BIYU.

3.4K 269 10
                                    

( Hoton garin Halman

Oups ! Cette image n'est pas conforme à nos directives de contenu. Afin de continuer la publication, veuillez la retirer ou mettre en ligne une autre image.

( Hoton garin Halman.)

Garin halman, na daya daga cikin manyan garuruwan k'asar 'Parvez' kuma a duk kasar babu inda ya kai su albarkatuwa da kyan shuka, k'asar garin nada mutukar kyau da saurin yado. Saboda haka yawancin arzikin garin gaba daya ya ta'allaka ne akan noma, ta yadda har su kanyi cinikaiya da wasu kasashe dake makwabtaka da 'Parvez'.

Birnin halman na daga cikin alfaharin Parvez ta harkar noma da kuma jarumta a yaki, domin kusan duk manyan jaruman matasan da ake alfahari dasu a kasar sun fito ne daga garin halman, a yakuna da dama da akayi tsakanin 'Parvez' da wasu kasashen, garin halman yasha zama jigon nasarorin da aka samu.

Rayuwar garin mai sauki ce kasancewar adalin shugabansu, 'Sarki marzuq' mutum ne mai tsanani son al'ummarsa da kuma son adalci a mulkinsa, yana da kirki da saukin kai, sannan a tsawon shekaru talatin da biyar da yayi akan mulki, da wuya kaji ranar da jama'a suna koka dashi.

Kafin hawan sarki marzuq mulki, mahaifinsa yayi masa aure da 'yar sarkin garin agsin, wanda suke makota da garinsu, sai dai shekara biyu bayan auren ta rasu a wajen haihuwar danta 'HAFID'.

Bayan hawa mulkinsa ne ya auri sarauniya masiya wadda ta kasance Baiwa da aka kawo masa talla saboda kyaunta, aurensu ya zama baban abin magana a kasar Parvez gabadaya wanda har shugaban kasar, "Nur Jaahan" yaso hanawa da cewar hakan zai rage darajarsa a idanun al'umma, Amma kwararan dalilan da sarki marzuq ya kawo yasa suka amince masa.

Yarima hafid ya taso cikin gata da kulawa, na mahaifinsa kuma al'umma, wanda hakan ya haifar masa da mummunar akida ta girman kai, gadara, da kuma nuna kaskanci gana kasansa. A lokacin da yake amfani da damarsa na cewar shine kadai yarima a kasar, a lokacin sarauniya masiya ta haifi 'YARIMA HUZAIL'.

Duk da karancin shekaru irin na yarima hafid a wancan lokacin amma zuciyarsa tayi baki da labarin haihuwar huzail yana ganin tamkar an yanke masa damar samun nasarori ne nan gaba a rayuwarsa.

Yarima huzail ya taso cikin tsananin soyayyar mahaifinsa wadda ta samo asali daga son da yake wa mahaifiyarsa, Wanda hakan ya dada sawa yarima hafid jin haushin dan'uwan nasa don yana ganin cewar ya kwace masa fada a wajen mai martaba, sai dai baya nunawa ko don girman da yake ganin mahaifiyarsa dashi, kasancewar ita ta raine shi kuma ta sa masa sunan da kowa ke kiransa dashi wato "Yarima Babba"

A lokacin da yarima huzail ya fara girma, sai kusan soyayyar al'umma ta koma gare shi, domin banbancin halayensa dana yarima hafid.

Huzail ya kasance mai saukin kai,yayin da Hafid yake da girman kai.

Huzail yana da son jama'a amma yarima Hafid baya son mutane.

Huzail mai daraja mutane ne, amma kaskanta al'umma shine abinda Hafid ya tashi akai.

Sarauta itace abin alfaharin Hafid yayin da Huzail kan manta shi jinin sarauta ne.

Sha'anin mulki da samun mukamin sarauta sune burin Hafid yayin da Huzail yafi maida hankali kan fada da sanin dabarun yaki, Wanda hakan ya samo asali daga alkawarin daya da daukarwa mahaifiyarsa na ganin bayan 'SADANU'.

Lokacin da huzail ke kokarin koyan dabarun yaki, yarima hafid ya dauki hakan akan shirme don a sannan baya wani aiki sai dai ayi ta dora masa buhun jikakkiyar kasa, yayi ta kaiwa da kawowa har rana ta fadi, sai da jikinsa ya jure da wahala sannan ya fara koyan ainihin dabarun fada a garin agsin inda kafin ya kai shekaru goma sha biyar ya goge a harkar fada har ta kai ana iya kwatanta shi da manyan jaruman Halman, Amma lokacin da ya kai shekaru ashirin, sai ya zama duk a kasar Parvez gaba daya, mutum biyu za'a kira sama dashi a harkar jarumta, Amma bayan su, kowanne jarumi kasa yake dashi, hakan yasa garuruwa da yawa neman taimakonsa wajen yaki. Wanda ya dada janyo masa tsana a wajen yarima hafid.

 Wanda ya dada janyo masa tsana a wajen yarima hafid

Oups ! Cette image n'est pas conforme à nos directives de contenu. Afin de continuer la publication, veuillez la retirer ou mettre en ligne une autre image.

( Yarima huzail a lokacin yaki.)

Faris babban abokin huzail ne wanda suka taso tun suna kanana har zuwa girmansu, sai dai shi iyayensa talakawa ne dake zaune a cikin garin halman, amma hakan bai taba sa huzail ya dauke shi daban ba daidai da rana daya, tsanananin shakuwarsu yasa har mai martaba ya bawa iyayensa kyautar gida a cikin garin, duk abinda yarima huzail zaiyi tare yake da faris, daidai da lokacin daya basu taba ware kansu ba a duk wata harka data shafi rayuwarsu, ra'ayinsu da komai nasu daya ne, sai dai wasu lokutan faris kan fi huzail yawan magana.

Gimbiya ruwaila, 'yar gidan wazirin halman ce, wadda tsananin son da mai martaba yake mata yasa ya bata mukamin 'Gimbiya' ta garin halman kasancewar bashi da diya mace, har taro na musamman akayi, sarki ya gaiyaci manyan sarakuna har da shugaba Nur jahaan, inda aka bata mukamin 'Gimbiya'.

Sai dai tun tasowarta, kowa ya san tsananin son da take wa yarima huzail domin a da lokacin yarintarta babu wanda ruwaila ta saba dashi kamar huzail, ya dauke ta tamkar kanwarsa kasancewar bashi da 'yar uwa mace, komai tare suke yi, hatta abinci ruwaila bata ci sai tare dashi, shi ya koya mata karatu, rubutu, hawa doki da duk wasu k'ananan abubuwa, a duk sanda yake gari zai shafe rabin yininsa ne yana hira tare da ita har sanda zata yi bacci  kuyanginta su maida ta gida.

Lokaci da ta fara girma, sai duk wata kyautatawarsa ta juyewa mata zuwa tsananin sonsa, ta yarda cewar babu wanda zata iya so a duniya sama dashi, bata iya boyewa sam, dalilin da yasa kowa ma ya lura da hakan kenan, amma tun lokacin da huzail ya fahimci take takenta, ya dauke mu'amalarsa da ita, domin ko kadan babu tunanin wannan a tsarin rayuwarsa, ya dauke ta ne kamar kanwarsa data haramta a gareshi, amma tunda ta b'arar da hakan sai su tafi a matsayin 'ya'yan aminan mahaifansu kawai.

Sai dai tsananin son da mai martaba yake wa dukkaninsu, yasa akayi baikon ba tare da son ran huzail ba, sai dan ba zai iya yiwa mahaifinsa musu ba.

Rayyana 'ya ce ga babban bawan gidan waziri 'Aaban' wanda ya kasance malamin yarima huzail, don shi ya koyar dashi dabarun yaki kafin ya koma Agsin wajen wani babban malami. Huzail na girmama Aaban sosai domin kyawawan halayensa da suka sa yaji dadin zama dashi, akwai lokacin da ya ziyarce shi a gidansa dake daya daga cikin gidajen da ake bawa manyan bayin waziri har yayi niyyar kwana, amma mai martaba yasa aka dawo dashi cikin daren.

Aaban da matarsa sun rasu kusan shekaru biyar da suka wuce, bayan ya danka wa waziri kyautar diyarsa daya Rayyana a matsayin baiwa, inda shi kuma ya mika ta ga bangaren 'yarsa gimbiya ruwaila.

Girman mahaifinta da yake gani yasa yarima huzail kula da rayuwar rayyana tamkar kanwarsa, wanda hakan ya janyo mata bakin jini a wajen ruwaila, a tunaninta ya za'ayi baiwa ta sami kulawarsa fiye da yadda ita bata samu. Hakan yasa tayi kokarin hana mahaifinta bashi 'yancinta lokacin da ya nema, amma duk da haka baya kula ta kamar yadda yake damuwa da rayyana, dalilin da yasa tana jin zancen sulhun da mai martaba ya tura shi Qiyadha, wanda ta san zai dauki lokaci, ta tura ta gidan kurkuku har tsawon shekara guda.

Komai Nisan Dare | ✔Où les histoires vivent. Découvrez maintenant