SHA TARA.

3.3K 255 25
                                    

Vote and comment please!

This chapter is dedicated to you reading this page! Thank you so mush mush for sticking with KND to this very chapter... you don't know what dat means to me, daga 53, 78, 140....views gashi yau har mu kai 2k.....

It makes me cry wallah...😭

-----

HALMAN.

"Sunansa Hisham, k'anin mahaifin rayyana ne yazo nan garin ne a matsayin bawa bayan b'atansa da shekara guda. A lokacin mahaifin rayyana 'Aaban ' yana babban bawa a gidan waziri, wazirin ne da kansa ya fanshe shi a kasuwa bayan Aaban d'in ya gano shi da kansa."

Mahaifiyar burayd ta fad'a tana kallonsu zaune a gabanta.

"A lokacin mahaifinka yana raye burayd, saboda haka muna zaune ne a cikin masarauta, akwai mutunci sosai tsakanina da mahaifiyar rayyana har ya kai kusan duk wani abinda ya shafeta tana fad'a min. Saboda haka ita ta shaida min cewa k'anin mijin nata babban attajiri ne kafin b'atansa, kuma wai wasu irin halittu ne suka kamashi dake k'ark'ashin shugabansu mai suna SADANU.

Ta shaida min cewa yasha mutuk'ar wahala a wajensu kafin ya iya samu ya kub'uta, kuma bayan kub'utarsa ma yasha wuya da har hakan ya kusan tab'a hankalinsa, don sau da yawa yana yin abubuwan da mai hankali ba zaiyi ba. Bayan kub'utarsa ne ya had'u da masu kamen bayin da suka yi ta cinikinsa daga k'asa zuwa k'asa har aka shigo dashi parvez."

Burayd ya lankwasa yatsunsa suka bada k'ara yana saurarenta, bayan duk hak'urin da yayi suka gama doguwar gaisuwarsu itada rayyana wadda ta k'unshi duk abinda ya faru a d'an tsukin nan, yanzu kuma ta d'auko bayanin tun daga farkon da ya tabbata ba zai amfane shi ba, shi zuciyarsa ta k'agu yaji abinda yake nema, saboda haka ya bud'e baki yace.

"Toh ummu me ta shaida miki game da inda aka kaishi din? Da kuma ya hanyar take?"

Ta kalle shi da d'an guntun murmushi.

"Inda muke tafiya kenan burayd, zaka iya koda hakurin minti d'aya ne?"

Bai ce komai ba ta cigaba.

"Bayan mahaifinka ya rasu, sai muka fito daga masarauta muka dawo gidansa dake cikin gari, a lokacin hisham ya sake da garin nan har ya fara tara arzikinsa daya rasa, kasancewarsa mai nasibi duk abinda ya fara yana bunk'asa nan da nan. Dalilin kasuwancinsa da nima na nuna ina sha'awa yasa muka saba sosai, dan sau da yawa ma zai ziyarce ni mu dad'e muna hira.

To a irin wannan zuwan nasa ne yake shaida min cewa da yana da runduna ta mayak'a kuma ya iya tsafi, tsaf! Zai iya komawa wajen maguzawan nan ya yak'e su don ya san daidai mararrabar da suke tsayawa suyi tsafin da yake maida su can nahiyar da suke fitowa.

Daga wannan lokacin bai dad'e sosai a garin nan ba ya koma can k'asar su tehran, shi yasa nace ka zo da rayyana saboda ya santa sosai kuma zaka fi samun had'in kansa in har ya ganku tare."

Burayd ya gyada kansa a hankali yana jin kowacce kalma na nutsewa cikin kansa, wani d'oki da k'aguwa ya dinga shigarsa, ji yake kamar ya rufe idonsa a lokacin kawai ya ganshi a cikin birnin tehran.

"Rayyana ta riga ta amince da komai, yanzu sai kuyi shawarar yadda tafiyar taku zata kasance."

Ya tsinkayi muryar mahaifiyarsa, ya bude idanunsa daidai lokacin da take fita daga d'akin.

Komai Nisan Dare | ✔Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang