(Rumfa ta hudu, fadar gimbiya Ruwaila.)
Vote and comment please!
"Soyayya shine lokacin da kaji zaka iya kashe ko waye a hanyar farin cikin ka."-Ruwaila.
-
-------
"Bani labarin shigowarku." Gimbiya Ruwaila ta fada zaune akan karagar dake cikin fadar, sanye take da wata doguwar Riga kalar ruwan hoda don sanin ba lallai ta samu damar ganin Huzail a ranar ba yasa ta canja shawarar sanya kalar da tafi so maimakon baki, an nannade gashin kanta cikin tufka daya da ya tsaya a can sama.
Daga amintattun bayinta sai bakinta na kasar 'Dezhwar' a cikin fadar. Daya daga cikin bakin ne ya gyara zama kafin yace.
"Lokacin da muka iso garin nan, mun sauka a wani kauye kafin mu karaso cikin ganuwa don a lokacin dare ya fara, a lokacin ne muka ji ana jita-jitar cewar yarima ya dawo cikin daren, don wasu mutane daga kauyen sun ce sun ga wucewarsu a lokacin da suke kamun kifi a wani rafi dake kan hanya, akwai wanda ya rantse ma yariman ya dago musu hannu. To tun a sannan muka fara tunanin canja shawarar mu ta shigowa cikin garin.
Washegari da sassafe kuwa labari ya tabbata cewa lallai yarima ya dawo a daren, nan da nan kuma mutane suka fara tururuwar tafiya cikin gari, hakan yasa muma muka yi shiri cikin kaya tamkar na sauran mutane sannan muka siyo kayan marmari da yawa muka dora akan kudi da kuma kayayyakinmu muka shigo cikin ganuwa a matsayin masu saida a kayan marmari." Ya karasa dauke da murmushi.
Itama murmushin tayi kafin tace.
"Lallai kun cika masu hikima."
Wani daga cikinsu ya dauki kwayoyin inibi daga cikin farantan dake gabansu wadanda ke cike da nau'inkan abinci kala kala na alfarma da suka fi karfin cikinsu, kafin yace.
"An shaida mana kin aika da sako tsawon shekara daya kenan amma mu bai iso garemu ba sai a mako daya daya wuce, don bawan yace yasha wahala da 'yan ta'adda a hanya kafin ya samu kubuta, sai dai duk da haka, yazo da ciwon da ya zama ajalinsa kwanaki kadan bayan zuwansa."
"Ai asarar bawa daya a wajen gimbiya na tabbata ba wani abu bane." Cewar wani daga cikinsu.
"Haka ne, ba don sakon ba ma, da ban san dashi ba." Ta fada har a lokacin tana murmushi don zuciyarta cike take da farin ciki, ta juya wajen raila dake gefenta tace.
"A shigo da ita."
Raila ta dubi wasu kuyangi biyu dake tsaye daga can gaba tayi musu inkiya, da sauri suka juya suka fita sannan cikin abinda bai fi yan dakiku ba suka sake dawowa, biye dasu Rayyana ce kanta a sunkuye tana kallon yatsunta data dunkule su wuri daya saboda rawar da hannunta ke yi.
Bakin guda shida suka zubawa Rayyana ido kowa da irin abinda yake nazarta game da ita har ta sami waje ta zauna a gaban Gimbiyar.
"Barka da warhaka gimbiya, fatan na same ki lafiya."
YOU ARE READING
Komai Nisan Dare | ✔
General FictionSarauta, Mulki, Soyayya, kalubale, da kuma kaddarar rayuwa.