YAY page 4.

1.5K 136 4
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖




By Sawwama A.





Page 4.






Vote and follow me on wattapad @sawwama14







K'ara ta saki wanda yayi sandiyar jawo hankalin papa da sauri ya nufo d'akin dan jin kukan shalelensa.

"Yuhaana wai ke wata irin yarinya ce me taurin kan tsiya da kafiya? Shegiya me tsinannan nacin masifa sai kije ki nemo iyayenki a inda suke tunda kin kasa amincewa da muna iyaye nki wata k'ila soyayyar muce ta miki kad'an sai kije ki nemi wasu iyayen da zasu nuna miki soyayya fiye damu ban sani ba ko halittarki ke rud'anki yake saki jin munyi kad'an da zama iyayenki. Banzan yarinya she...."

"Hajara!" Papa ne ya daka mata wani uwar tsawa "hajara karki k'ara kar ki kuskura inji kin kara danganta min diya da shegiya wani iskanci ne haka zaki tisa yarinya gaba kina wani banzan surutan ki haba wai so kuke ku kasheni a gidan nan ne?"

"Gata nan d'iyarka ke neman jin ba'asin ko mu muka haifeta saboda mu munyi muni da zama iyayenta ita zankad'ed'iya me kyau fara a ga iyayenta bak'a." Ta sa kai ta fice a d'akin a lokacin da wasu hawaye masu d'umi suka zubo mata na tausayin d'iyarta amma bata da wata mafita da ya wuce tayi mata haka ko zata barta ta sarara ta sani dole abin ya dameta duba da yanayin banbancinsu toh amma ya zata yi bata da hurimin fad'a mata yanda abun yake. Kuka yuhaana ta fashe dashi jin sharrin da umminta ke mata rungumeta papa yayi yace " shushhh rabu da ita yuhaan papa zo ki fad'a min menene matsalan me yasa xaki dinga jayaya da ikon Allah?"

"Papa ba haka bane ba jayayya nake da ikon Allah ba amma papa ka duba al'amarin nan banbancina da sauran y'an uwana yasa watak'ila ma ba zan auru ba."
"Subhanallahi mamana me kike fad'a haka?"

Goge hawayenta tayi da bayan hannunta tace "papa sadam yace ba zai aure ni ba saboda bani da asali iyayensa sunce basu yarda ya auri mara asali ba?"

Tashi tsaye papa yayi yace "what? Su iyayen sadam d'in suka ce haka?" Gyad'a mishi kai tayi wani sabon hawayen na gangaro mata.

Cikin huci yace "toh wallahi su jirani zasu ji sammaci a kotu zasu fad'a min ta yanda aka yi d'iyata ta zama mara asali.. Su ba musulmai bane da basu san Allah ba basu san Allah na halittan mutum a yanda ya so ba so nawa me k'afa yake haifan gurgu sai ace dan me yasa be yo k'afar ubansa ba ko uwarsa? Mamana kar ki damu sai na k'watan miki y'ancinki ."

Hannunshi ta riko tana tsananta kukanta ganin hankalinshi ya tashi ranshi ya baci tace " papa ya isa ba sai kai k'aransu ba ka barsu da Allah d'ansu ne tunda sunce ba zai aureni ba Allah zai kawo min wani fiye dashi." Ta k'arasa maganan cikin karaya.

Tausayinta ne ya kamashi ya janyota ya rungume tsam a jikinshi zuciyarsa nayi masa suya hawaye ne suka cika mishi ido hakan yasa ya saketa ba tare da ya kalleta ba ya fita a d'akin.

D'akinsa ya nufa kai tsaye,yana shiga ya murza key kafin ya fashe da wani irin kuka ummi ya spotting kan gadonshi ta kifa cikinta tana kuka.

Cikin sassarfa ya k'arasa kan gadon ya janyota jikinshi yan zubar da k'wala k'ank'ame shi tayi lokaci d'aya ta tsananta kukanta shima a nashi b'angaren haka ne zuciyoyinsu cike yake da bak'in ciki da tausayin d'iyarsu babu wanda yake iya ba d'an uwanshi hak'uri dan dukkansu abin na tab'a zuciyoyinsu in ka gansu gwanin tausayi.

B'angaren Yuhaana ma haka take jikinta ta ja zuwa kan gadon ummi sanin da tayi yau ummi ke da girki yasa ta kwanta nan tana rusan kuka a haka har baccin azaba ya d'auketa.

Washegari ko da zazzafan zazzab'i ta tashi ummi ce ta shigo ta samu sai karkarwa take fuskanta ya kumbura alamun taci kuka duk da itama idanun ummin a kumbure suke da sauri ummi ta tasheta ta bata tea da magani tasha ta san ba komi bane illa zallan damuwa da ta sawa zuciyarta rok'am Allah take a zuciyarta da ya kare mata d'iyarta daga kamuwa da mummunan cuta."

Papa ma da ya zo duba ta sosai ya tausaya mata yaso su tafi hospital ummi tace ah ah.

Ko da momy taga idanun papa da na ummi a kumbure ga yuhaana ance ba lafiya wani murmushi kawai tayi ta girgiza kai ta san ba komi bane illah b'oyayen sirrinsu dake bibiyarsu.

Sanda yuhaana ta kwashe kwanaki uku a gida tana jinya kafin ta warware duk da dai zuciyarta akwai miki amma ta daure ta saki ranta.

Waya suka yi da mariam akan tana zuwa gidan tace ah ah ta bari ita zata zo dan tunda ta kwanta ciwo mariam d'in ke sintiri.

Ummi ta samu a d'aki tana shirya kayan da muhsin me biwa yuhaana ya goge a drawer zama tayi a bakin gadonta tana wasa da yatsunta da yasha jan lalle tace " uhmm ummi dan Allah ine gidansu mariam jikina ciwo yake yi so nake in d'an mik'e k'afa."

Kallonta ummi tayi dan son gano abinda ke zuciyar d'iyartata harara ta d'an wurga mata tace "son yawon dai ya motsa." Murmushi tayi tana d'aga kanta sama tace "kai ummi dan Allah gidansu mariam ne yawo?" Girgiza kai kawai ummi tayi tace "naji jeki cikin drawer d'in can zaki ga wani leda ki d'auka ki kaiwa umman mariam d'in"

Tashi tayi ta nufi drawer d'in tana bud'ewa taga ledan da aka ce ta d'akko tana d'agawa ta hango wani IV d'akkowa tayi tana dubawa invitation to the wedding fatiha of Mukhtar and Hajara ta gani.

"Lahhhh ummi watanki tara cif cif da aure kika haifeni" dak'uwa ummi ta watsa mata had'e da wurginta da purse d'inta dake gefenta tace "kinci gidanku mara kunyan yarinya." Da gudu ta fita tana dariya tare da fatan Allah yasa hakan ne dan har yau zuciyarta cike take da wasi wasi.

D'aki ta shiga ta d'akko handbag d'inta domin duba ajiyarta jijjiga kai tayi kafin ta d'auki blue hijab d'inta iya guiwa ta saka a rayuwarta tana son duk wani abu blue ko dan kallom idanunta ne ya sa oho.

Sallama tayiwa ummi sannan ta fita bakinta d'auke da addu'an Allah ya jiyar da ita alkhairi
Abin hawa ta tare zuwa anguwansu mariam.
Wani lab dake farkon anguwan ta sauka a lokacin zuciyanta ya tsananta bugu amma hakan bai sata karaya ba sai ma kutsa kanta da tayi ciki..

Gaisawa suka yi da matar dake kan kantan kafin ta sanar mata da abinda take dashi jinjina kai matar tayi ta buk'aci da ta bata jakanta ta zuge ta fitar da hanky biyu wanda dukka tayi musu alama da marker inda d'aya tasa P d'aya kuma U sannan wani da bata yi mishi alama ba ta mik'awa matar.

Sanar da ita tayi da ta dawo nan da awa biyu fita tayi a wajen tana adduan Allah ya jiyar da ita khairan.

Tana isa gidan mariam tasa ihun murna had'a da rungumeta kaman ba jiya suke tare ba.

Hira ne ya b'arke a tsakaninsu bayan ta gaida umma ta bata sak'on ummi.

"Ke ya jinyar zuciya?" Mariam ta jeho mata tambayan bayan sun zauna a tsakiyar gadonta.

Tab'e baki tayi tana zuk'an ruwan pure water da ta kawo mata
"Hmm ai kaman an zare min k'awata... Papa fa kullum kadin ya fita sai yazo ya ban baki haka da dare sai lallab'ani yake yi kinga ko dole in cire komi a raina."

Yatsina fuska mariam tayi tace " ni wallahi naji dad'i sosai da rabuwarku." A firgice ta d'ago tana kallonta kafin tace "me yasa sahiba?
Tab'e baki tayi tace " haka nan nake ganin baku dace ba wani gaja gaja dashi wallahi." Daeiya yuhaana ta sa tace "kefa uwar sharri ce dan dai kawai kinga mun rabun ne wai ancewa makaho ga ido yace da wari." Dariya suka sa had'e da tafawa.

Hira suka dasa sai wajen biyar yuhaana ta fara shirin tafiya mariam sai mita take yi wai yayi wuri Allah yasa suna fita ta samu napep suka tsare sannan suka yi sallama.

A dai dai lab d'in tace me napep din ya tsaya ta karb'i aika sannan ta shiga bata dad'e ba ta fiti sai zazzare ido take.

Napep d'in ta shiga zuciyanta na bugawa da k'arfi dan tsoron ganin abinda ta binciko amma hakan bai hanata yin Allah Allah ta isa gida ba dan ta bud'e ta gani.

_ni kaina sawwama Allah2 nake inga meye a ciki._


Sawwama Qawwama.

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now