HUDU.

2.4K 203 2
                                    

Vote and comment please!

"Dole a wasu lokutan, muna bukatar mutanen da zasu tallafe mu, ba wai don bamu iya ba ko wani dalilin...sai don kawai muji cewa muma wasu abubuwa ne masu daraja da matsayi."-Huzail.

HALMAN.

"Ta yaya duk irin bayanan da muka samo zaka ki fada mata yarima, akwai wanda ya cancanta ya fara sanin hakan ne bayan ita?" Cewar faris wanda ya dawo daga wajen iyayensa a safiyar.

Mamaki ne ya jamashi lokacin da huzail me fada mass cewa bai sanar da mahaifiyarsa zancen tafiyarsu ba, don a tunaninsa ita ce mutum ta farko a duniya daya kamata ta sani, kamar yadda ita kadai ce ta san kudurinsu da kuma tsare-tsarensu, ko kuma kadan daga cikin tsare-tsarensu.

"Ta yaya kuwa zan iya gaya mata cewar ba zan kara wata guda a garin nan ba zan sake tafiya, idonta cike yake da murnar da na dade da ban gani ba faris, ta yaya kake zaton zan iya rusa wannan farin cikin."

Yarima huzail ya fada yana kallon hoton taswirar hanyar da suka biyo daga qiyadha zuwa halman. Yana zaune ne akan wata kujera dake cikin dakin baccinsa, gabansa wani tebur ne mai cike da tarin takardu wanda kamar komai a dakin, daga kujerar har teburin bakake ne.

Faris ya zauna akan wani tin-tin din dake gefe kafin yace.

"Ka shirya sai a kurarren lokaci zaka sanar da ita kenan?"

"Ka fahimce ni."

"Ni kaina ban sanar dasu Abbu ba, na fi son mai martaba ya fara sanin maganar tukunna."

"Hakan yayi amma bamu da matsala da mai martaba, zai fahimce ni kamar kodayaushe."

Ya fada yana juya bayan takardar, hoton dake wajen ya dauki hankalinsa tamkar yau ne farkon ganinsa dashi, ya dora idanunsa akai ba tare ko kiftawa ba, hankalinsa ya tafi gaba daya kan zanen yayin da kwakwalwarsa ke nazartar rubutun ciki.

"Akwai aiki da yawa a gabanmu." Cewar faris wanda yana lura da yanayinsa ya san me yake kallo."

"Ba zamu iya Barin Parvez har mu shiga kasar Behzad a wata daya ba, dole ne mu rage lokacin tafiyarmu." Huzail ya fada yana dora hannunsa akan taswirar dake dauke da yadda hanyar tafiyarsu zata kasance.

Faris ya taso ya tsaya daga bayansa sannan ya dora yatsansa akan takardar, wajen da aka yi zanen wasu kananan gidaje alamar birni, a kasan zanen an rubata 'Misata'

"Ko bamu rage lokacin tafiyar ba, idan mun shiga kasar Behzad sai mu rage tsayawa a wasu garuruwan, kamar nan misata zamu iya wuce shi da kuma..." Ya ja yatsansa zuwa zanen wani gari mai sunan 'Darlam'

"In muka tsallake su ina ga tafiyar zata kaimu akan lokaci."

"A yadda lissafin yake, nan da wata biyu zasu daina siyan bayi, bayan sati guda kuma su tashi, zamu yi hakan kuma mu rage lokacin tafiyar, in ba haka ba damar shekaru goma ce zata subuce mana."

Har faris zaiyi magana, suka ji muryar wani bawa daga farkon turakar yana neman ison shigowa, sai da huzail ya maida takardun cikin wani akwati dake gefe kafin ya bashi izinin shiga.

"Barka da war haka ranka ya dade, ance kana nemana." Bawan ya fada kansa a kasa.

"Barka ka dai, kayan da muka iso dasu daga qiyadha, a ina aka sauke su?"

"Daki guda aka ware musu a gidan ajiya ranka ya dade."

"Akwai jakar turarurruka dana siya a kauyen taimur a cikin kayan." Cewar faris yana tafiya wajen wani farantin kayan marmarin dake ajiye a wani karamin tebur dake gaban gadon huzail.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now