SHA TAKWAS.

1.8K 182 5
                                    

Vote and comment please!

"Rayuwa itace wannan bugawar dake gefen zuciyarka, wannan motsin da a kullum yake sawa kaga safiyar gobe, wannan kid'an dake sawa ka yak'i tsoronka, sannan wannan dukan dake baka kwarin gwiwar da zaka fuskanci k'alubalen rayuwarka." -Huzail.
-

------

K'arar rugurgujewar wani abu ya cika kunnuwanta, zafreen ta farka a gigice lokacin da wani katon dutse ya fado gabanta, ta juya kowanne bangare babu abinda take iya gani sai kura kota ina. Ta jiyo k'arar abubuwan nan daga can nesa na tunkarowa, dole ta bar wajen nan in ba haka ba, zasu iya karasowa su tarad da ita.

Ta d'age kasan rigarta, sannan ta shiga gudu tsakanin duwatsun dake fadowa, amma duk da haka, tana iya jin kararrakinsu na matsowa, zuciyarta ta dinga bugawa kamar zata fito daga kirjinta.

A lokacin wani dutse ya fad'o a gefen kafadarta, tayi kokarin kauce masa amma sai da ya karci hannunta tun daga sama har kasa, ta dafe wajen tana jin danshin jini na fitowa, k'arar daya daga cikin halittun ya taho tare da fadowar wani dutsen, ta mike da sauri ta cigaba da gudu cikin wajen da bata san ina karshensa yake ba, bata tabbatar ma zata iya fita daga cikinsa ba. Zata cigaba da kokarin neman hanya ne kawai duk ta san dole ne ta mutu, amma akalla ruhinta zai san cewa tayi iya nata kokarin.

Darn!

Taji wani dutsen ya daki bayanta, rad'adi ya zarce daga jijiyoyinta zuwa cikin kanta, taji gudun jini akan fatarta yana zirarewa k'asa. A yanzu mutuwar zata zo, ta fadawa kanta lokacin da Kafafunta suka shiga gurdewa, amma duk da haka bata tsaya ba, ta cigaba da tafiya tana tangadi cikin kurar wajen.

Wani dutsen ya sake fadowa ya bugi hannunta, bata tsaya ba ta cigaba da tafiya amma ta kasa cigaba da kaucewa, tana jin dukansu kota ina a jikinta, kanana da manya.

Tsoro ya fara kamata, ya kamata ace mutuwar tazo mata yanzu, ya kamata ace jikinta yayi raunin da ba zai iya d'aukan ruhinta ba, bai kamata ta cigaba da iya tafiya ba, amma zata jira, tunda ta san dai duk karkari ba zata kara cikakken k'irga ba a yanzu.

Kafafunta suka tsaya, ta juyo a hankali ta kalli abubuwan nan ta cikin dishi dishin idonta, wadannan mugayen makaman dake jikinsu na jijjigawa tare da gudun da suke yi, ta hango sanda daya daga cikinsu ya daga wani mashi yana shirin jefo mata.

Ga mutuwar nan ta taho! taji zuciyarta na rokonsa da ya jefo mashin da wuri ba sai sun karaso ba, ta rufe idanunta a hankali lokacin data hango mashin ya taho a saiti daidai bangaren zuciyarta.

Amma maimakon taji shigar sa sai taji ana girgiza kafadunta da karfin gaske.

A lokaci d'aya ta bude idanunta, taga huzail a gabanta, yana kallonta da mamaki a fuskarsa, ta rungumeshi da karfi tana fadin.

"Gasu nan tahowa, zasu kashe ni...mutuwa..mu..tuwa zanyi."

Huzail ya d'an tsaya da mamaki kafin ya d'ora hannunsa a bayanta, tunanin wancan lokacin data fara rungumeshi yazo masa, kuka take sosai tana firgita, da alama mummunan mafarki tayi, daga yadda take kakkarwa kamar mai jin sanyi.

"Babu kowa, ki kwantar da hankalinki, babu kowa anan."

Ta k'ara cusa kanta cikin kirjinsa tana jin wani abu na gudu daga idonta zuwa kan fuskarta. Jikinta sai faman rawa yake yi kamar shi kansa zata jijjiga shi.

Ya shiga shafa bayanta a hankali yana kara tabbatar mata cewa, mafarki ne kawai tayi babu kowa a wajen sai su biyu, yaji tausayinta ya kamashi da kyar kukan nata ya tsaya amma jikinta bai bar jijjiga ba, sai faman ajiyar zuciya take yi kamar wadda ta tserewa abinda zai kasheta.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now