya hakan ai, tunda a wajen yazo ya sameta.

Watakila ganin tayi shirun ne yasa shi cigaba da magana.

"Lokacin da suka tara mu dazu na san kinji suna fadin cewa kwana dari kawai muke dashi mu gama abinda za'a tura mu, toh samo wannan dutsen da kuma inda zai kaimu shine mataki na biyu kuma abinda zamu yi cikin kwanaki dari, ba wai gini ba."

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now