SHA BIYAR.

1.3K 159 0
                                    

Vote and comment please!

"Duk abinda ya iso gareka, mallakinka ne tun lokacin da baka san shi ba."-Zaid.

------

"kar kace min cikin wajen nan zamu shiga."

Zaid ya fada tsaye kusa da faris, dukkaninsu suna kallon wani bakin daji ne da iskar dutsen dake hannun faris ta cillo su gabansa.

"Nima tambayar da nake yiwa kaina kenan, da gaske nan din zamu shiga." faris ya fada a hankali yana kallon dajin.

Zaid yayi kasa da muryarsa sannan yace.

"Tunda baka tabbatar ba, ina ganin ya kamata mu koma inda muka fito, don da alama gwara azabar halittun can da abinda ke cikin dajin nan."

Faris yayi murmushi sannan ya juyo ya kalle shi yace.

"Ai tunda muka riga muka zo babu hanyar komawa baya, sannan tunda ka ganmu anan, nan din zamu shiga kenan bai kamata ka karaya tun yanzu ba, ka manta kace babu irin bala'in da baka tsallake ba a rayuwarka ta baya."

Zaid ya kalli fuskar faris dake murmushi sannan bakin dajin dake gabansu, ya hadiye yawu yace.

"Akwai wata matsala ne, duk wadancan bala'in dana fada maka, ba a cikin duhu suke ba, haske ne sosai a wajen."

Faris yayi murmushi sosai sannan yace.

"Neman mafita ba ruwan shi da haske ko duhu, ko a ina ne zaka iya fitar da kanka."

Yana fadin haka, ya jawo kafadarsa suka taka cikin dajin. Wani irin duhu ne da dogwayen bishiyun ciki suka haddasa shi, sannan ga dan karen sanyi dake ratsawa har cikin jijiyarsu, saboda tsananinsa har wani hazo yake fitarwa daya mamaye koina. Sannan ba abinda ake ji sai kukan tsuntsaye da kwaruka koina.

Zaid na cikin waige-waige idanunsa suka hango masa wani abu kamar tsuntsu yana tahowa saitinsu, da farko ya tsaya don ya tabbatar da zarginsa, amma daya fahimci da gaske tsuntsun ne kuma kansu yake tahowa sai ya tabo faris dake gefensa.

Wani irin tsuntsu ne mai kama da mikiya amma kuma yafi girman mikiya kusan sau biyar, kafin dukkanninsu su gama tantance me zasu yi tsuntsun ya karaso kansu, ya shiga kartar zaid da dogwayen yatsunsa kota ina a lokaci daya kuma yana caccakar faris da bakinsa.

Kowannensu ya rasa yadda zaiyi, hannayensu da suke kokarin kare fuskarsu dashi duk sun yi jini saboda yadda farata da bakin tsuntsun ke kartarsu, garin yin baya faris ya fadi akan bayansa, saboda haka tsuntsun ya sauka akansa gabadaya ya rufar masa.

Zaid dake tsaye ya shiga waige, cikin sa'a kuwa idanunsa suka hango masa wani dogon reshen bishiya daya fado kasa, ya dauko shi da sauri sannan yayi kansu, amma kafin ya karasa tsuntsun ya waigo yayo kansa shima, ya tsaida reshen a tsaye lokacin da ya fado kansa. Reshen ya fasa wuyansa sannan ya fito ta baya.

Tsuntsun yayi wata irin kara data cika wajen sannan ya fada kan zaid. Katon jikinsa gaba daya ya danne shi, yayin da jinin dake fitowa daga wuyansa ya dinga zubowa kan fuskarsa, ya shiga kokarin ture shi amma nauyin jikinsa yafi ya iya daga shi shi kadai.

Faris ya karaso da sauri ya fara kokarin janye shi amma sai yaji kamar wani gingimeman dutse yake turewa, babu alamun yana matsawa, ya jiyo alamun muryar zaid daga can kasa yana kiransa, da alama shima kokarin fitowa yake.

Ya sake kokarin jan tsuntsun amma babu abinda ya canja, ya matsa daga baya yana kare masa kallo, ya gama tabbatarwa dukkan karfinsu ba zai iya janye shi ba, sai dai ko dabara ta fitar dashi, saboda haka ya juya ya hango wata katuwar bishiya mai zara-zaran igiyoyi a jikinta, tunanin daya gifta cikin zuciyarsa ya tabbatar masa zai iya samun mafita.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now