💖YA ABUN YAKE?💖
By Sawwama A.
Page 12.
Vote and follow me on wattpad @sawwama14
Suna nan zaune da mama suna tattauna yanda za su b'ullowa maganan aurenta ba tare da an sami matsala.
Sallahn la'asar aka kira duk suka mik'e Yuhaana na fad'in "Hassan ba zai zo ya wuce ba sai dare yayi ko."Tana zaune tana lazimi ta ji muryar Hassan da uncle Fu'ad bata tashi ba sai da taji murya uncle muhd da gudu ta tashi ta fita a d'akin d'aneshi taje tayi tana murna zagaye hannunsa yayi a jikinta yana murmushi.
Bata ko kula da matarsa dake bayansa ba sai da ta gama murnanta,ta hangota da sauri ta sakeshi taje ta rik'o hannunta "ah ah auntyna lallai uncle d'ina ya iya kiwa irin wannan kumatu,sannu da zuwa."
Ta sake hannunta taje ta rik'e na uncle d'inta tace "uncle moh sai kallona kake kaman yau ka fara gani ne komi fa ba ka ce min ba."
Murmushi yayi had'e da jan hancinta kafin ya fara tafiya yace "kawai mamakin ki nake sai wani murna kike kaman wacce ta dad'e rabonta da nan."
Fizge hannunta tayi tana k'unk'uni gefen mama taje ta zauna a kan dakali tana mitan "tun fa bikinka yanzu fa kusan wata hudu kenan amma kace wai ba a dad'e ba yanzu ka daina sona tunda kayi aure ko"Dariya duk suka saka Hassan har dayi mata gwalo kallon matar uncle moh tayi tace "auntyna kece kika sa uncle dina ya daina ji dani ko?" Ta tambayeta tana mata hararan wasa.
Sunkuyar da kai amaryar tayi tana murmushin yake janyo farar plastic chair da fu'ad ya ajiye mishi janyo hannun yuhaana yayi ya zaunar da ita kan k'afarsa inda sabo mutanen gidan sun saba da wannan iya shegen nasu sai dai Amaryar moh Amina da bata tab'a cin karo da hakan ba taji wani abu ya caketa a zuciya a ranta tana fad'in wannan wani irin wasa ne? Ko da y'ar uwarsa ta jini ne ai tayi girman da za a daina d'aukanta a k'afa balle wannan daga ganinta akwai ayar tambaya a dangantakarsu duba da yanda kamanninta kwata kwata bai yi dai dai ba,tunda ga k'aninta nan shima basa kama balle a ce da babanta take kama gaskiya ita wannan abun bai mata ba baza ta d'au wannan sakarcin ba mijinta ya dinga daukar wata mace ba ita ba a cinyarsa,ido ta waro jin kalaman mijinta.
"Haba yuhaanan uncle moh sanyin idaniyarsa the treasure of my eyes kema kin san babu wanda zai kamo ki a ziciyata babbar y'ace fa ke kin fi kowa har mamanki." Wani murmushin jin dadi tayi harda kwantar da kanta a kafadanshi dan dama da wannan kirarin yake samo kanta.
Hassan ma murmushi yayi na jin dadin yanda dangin mahaifiyarta ke ji da ita dole yuhaana ta zabi zaria so dubu a maimakon kaduna dan tafi samun kwanciyar hankali a nan shi kanshi basa nuna masa bambanci zuciyarsu a wanke take.
Sai a lokacin uncle moha ya samu daman gaisawa da mahaifiyarsa kallon amina tayi yanda duk ta takure ta mai da kallonta kan moh tace "ku kuwa mai ya fito daku da yamman nan?"
Kallon gefen da Amina ke takure a gefe yayi yace "ke menene haka yau kuma surkunta kike ji ke da maman? Ko yuhaana kike kunya yuhaana fa y'ace diyarki ce."Dariya yuhaana tayi tace "ai ko dai gwara ka fada mata uncle na"
"Mama wai ya diyar taki tuwonki take son ci shi yasa ta tuso ni gaba wai in kawota." Mama tace "toh har ina murna yuhaana zata shigan min kitchen toh bari in tashi maza in dora tukunya."
"Gwara dai kam mama ni da nake bakuwa ba a sani shiga kitchen ba,kai Hassan ba zaka tashi ka fara shiri ba ko sai dare yayi maka?" Ta watsawa Hassan tambaya ganin ba shi da alaman tashi saima mai da kai da suka yi a can gefe shi da fu'ad suna duba abu a cikin wayar Hassan din.