Vote and comment please!
"idan hanyoyi sun ratsa...!"
-------Yawun bakinta ya riga ya kafe, kukan dake fita ta makogwaronta ma ya kare, amma duk da haka, hawaye na ta sauka akan kumatunta wasu na korar wasu, tayi zaton shi kansa ruwan hawayen nata ma ya kare tsabar yawan kukan data kwana tana yi babu kakkautawa.
Gaba daya duniyar tayi mata daci da duhu, zuciyarta tayi mata nauyi cike da hatsaniya wadda tayi kama da bakin hadarin daya lullube sama a lokacin. Duk da kukan nata ya tsaya amma jikinta bai bar jijjiga ba tare da ajiyar zuciya, idanunta a tsaye suke waje daya cike da tashin hankali don tun da take a rayuwarta bata taba shiga masifa irin wannan ba, sau daya ta taba fuskantar mutuwar wani na kusa da ita, lokacin da mahaifiyarta ta haihu 'yar tazo babu rai, amma wani wanda ta saba dashi bata taba jin mutuwarsa ba balle kuma a kashe shi a gabanta.
Saboda haka lokacin da idanunta suka dauko mata fadowar kan Aaryan, tunaninta dama kwakwalwarta gaba daya suka fice daga kanta ta kasa gane komai, ta san dai ta rarrafa ta rike gangar jikin nasa data zube a wajen ta girgiza shi, ta kira sunansa amma bai motsa ba, duk da jikinta nata faman rawa amma haka tayi ta jijjiga shi da iya kafin da zata iya, jinin dake fitowa daga wuyansa na wanke hannayenta.
Kansa baya tare da gangar jikin nasa, amma duk da hayaniyar mutane da kuma inowoyinsu dake tsaye akansu bata bar fatan cewar Aaryan zai iya tashi a lokacin ba, zai tashi ya fada mata cewa haka ma yana daga cikin tsarinsu ne, yanzu zai je ya karasa komai su sami hanyar fita daga wajen nan, su tafi har abada zuwa kasarsu, tunanin su ma ya manta da wani abu makamancin wannan ya taba faruwa.
Tun bayan karar farko data fito bakinta, babu ko danshin hawaye daya kara fitowa cikin idonta sai a lokacin da taji daya daga cikin maguzawan nan yana shaida umarnin cigaba da tafiya daga shugabansu, lokacin ta taji ana janta don maida ita cikin kejin da bata taba tunanin komawa ba, a lokacin ta tabbatarwa kanta rayuwarta tazo karshe, bata da wani sauran fatan barin wajen.
Don daga misalin Aaryan ta san ba ita kanta ba hatta wanda yafi shi dabara ma babu ta yadda zai iya barin wajen...don bamugujen daya kashe shi ko kusa dashi ma bai karasa ba, akwai nisan taku hamsin tsakaninsu kuma ya juya bayansa amma ta haka har yaji tahowarsa da kuma abinda yaje yi. To ta yaya kuwa wani zai sake gangancin fita? bayan sun shaida babban misali da idanunsu.
Ba halinta bane nuna rauninta a gaban mutane, balle kuma fitar da hawaye amma a lokacin bata san sanda ta fashe da wani irin kuka ba dake tasowa daga tun daga kasan zuciyarta yayin da bamugujen daya janyota ke kokarin rufe kejin. Irin kukan da tun da take a rayuwarta bata taba yinsa ba.
Ta cigaba da yinsa har zuwa lokacin da bata san dadewarsa ba, kuma har zuwa sannan babu wanda ya kulata a wajen in banda wannan yarinyar data dafa kafadarta sau daya alamun rarrashi, saifa sauran dake ta binta da ido, hakan ya dada tabbatar mata cewar an canja ta daga duniyar data sani ne zuwa wata daban.
A zuwa yanzu data kwana tana abu daya, wata murya a cikin kanta ta fara jaddada mata cewar kukan da take bashi da wata fa'ida kuma babu abinda zai taimake ta dashi sai dai kuma ta gagara hana idanunta fitar da hawayen sam, ta yarda cewa suna da damar yin makokinsu zuwa sanda suke so, don abinda suka gani wani hoto ne da har abada bata fatan sake ganin makamancin shi.
Ta cigaba da share kwalla tana jan hanci, cikin dishi- dishin ruwan hawayenta dake shirin diga, zafreen taga hannu ya zuro mata wata busashiyar gurasa kan ciyarta. Aikuwa take cikinta ya hau tsallen murna da kuma kugi, sai a sannan ta tuna kusan kwanaki uku kenan rabonta da wani abu mai sunan abinci, tabbas masifa irin wannan babu abinda bata haifarwa.
YOU ARE READING
Komai Nisan Dare | ✔
General FictionSarauta, Mulki, Soyayya, kalubale, da kuma kaddarar rayuwa.