TAKWAS.

1.6K 139 7
                                    


Vote and comment please!

"Wata muguntar, kan zama alkhairi."-Huzail.

-------

"Bayan baiyanar kwakkwarar shaida daga wajen gimbiya ruwaila, ya tabbata cewar kasar dezhwar ita ke da gaskiya akanmu, saboda haka zamu yi yaki ne na kare kai ba na 'yanci ba."

Muryar huzail ta karade 'yar karamar rumfar da suke ciki, inda mai martaba da wasu daga cikin manyan mukarraban fada suka bukaci sanin irin shirye-shiryen da kungiyar kula da yakin ke gudanarwa. Bayan su kwamandojin halman guda goma sha hudu ne durkushe daga bayan huzail wanda ya durkusa gwiyoyinsa daga gaban kujerar mai martaba, sai kuma yarima hafid dake zaune a gefen sarki. Duk wanda ke wajen amintacce ne a garin halman, domin tsoron fitar wani sirri na tsarinsu.

"A yanzu haka muna da adadin manyan jarumai na mutum dubu daya da dari uku da hamsin, sannan kananan mayaka Kuma akwai tsayayyiyar runduna ta mutum dubu goma da dari biyu, wanda dukkanninsu ke karkashin kwamandojin mu goma sha hudu.

Daga yammacin yau zamu saka runduna guda biyu su zagaye ganuwar garin nan gaba daya, domin kamar yadda mutanen kasar dezhwar suka saba, zasu iya yi mana shigowar bazata, su shigo cikin gari su bi ta kan al'umma da basu da lafin komai sannan su kona gine gine kafin faruwar yakin.

Daga wata majiya wadda duk da bamu tabbatar da igancinta ba, an fada mana cewar suna da kimanin runduna ta mayaka dubu talatin da daya. Amma a wajenmu, yawan mayaka bashi ne kadai nasarar yaki ba, tsari da kuma dabarun yaki a filin daga, shine babban jigon dake nuna nasara a ko'ina, saboda haka muyi tsare-tsare da kuma wasu dabaru da muke fatan su kaimu ga ci, domin dole ne mu kare masarautar mu, kasar dezhwar tayi kadan ta zama tarwatsewar gari mai dinbin tarihi da albarka irin halman."

"Wane irin dabaru kenan?" Galadima ya tambaya.

Huzail ya danyi gyaran murya kafin yace.

"Mun yanke shawara zamu yi amfani da irin dabarun kasar Romawa. (Rome)"

Maganarsa tasa dukkanin mukarraban fadar suka dago suka kalle shi, wasu ma bakinsu bude saboda mamaki. Shi kansa mai martaba da rabin fuskarsa ke rufe cikin rawani sai da ya tsaida kallonsa akan dan nasa.

"Ya za'ayi muyi amfani da wani tarihi dake cikin bayanan litattafai, wace kasa ka taba ji sunyi amfani da tsarin romawa balle har ayi maganar gari guda daya tal? ta yaya zamu yi abinda da ba'a taba gwadawa ba?" Daya daga cikin mukarraban fadar ya fada hannayensa a ware.

"Gaskiya kam." Na kusa dashi ya amsa.

"Wannan yaki ne na gaske, wanda in muka yi sake, xai iya shafar wasu garuruwan, ba wai filin koyo ba da zamu fara gwada sababbin abubuwa." Yarima hafid ya fada yana nuni da hannunsa.

"Haka ne, yaki na gaske zamu yi, yaki ne wanda abokan gabarmu sun ninka mu a yawa saboda haka, dole muyi amfani da dabaru masu hikima wadanda zamu shammace su har mu sami lagon yawansu, tsarin romawa tsari ne da babu wanda ya taba amfani dashi bayan su, kenan mutanen kasar dezhwar baza su taba tunaninsa ba balle har suyi tunanin muma gari guda daya tal zamu yi amfani dashi." Huzail ya bashi amsa yana kallon idanunsa.

Hakan yasa fadar ta rude da yan maganganu wasu na ganin hakan yayi, yayin da wasu har a lokacin suke shakkar al'amarin.

"Na amince da hakan." Muryar mai martaba ta katse surutun kowa har a lokacin idanunsa na kallon huzail. Hakan yasa wajen ya koma tsit.

Huzail ya gyada kansa alamun godiya sannan ya cigaba da bayani.

"Ba duka tsarin zamu yi amfani dashi ba, mun dauki wasu bangarori ne kawai da zasu dace da irin tsarin mu. Zamu saka mayaka dubu hudu masu rike da mashi da kuma katuwar garkuwar karfe wadda zasu buya a bayanta su tsaya daga farkon kowacce runduna ta yadda kafin mutanen dezhwar su iya fasowa cikinmu za mu iya soke da yawansu da wannan mashin.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now