Salam, Abin nawa sai addu'a kawai 😀 truly I'm a lazy writer, gaba daya labarin nan I've it written paper amma kafin in samu in rubuta muku shi a wattpad shine aikin cox writing isn't my thing...so bear wit me plxx, i promise to gyarawa insha Allah.
And now brace urselves to a chapter of 5,000➕ words..😀
Vote and comment please!
-
------
A hankali dare ya koma safiya, safiya ta koma dare, duhu ya kara mamaye sararin samaniya hasken farin wata dana taurari ya haskake doron duniya kafin na alfijir ya keto ya mamaye su.
Ta bude idanunta da kyar, ta rufe, sannan ta sake budewa, hakan kadai ya harba wani abin mai zafi cikin kowacce jijiya ta jikinta, ba zata iya tuna dadewar da tayi kafin ta iya bude idanunta nata ba, ta san dai tasha yunkurin hakan tana kasawa.
Sanyi da kuma kamshin wata sassanyar iska ya ratsa cikin hancinta, kamshin ba irin na turakarta bane, hakan yasa tayi tunanin ko a wani wajen take, a hankali idanunta suka cigaba da budewa haske na shiga cikinsu, da farko ba abinda ta ke iya gani sai farin hasken kawai, amma a hankali kuma hasken ya koma siffar dishi-dishin ganyayyakin bishiya daga can sama suna motsawa, kamar masu tafiya suna wucewa, ta cigaba da kallon wucewarsu don ganin nata ya daidaita sai dai kuma tsillin hasken ranar da ganyayyakin suka rufe daga bayansu ya fara ratsowa ta tsakanin su yana dukan kwayar idonta, hakan yasa tayi yunkurin canja yanayin kwanciyarta gefe don kaucewa hasken.
Abinda ta gani ne yasa ta saurin zabura ta mike zaune idanunta na kallon sauran jikin fuskar matar da tayi arba da ita kwance a kusa da ita, a lokacin ne kuma ta lura ba su kadai bane a wajen, har da karin wasu mutane da ko a zagin ido, zasu kai hamsin sannan kuma gaba dayansu mata ne wasu cikin shiga mai kyau yayin da wasu kuma sanye da yagaggun kaya, dukkaninsu sunyi shiru kuma sun sunkuyad da da kansu kasa.
Ina ne kuma nan? Wata murya a kwakwalwarta ta tambaya, me ya kawo ta nan? Su waye wadannan mutanen?
Da sauri idanunta suka shiga zagaye wajen, tambayoyi da kuma rudani na shawagi cikin kanta, ta daga kanta sama anan ta lura cewar ganyayyakin da ta fara gani masu tafiya ba tafiya suke ba, sune suke wuce su ta cikin wani faffadan keji da aka yi shi da itatuwan jikin bishiya, aka kuma fitar da 'yan raga-raga wadda hannun mutum ne kawai zai iya shiga. Kejin na daure ne jikin wata katuwar giwa dake jansa a duk motsa kafafunta da take, daga saman giwar kuma, tayi arba da wata katuwar halitta mai siffar mutum, irin wadda ta gani kafin sumanta.
YOU ARE READING
Komai Nisan Dare | ✔
General FictionSarauta, Mulki, Soyayya, kalubale, da kuma kaddarar rayuwa.