SHA BAKWAI.

1.4K 148 2
                                    

Vote and comment please!

"Idan ka kasa cire tunanin wani daga zuciyarka, watak'ila an halicce shi ne don ya zauna a tunaninka."

-

-----

"Na fada maka ka tsaya na huta!"

Zafreen ta fada da dusasashiyar muryarta tana kokakrin kamo huzail dake gabanta, amma kafafafunta sai gurdewa suke cikin wasu fararen dutsuna dake barbarje a koina na wajen. Tun bayan fitowarsu daga cikin wannan ruwan, yini guda kenan suna tafiya basu tsaya ba.

Huzail ya dan girgiza kansa jin yadda muryarta ta fita a dusashe, da alamu har yanzu ruwan data shaka bai gama fita daga kunnuwanta ba, ya fada mata yadda zata yi amma taurin kanta yasa taki saurarensa.

"Idan ke zaki huta, me yasa sai ni na tsaya." ya fada yana cigaba da tafiyarsa.

"Saboda na san kafin na gama hutawa kayi nisan da ba zan iya kamo ka ba."

Ya dan waigo da kansa.

"Nayi zaton ai ba son tafiyarmu tare kike ba."

"Ba zato kake ba, kaima ka san ina binka ne don ban san hanyar inda taurari ukun suke ba."

Ganin bai saurareta ba yasa ta d'age kasan rigarta ta karaso da sauri ta sha gabansa, ta tsaya daf dashi, ya matsa gefe zai wuceta tayi saurin damke hannunsa na hagu, ya kalli hannun nasa sannan ya dago ya kalli yadda ta ware fararen idanunta cike da fushi. Irin wannan karfin halin zai taimaketa a wajen nan.

"Idan na bada umarni, a lokacin ake yinsa."

Ya dage girarsa daya.

"Idan kika bawa wa umarni?"

"Kowa waye ma." ta fada tana kallon cikin idonsa.

"Ba'a kin bin umarnina, koda kuwa numfashi nace a daina yi."

Har yanzu muryata a dashe take, hakan ba karamar illa zai jawo mata ba, yaji kamar ya sake fada mata yadda zata fitar da ruwan, sai kuma ya fasa yace.

"Tun yaushe kika yarda cewa zan dinga bin umarninki?"

Ta hade rai tace.

"Tun lokacin daka yaudareni ka kawo ni nan, ka kuma ce min ba zan iya komawa ba."

Ya kalli yadda dan karamin lebbenta ke motsawa cike da fushi, idan ta rufe shi, wani zai yi tunanin cewa da tayi magana da yawa zai yage ne.

"Ya kamata ki san cewa da rayuwar mafarkin ki na baya da yanzu ba daya bane."

"Rayuwata ba mafarki bace, kaddara ce ta kawo ni nan kuma zan koma da yardar ubangiji."

"Ba yardar ubangiji kadai ba, sai kin hada da naki kokarin kema."

"A lokacin da nake wannan kokarin ne ka yaudareni ka kawo ni nan."

"Baki da tunanin da zaki gane cewa zamanki a can ba mafita bane, nan wajen shine kadai inda zaki iya sa ran samun hanyar komawa rayuwarki in kin jajirce, ba wai tun yanzu kina neman hutu ba."

Ya fadi kowacce kalma dalla dalla.

Iskar dake kadawa ta tarwatsa gashinta a sama yayi baya. Ta girgiza kanta har a lokacin tana kallon idonsa.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now