YAY page 1.

5.9K 263 16
                                    

Hey guys here I come again this time is more of a mystery not love story though buh I promise it's gon be interesting and those love part u love it's going to be included inshaa Allah 😉
I love you bohud bohud....lets begin the journey.




💖YA ABUN YAKE? 💖



By Sawwama A.

_Bismillahir rahmanir raheem_






Follow and vote for me on wattpad @ _sawwama14_

*Assalamu alaykum mabiyana Allah cikin yardansa ya k'ara had'amu a cikin wani sabon labarin da inshaaAllahu zai k'ayatar daku uwa uba ya fad'akar ina fatan zaku jure bina domin mu amfana da abinda yake cikin labarin, kuma ban yi muku alkawarin zaku dinga samun post a kan kari ba. Allah ubangiji ya jagoranci tafiyarmu da Ku amin.*


"Keh! Keh! Keh! Kar ki kuskura ki tab'a min d'a shegiya bak'ar aljana" hawayene ya cika idanunta taf bakinta ne ke motsawa alamun tana so tayi magana amma halshenta ya mata nauyi.
Wata uwar harara ta zabga mata kafin ta figi d'anta ta wuce ta barta a palon.

Ummi ce ta fito daga kitchen da alamu taji abinda ya auku itama harara ta watsa mata tace "maganin mara ji kenan ban da rashin zuciya dole ne sai kin tab'a musu y'ay'a ?" Hawayen da take rik'ewa ne ya zubo cikin k'unan zuciya tace " haba ummi!  Haba ummi ni da d'an k'anwan mahaifina ace ba zan jashi a jiki ba?" Ta goge hawayen da ya zubo mata cikin tausayawa ummin ta rik'o hannunta suka shiga bedroom d'inta zaunar da ita tayi kan gadonta tana share mata hawaye numfashi ta sauke tace " *Yuhaana* komi na duniyan nan d'an hak'uri kiyi hak'uri da halin dangin mahaifinki kin sani sarai ba sa sonki ko kad'an sai ki fita batunsu ki mai da lamuranki ga rabbi inshaaAllah zaki ga komi ya daidaita."

Hancinta ta d'an ja cikin muryar kuka tace " toh ni ummi na dad'e da sanin basu sona haka zalika kema ba wani dad'insu kike ji ba duk ta dalilina ummi abinda nake son sani nake rokanki kullum da ki gaya min menene dalilin wannan k'i da suke nuna min wanda har ya shafeki ke kad'ai da kika haifeni amma bai shafi kannena da muke ciki d'aya ba? Anya ummi ni y'ar zuriyar nan ce ko kuwa d'auko ni kuka yi a gidan marayu in ba haka ba ko....." Sai tayi shiru kuma saboda nauyin da abinda take shirin furtawa yayi mata.

Wani kallo ummin tayi mata tace " uhm ina sauraronki ko kuwa me? Mara kunya wato ke ba isa ace kiyi shiru da magana ba kiyi ko? Ke sai dai a gaya miki dalili.. Yuhanasu na san me ke yawo a k'wak'walnki ni d'in nan Hajara da na haifeki ban tab'a aikata zina ba har kullum ina gaya miki ki fita batun mutanen nan kin k'i ji toh ki cigaba ba zan hanaki ba ki saka su a ranki har wani ciwo ya kamaki babu abinda ya damesu ba asararsu bane" da haka ummin ta rufe bakinta ta wuce d'akinsu da k'annenta.

Tagumi ta zuba a bakin gado tana hango kanta ta cikin mirror tana k'arewa kanta kallo yau taji kunyan abinda ta aikatawa ummi gashi ummin har ta d'agota ta tabbatar mata da bata tab'a aikata zina ba. Ajiyan zuciya ta sauke toh ba dole tayi tunanin ko ummin ce ta sameta ta wani hanya duba da yanda kap danginsu bata kama dasu in ba a fizge ba da take yanayi da ummin saboda d'an madaidaicin hancinsu da ya kasance iri d'aya amma banda wannan babu abinda ta d'akko nata ko na papa ba sab'anin k'annenta da kap papa suka d'akko da wanda suke uwa d'aya da wanda suke uba d'aya kawai.

Ba wannan ne kad'ai ke damunta illa kalan fatar jikinta fara ce sol amma me duhuwa gashin kanta kuma sai ya kasance bakik'irin kaman wacce aka yiwa dye da ka kalleta zaka yi zaton baturiya ce ko tana da jib'i dasu sab'anin sauran yaran danginsu da ba farare bane daga dangin uwa har na uba sannan duk danginta biyun babu me wani shahararan gashin arziki iya wuya a sami na parking sab'anin nata me tsawon gaske har gadon bayanta ga cika so da yawa sai dai ta tashi ta samu an yanke mata gashi.

Ba wannan bane kad'ai ke sata rud'ani ba illa kwayar idonta da ya kasance blue shin ita ko ina ta samo wannan halitta da ya banbantata da sauran y'an uwanta dan hatta ta suran jiki ita d'in ta banbanta da su.

In tayi wannan furucin ummi kan ce mata dake da sauran y'an uwanki wa ya hallice ku?" "Allah" shine amsanta a ko da yaushe da zarar ta fad'i hakan ummi zata ce "toh shi yaso ya ganki a haka shi yasa ya banbanta ku"

Kanta ne ya d'au caji tuno irin soyayyan da mahaifinsu yake mata duk a cikin y'ay'ansa babu wanda yake so yake nunawa so irin ta soyayyan da yake mata ya banbanta da na sauran kuma nunawa yake abinshi lamarin da yake  tunzurar da zuciyar momy uwar gidansa.
Ya fifitata akan kowa a gidan yana bakin ciki da halin ko in kula da danginsa suke nunawa akan y'arsa da tafi soyuwa a zuciyarsa.

Sau da yawa zai sata a gaba yana kallo wani sa'in har ruwa ke kawowa idanunsa yana son y'arsa yana tausayinta.
Shin me yasa y'an uwa shi baza su y'arsa da yake ji har cikin b'argonsa ba?

_ni kaina sawwama zan so jin dalilin wannan kiyayyan_


Sawwama Qawwama😘

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now