SHA SHIDA.

1.5K 151 14
                                    

Vote and comment please!

"Wata damar...tana zuwa sau daya ne a rayuwa!"-Burayd/Hafid.

-------

HALMAN.

"Da ka san dalilin da yasa na taimake ka da baka zo yi min godiya ba."

Tamrukka ya fada yana kallon Yarima hafid dake zaune a gabansa shi da yaransa, bahir da wisam, wadanda dukka suka daina murmushin da suke yi jin abinda ya fada.

"Kowannenku ya sani cewa ni bawan masarautar nan ne, amma a masarautar ma biyayya ta tana kasancewa ne kawai ga sarki shi kadai. Yau shekaruna sittin da daya ina bauta a masarautar nan, kuma a cikin shekarun naga wucewar zamanin sarakai biyar, hakan na nufin kenan duk wanda ke kan kujerar mulkin garin nan, ina rayuwa ne bisa umarninsa. Saboda haka idan kayi la'akari da wannnan bayanin zaka ga kawai ina yin aikina ne, don in baka manta ba lokacin da muka hada ido a fada, ka roke ni da in boye sirrinka, biyayyar da nayi kenan."

Dukkaninsu sunyi shiru suna kallonshi, daga yanayin fuskarsu zaka san zancen ya daure musu kai. Bahir yayi gyaran murya lokacin da ya kula yarima hafid ya kasa magana yace.

"Zancenka haka yake tamrukka, sai dai abinda bamu fahimta ba shine, kace kana yin biyayya ne kawai ga duk sarkin dake kan kujerar mulki, kuma kayi abinda yarima ya roke ka bayan ba shine sarki mai ci a yanzu ba."

Tamrukka yayi murmushi sannan yace.

"Yarima hafid shine sarki mai ci a yanzu, abinda ya rage kawai a tara jama'a a nada shi, wanda hakan ma ya kusa faruwa nan da kankanin lokaci."

Hafid ya zare idanunusa cike da mamaki lokacin da yaji haka.

"Idan na fahimce ka, hakan na nufin mai martaba ya kusa mutuwa kenan?" wisam ya tambaya.

"Kwarai da gaske wisam, mai martaba ba zai kara mako guda a raye ba."

Bahir yayi murmushi mai fadi sannan ya juya ya kalli hafid dake gefensa. Ga mamakinsa, maimakon yaga yana murmushi sai fuskarsa ta nuna wani abu kamar tsoro, fargaba ko kuma damuwa, kafin yayi magana hafid din ya riga shi.

"Ciwon ne zai kashe shi ko kuma kai zaka kashe shi tamrukka?"

Ya tambaya yana kallon cikin idanunsa.

"Ciwon ne zai kashe shi, saboda magungunan da nake bashi ba na ciwonsa bane, maganin..."

"Toh don me yasa zaka yi hakan...?" ya katse shi da karfi yana mikewa kan gwiwoyinsa, tamkar zai kai masa duka.

"Ka san irin azabar da yake ciki kuwa? Ka san irin ciwon da yake ji? Zuciyarsa ce ke rub'ewa alhalin yana raye, yana jin ciwonta da wucewar kowanne dakika, akwai azabar data fi wannan? karyane kenan da kace kana yin biyayya ga duk wanda ke kan kujerar mulki, mahaifina har a yanzu yana raye, kuma shine sarki ba ni ba, wace irin biyayya ce wannan kake masa? Wace irin biyayya ce zata sa ka kashe shi?....mahaifina ne fa tamrukka!"

Ya fadi kowacce kalma cikin karaji da huci. Bahir ya mike da sauri ya riko shi ya zaunar dashi cikin fadin.

"Ubangiji ya huci zuciyarka ranka ya dade, hakan bai dace da kai ba, tamrukka yana yin abinda yake tunanin alkhairinka ne, bashi da niyyar cutar ranka, ka sassauta zuciyarka ka fahimci inda ya dosa..."

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now