TARA.

1.5K 147 0
                                    

Vote and comment please!

Hikima da dabara, sune jigon kowacce irin matsala."-Zafreen.

MURAK.

"Abubuwa da yawa sun faru a cikin makon nan, ciki har da kawo baikon ki daga kasar Hindu da kuma janyewar dashi yariman yayi daga baya, hakan yasa surutai ke ta yawo a gari game da hakan, me kuma kike tunanin jama'a zasu ce yanzu in na baki damar fita zuwa wata kasar?"

Sarki saifa ya fada yana kallon 'yar tasa dake durkushe a gabansa tana neman izinin fita farauta kasar Parvez bayan sati daya da janyewar baikonta.

"Ranka ya dade maganganun mutane wani abu ne da ba zai taba karewa a duniyar nan ba, da gaske ne cewar yarima Aaryan ya janye baikonsa akan wani dalili da ba wanda ya sanshi, amma hakan ba zai hana ni cigaba da rayuwata ba, in har muka ce zamu yi la'akari da maganar mutane lokaci zai ta tafiya ne bamu yi abin da ya dace ba." Ta fada kanta a durkushe.

"Zafreen..." Taji muryarsa ta kirata bayan wani lokaci da gama maganarta. A hankali ta dago da idanunta ta kalle shi, a duk sanda yayi mata irin wannan kiran, yana ajiye girmansa na sarki ne ya koma matsayinsa na mahaifinta.

"Hakan kike so?" Ya tambaya.

"Na karbi wancan al'amarin a matsayin kaddara Abbu, ina fatan in cigaba da rayuwata yanzu kamar da."

Ya dan nisa kadan kafin yace.

"Ya kike tunanin ra'ayin mahaifiyarki?"

"Duk da ra'ayin mu ya banbanta da ita, a kullum ita mai fahimta tace."

"Wane bangare ne a kasar parvez din?"

"Bangaren arewa ne Abbu, a wancan zuwan bangaren kudu na shiga."

"An sanar dasu kuma anyi kyakkyawan bincike akan wajen?"

"Duk Adham ya gama da wadannan."

Ta fada a hankali saboda ita kanta ta san karya ta fada, domin ko a jiya Adham ya sake mata magana akan ta jinkirta tafiyar zuwa wani lokaci ko ta canja waje domin ya hango wata matsala, Amma ta dauke shi da maganganunsa ta ajiye a gefe, haka kawai taji babu inda take son shiga a yanzu kamar kasar parvez.

"Hakan yayi kyau, na baki izini ki tafi duk lokacin da Kike so."

Take fara'ar fuskarta ta karu.

"Nagode Abbu, Ubangiji ya kara girma."

-------

"Ina tsoron fitar nan taki ranki ya dade, kamata yayi mu bi shawarar Adham..."

Raila ta fada yayin da suke tafiya bayan gimbiya zafreen ta fito daga turakar mai martaba. A yau ita kadai ta rako gimbiyar wajen iyayenta don har an gama shirya jerin kuyangin rakiyarta a kullum amma tana fitowa tace duk bata bukatarsu a yau, halrat kadai ta ishi tafiyarta.

"Adham, Adham...kin damu da zancen Adham din nan tamkar maganganunsa sune na mai martaba."

Zafreen ta fada har a lokacin murmushin fuskarta na nan. Raila ta danyi shiru tana nazarinta, ganin yadda take jin dadi irin wanda ta san ba karamin abu ne ke sata ba, ta rasa me kasar parvez ke dashi wanda ya sa gimbiyar wannan dokin.

Ta danyi gaba da sauri don ta kamo zafreen wadda ta wuce ta.

"Toh ta yaya zaki yiwa sarauniya bayani?"

"Kar ki damu, wannan ba matsala bace."

Ta fada tana kallon ginin bangaren mahaifiyarta da suka doso. Wanda da hango su tarin bayin dake gadin wajen gaba daya suka sunkuyad da kansu alamun gaisuwa. Murmushi ta sake yi lokaci da ta tuno zuwan da tayi wajen mahaifiyar tata bayan janyewar baikon Aaryan.

Komai Nisan Dare | ✔Where stories live. Discover now