SHIDA.

2K 226 4
                                    

This one is for my Aunty, Summayya Abdulkadir takori nd her new born baby, Allah ya raya mana 'Aleem'!


Vote and comment please!

"Ruhina da Burina, wasu abubuwa ne dake tafiya tare, daya baya iya aiki saida daya, idan har na rasa burina toh tabbas na rasa Ruhina."-Zafreen.

MURAK

Dakin baccin Zafreen

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Dakin baccin Zafreen.

"Murmushin da sarauniya tayi lokacin dana fada mata isowar yarima Aaryan, na dade banga irinsa ba ranki ya dade, murmushi ne da ko lokacin da abubuwa suke daidai, da wuya tayi shi." Cewar raila.

Tana zaune ne daga wani gefe na dakin baccin zafreen tana jera turarukan gashi da aka kawo a safiyar daga garin 'Garmal' a cikin wani karamin kwando. Bayanta, wata katuwar taga ce da aka lullube ta da jan labule mai kusan hawa uku kasancewar kusan komai na dakin ja ne da kuma adon ruwan zinare. A duk dakunan baccinta guda shida, zafreen tafi son wannan kalar saboda hakan ne ma tafi yawan amfani dashi akan sauran.

Gimbiyar na kwance akan wani  zagayayyen gado mara girma sosai dake tsakiyar dakin, an lullube jikin gadon da wani tattausan mashimfidi kalar ruwan zuma.

Doguwar riga ce a jikinta ruwan makuba (maroon) mara nauyi mai saukin ado...hannunta rike da wani dunkulen abu na zinare an cike cikinsa kuma da wasu kananun zinaren kamar giman tsakuwa, da ta girgiza shi, sai su hadu su bada wata kara.

Ta rufe idanunta a hankali tana sauraron bayanin raila, sarai kwakwalwarta ta gane me take nufi da tace "lokacin da abubuwa suke daidai" wani zamani ne daya shude a shekaru kadan da suka wuce, wato lokacin da mai martaba bai sanya gasar dake dawainiya da rayuwarta a yanzu ba.

"Ni kaina ban daina mamakin yadda kika canja shawara a lokaci guda kika karbi baikon yarima Aaryan ba, har kuma kika yarda da zuwansa garin nan ranki ya dade." Raila ta fada tana nufar wani katon ma'adani inda ake jera kwandunan turaren gimbiyar.

Zafreen ta bude idanunta ba tare da tace komai ba, ta zubawa abin da ke hannnun ta ido, duk ta san dabarar data ke shirin aikatawa, har yanzu itama zuciyarta ta kasa daina mamakin yadda ta yarda mai martaba yasa tawagar galadima suka karbi baikon Aaryan kwanaki bakwai da suka wuce, duk da kuwa tarin dalilan da suka sa dole tayi hakan.

Tsawon shekarun data taso a duniya, mahaifiyarta bata taba fushi da ita irin ranar data shaida mata baxa ta iya karbar baikon Aaryan ba, tun daga ranar bata kara ganin walwalarta ba, bata kara yi mata murmushi ba, bata kara hira da ita ba sannan bata kara nemanta ba, har ta kai ma ta sa kuyangi su hana ta shiga turakarta a wata ziyara da ta kai mata, a ranar ta yini da mamaki, kwakwalwarta ta kasa gasgata wai yau mahaifiyarta ce bata son ganinta, ta tabbata ba karamin baci ranta yayi ba hakan yasa a daren ta zauna ta yanke shawarar da take ganin zata fidda ta, don a washegarin ranar shine damarta ta karshe.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now