UKU.

3.4K 245 2
                                    

This chapter is dedicated to the first viewers of KND, khameelarh, mss_gara, deeza1210, khada13...guys, i appreciate your votes!

Vote and comment please!

"Kowanne mutum rayuwarsa a cike take, baya yiwuwa ace sai da soyayyar wani zaka zama cikakken mutum, hakan wata ma'ana ce ta rauni."-Zafreen.


MURAK.

Sanye take cikin farar doguwar riga wadda ta tsaya iya gwiwarta, daga kasa kuma wani siririn wando ne da ya kwanta sosai akan fatar ta saboda tsananin laushin yadin da babu ado ko daya a jiki, amma hasken ranar daya bude a wajen, yasa shi wani irin kyalli mai d'auke hankalin mai kallo.

Kamar yadda ta nannade gashin kanta da wani farin yadi, haka fuskarta rufe take duka da yadin, sai iya ramukan kyawawan  idanunta kawai ake gani wanda dogon gashin jikinsu, ya sauko har ana iya ganin kwanciyarsa akan bakin yadin dake k'asan idanunta.

Ta mike dogon hannunta na dama wanda ke rike  da wata baka da akayi karfenta da danyan ruwan azurfa yayinda ta ja dayan hannun baya, dogwayen yatsunta harde cikin farar kibiyar, wadda ta saita ta a mike daga cikin bakar har zuwa tafiyar taku arba'in inda aka ajiye wani allo mai dauke da zagayaiyun zanuka cikin nau'in kaloli daban.

Wajen tsit yake tamkar babu kowa ta yadda har kana iya jin k'arar yadda iska ke kadawa daga kowanne gefe duk kuwa da tarin bayi maza da mata dake gurin, kowanne tsaye bayan fararen labulayen da suka yiwa wajen k'awanya, wanda in ka hago wajen daga sama zaka ga ita kadai ce a tsakiyar filin yayin da daga kowanne gefe, banda can gaba, bayi sun zagayeta sai dai da wasu fararen labulaye a tsakanin su, wandanda iska ke faman kadawa a hankali.

Sai da ta tabbatar ta saita kibiyar a daidai ramin tsakiya na allon sannan tayi niyyar harbawa, har tayi shirin sakin kibiyar amma k'arar tarin da taji daga gefenta na dama ya janye hankalinta, ta juya idanunta tana kallon wajen yayin da yatsunta suka subuce, kibiyar ta fita da Sauri cikin matsanancin gudu ta fadi a gefen allon.

Ta dawo da idanunta wajen tana kallon abinda ta share lokaci da yawa tana kokarin yi, ya tafi a banza.

Hannu tasa ta janye yadin da ta lullube fuskarta, kyakyawar surar fuskar da take ji da ita fito fili dauke da alamun kananan gumi akan fatarta wanda nan take suka fara sulaluwa zuwa habarta saboda tsananin santsin fatar da bata iya rike komai a jikinta. Dogon gashinta dake nannade da a cikin yadin shima ya sauko har zuwa cinyarta.

Wata baiwa ce ta karaso da sauri dauke da wasu kananan bargo (towel) ta durkusa Har kasa kafin ta dago ta fara goge mata gumin, yayin da wata baiwar ta biyo bayanta dauke da kofin sassanyan lemon inibi, itama ta durkusa kasa sannan ta mika mata, Har a lokacin ba wanda yayi magana a wajen don kowa ya kwana da sanin ba'a koda yaushe shugabar tasu ke bukatar jin muryar bayin ta ba.

"Na tuba na tuba..ranki ya dade, na tuba madogarata, aikin kuskure ne ki min gafara, matsananciyar rashin lafiya nake fama da ita..ba zan taba yin hakan da gangan ba, afuwarki nake nema Jagorar al'umma" Cewar wata dattijuwar baiwa dake daya daga cikin masu gadin wurin, muryar ta na rawa, yayin da ta kwanta akan cikinta.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now