Vote and comment please!
"Dangantakar jini ba ita kadai ce shaidar 'yan uwantaka ba, dan'uwa shine abokin da zuciyarka bata nutsuwa idan baya nan."-Burayd.
HALMAN.
Taku ashirin ne daidai daga inda yake tsaye zuwa inda kungiyar wasu ma'aikata ke ta jera tarin makaman yak'i cikin wasu dak'una dake gidan ajiya, daga gefe kuma masu wanke takubba da kuma garkuwowin da suka baci da jini ne, dukkaninsu na aikin cikin farin ciki game nasarar da suka samu akan mutanen dezhwar ba tare da sunyi asarar mutanensu da yawa ba.
A karo na farko da ya rike matsayin shugaba a filin daga kuma aka samu nasara, ya kamata ace shima cikin irin wannan murnar yake koma fiye dasu, amma zuciyarsa da kuma gangar jikinsa sun kasa karbar hakan, ko yaya yayi kokarin nuna farin cikin, sai yaji kamar wani abu ne dake tsaye akusa dashi kuma babu ta yadda za'ayi ya karaso cikin zuciyarsa.
"Burayd!" Muryar lateef daga gefe ta kirashi lokacin da ya karaso gabansa.
"Sun bamu yarinyar, tana can gidan magani."
Ya gyada kansa kafin yace.
"Mutanen mu fa da suka kama?"
"Basu bamu amsa akan wannan ba, da alama suna zargin ko suma akwai mutanensu a wajen mu ne, tunda har yanzu basu gama tantance iya adadin wadanda suka rasa ba."
"Ba matsala nan da kamar sati daya sai mu aika musu, kafin nan sun san cewar bamu rike komai nasu ba."
"Haka ne, muje kaga yarinyar, na tsaida a fara duba ta sai kazo tukunna."
Lokacin da suka shiga cikin gidan maganin, Rayyana na kwance kan wani gadon rimi a d'aya daga cikin dakunan da ake ajiye majinyata, ta takure jikinta cikin cura daya.
Ba sai an kalleta sau biyu ba za'a tabbatar da cewar ta shiga tashin hankalin da yayi mummunar jijjigata, idanunta a bude suke, amma in mutum ya kalleta sai yaga kamar ta zare su ne.
Burayd yaga ta canja masa akan yadda ya santa lokutan da take zuwa gaishe da huzail, ta rame, tayi baki tayi duhu, dogon gashinta an yanke shi iya dokin wuyanta, wani abu mai kama da tausayi yaji ya tab'a zuciyarsa dake da tauri a lokacin.
"Ba zata iya fahimtar komai ba, a fara dubata tukunna." Ya ce da lateef sannan ya juya ya fita.
"Me ake ciki game da iyalan mamatan da za'a biya diyya?"
Ya tambaye shi bayan sun fito waje.
"Anata tantance su har yanzu, zuwa gobe muke saka ran biyansu gaba daya."
"Me yasa sai gobe? Kamata yayi duk wanda aka tantance a basu diyyar 'yan uwansu a yau tunda mai martaba ya riga ya fitar da komai, hakkinsu ne."
Lateef ya gyada kansa a hankali sannan yace.
"Haka ne, bari naje na sanar dasu don a canja tsarin."
Da haka ya juya yayi bangaren hagu inda zai kaishe ga sashin dasu daghfal ke tantance iyalan mamatan da aka rasa a yakin.
Burayd ya dawo da idanunsa zuwa hanyar da yake bi, sashin bangaren mai martaba ne, zuciyarsa yaji ta cukwuikwuye lokaci guda.
Tun daren da aka rasa su huzail, mai martaba baice komai ba, bai bude bakinsa ba balle har wani yaji maganarsa, duk umarninsa yana yin ishara ne ga makusantansa su kuma su dorar, a jiya da zaman kuramen ya dami waziri ne ya gaiyato wani mai magani don duba lafiyarsa, a lokacin ne aka fadi labarin daya girgiza kowa, cewar zuciyar mai martaba ta tabu har abin ya shafi maganarsa. A yanzu haka yana kwance cikin kyakkyawar kulawar da aka hana kowa ganinsa.
VOCÊ ESTÁ LENDO
Komai Nisan Dare | ✔
Ficção GeralSarauta, Mulki, Soyayya, kalubale, da kuma kaddarar rayuwa.