💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 20.
Vote and follow me on wattpad @sawwama14
"Yasmin!" Ummi ta ambata a tsorace wanda yayi sanadiyan da yuhaana da matar dawo da hankalinsu ga ummi.
Cikin tsananin b'acin rai matar da ummi ta kira da yasmin take kallon ummi,k'ara rungume yuhaana tayi a jikinta kafin ta kalli ummi cike da takaici tace "Hajara! Menene haka? Haka zaki yi min wannan wani irin rayuwa ne Hajara ban tab'a tsammatan haka a gareki ba,why? Me yasa zaki min haka.
D'iyata ce abar wulak'antawa? Yau ko baki k'aunaci yuhaanasu a matsayin d'iyar da kika haifa da cikinki ba yaci ki k'aunaceta saboda ni saboda matsayinta a zuciyata a matsayina na 'yar uwarki y'ar k'awar mahaifiyarki kuma k'awarki aminiyarki a shekarun baya."
D'aure fuska ummi tayi ta juya ta koma cikin d'akinta janye yuhaanasu matar tayi daga jikinta ta bi bayan ummi ta bar yuhaanasu a daskare a wajen wai me ke faruwa ne? Shine tambayan da yuhaanasu tayiwa kanta wacece wannan matar da ke d'auke da irin k'wayan idanunta kuma wasu irin maganganu take yi me take nufi?
Ta jerowa kanta tambayoyin da bata da amsansu zaro manyan idanunta dake d'auke da blue eyeballs tayi lokacin da wani tunani ya d'arsu a zuciyan lokaci guda kuma ta fad'a d'akin jin hayaniyarsi.
"Yasmin ki fita idona fa,ji fita idona y'a ce nace bani so na gaji ai nayi kokari ko,ku rabani sa yarinyan nan in kuna sona kuna k'aunar farin cikina i hate her! I hate seeing her,tun randa ta shigo rayuwata,rayuwata ta d'aid'aice bani da wani sukuni a takura nake i can't do ir anymore." Ta fad'a tana rushewa da kuka
Cikin tsananin b'acin rai Yasmin tace "lallai Hajara ban san kin zama jahila ba sai yau wacce bata san me take yi ba menene laifin yarinya? Ashe ba zaki iya rik'e min d'iyata ba in har ba....."
"Yasmen!"
Suka ji an ambata Daga bayansu kamar yanda ummi tayi itama.Duk su ukun suka juya ganinsu zuwa ga papa har yuhaana dake son fitar da ita a cikin duhun da take,take son sanin laifinta a wajen ummi da matsayinta.
Dan tabbas tana cikin rud'ani me ke shirin faruwa da ita ne? Wai ya abun yake ne? Menene matsayinta a wajen bayin Allahn nan.
Sauri papa yayi ya je ya d'aga ummi dake durkushe tana gunjin kuka yayin da suka zuba musu ido rungumeta yayi a jiki bai damu da yuhaana dake wajen ba balle bak'uwarsu magana ya fara
"Yasmen saukar yaushe? Yasmen baki san cewan Hajara bata da lafiya bane me yasa zaki zo ki tayar mata da hankali haka sannan kisa yarinya a gaba kuna wasu maganganu?"
Fuskantar papa tayi murmushin takaici kwance a fuskarta,kafin tayi magana papa ya zaro idanu yace"what?! Yasmen me kike yi da blue lence?" Dafe kai yayi yace "ko kin san hakan zai iya haifarwa da yuhaana rud'ani ko kin san ya akayi muka samu muka goge kokonton da ke cikin ran yuhaana?"
Murmushi tayi tace " mmm mukhtar manyan duniya,you didnt change a bit always strieght to the point ko ka san irin zaman da iyalinka suke yi?"
Gyara tsayuwanta tayi ta rungume hannunta a k'irji tace "ban tab'a zaton ba zaka fi k'arfin gidanka ba mukhtar wai yau ace d'iyarka je rayuwan k'unci a cikin gidanka kuma wai a gaban uwarta? Batun rashin lafiya kuma ni ban ganshi a tattare da hajara ba hajara ta kasance mace me son kanta."
"Enough! Yasmen!" Ummi ta dakawa yasmen tsawa kafin ta kwace jikinta da ya gama yin laushi a wajen papa cikin k'araji tace "ya isa haka nan yasmen ba zaki zo har gidana ki nemi gaya mi. Magana ba akan wancan a bar." Ta nuna yuhaana dake rakube tana zubar da k'wala
Dariya ummi tayi tace "hahha lallai yau nice me son kai duk tsawon shekarun nan wa aka cutar sama dani? Ko dan ina yin shiru bana magana yasmen ki gaya min me akayi miki me akayi miki tsawin shekarun nan ni ban kiraku masu son kai ba sai ni zaki kira me son kai i live with this burden for my entire marital life,she is like a curse to me ta hana min jin dad'in gidan aurena da dangin mijina ke ki gaya min me aka yi miki zaki zo kina feleke min?"
Gaban yasmen taje ta tsaya duk yanda papa ya so shiga tsakaninsu abin ya gagara alama yayiwa yuhaana da ta fita da sauri ta fice.
Cikin b'acin rai yasmen tace " me aka min kike son sani an hana min yin aure my youth is snatched away from me an hana min jin dad'in menene so yau ko me aka miki kina gidan aurenki tare da wanda kike so ni fa? All thanks to you and your husband ban san menene dad'in aure ban sani ba ko har abada san d'and'ana abinda ake kira aure ko zama da masoyi ba sannan dan rashin imani the result that leads to this baki iya rik'ewa da amana ba sannan kina tambayana me aka min wannan shine kad'an daga cikin abinda aka yi min"ta juya zata fita kafin ta juyo tace "blue eye lence kuma kafi kowa sanin how obsess i am with it." Daga fad'an haka ta fita ta bar su tsaye sororo.
Hawaye ne ya silalowa papa yaje ya rik'e ummi dake tsaye sororo hawaye yana sintiri a fuskanta.
Papa ya tsargi kanshi ya d'ora laifin kocokan akan shi da bai aikata wannan kuskuren d'aya da sunan gyara ba da rayukan mutane da yawa bai b'aci ba da bai sa rayukan mutane da yawa cikin garari ba.
Wayarsa ce tayi ringing a kasalance ya zura hannunsa cikin aljuhu ya zaro ganin Elsaan ke kiransa yasa ya dangana ummi da gado kafin ya fice a d'akin zuwa nashi.
Turus tayi ganinta tsaye a k'ofar gidan hannunta ta kamo ta kai ta har bakin motanta kafin ta bud'e mata motar ta shiga sannan itama ta zaga ta shiga.
Kallonta tayi na wasu lokuta kafin ta zaro tissue tana goge mata hawayen da ya wanke mata fuska.
Bakinta sai motsi yake yi amma ta kasa furta komi saboda yanda halshenta yayi mata nauyi makoshinta ya bushe haka labbanta ganin hakan yasa yasmen ta jawo goran ruwa ta mik'a mata.
Kafa kai tayi ta kwankwadi ruwan sosai kafin ta sauke goran wasu sabbin hawaye na zubo mata bayan hannu ta sa tana gogewa ganin hakan yasa yasmen bata tissue.
Kallonta take cike da so da k'auna tana ji kaman ta tafi da ita amma ba dama duk yanda ta so ta daure sai da idonta ya kawo ruwa babban yatsanta ta sa ta d'auke k'walan.
Muryar yuhaana ne ya dawo da ita "ke...ke....kece mahaifiyata?" A firgice ta d'ago kanta tana mata wani irin kallo cikin sanyin jiki kuma ta girgiza mata kai.
Rintse ido yuhaana tayi tasan dama za ayi haka ta gaji da wannan rainin wayon nasu.
Da k'yar ta iya bud'e baki tace "dan Allah ki gaya min gaskiya in kece mahaifiyata alamomi da yawa sun nuna hakan kamar kalan fatan mu duk da na fiki haske sannan uwa uba k'wayar idon mu,in kece mahaifiyata ki gaya min ba zan ce ki so ni dole ba ko ki tafi dani inda kike har gobe papa da ummi sune iyayena ko da kuwa basu suka haifeni ba kawai dai ina ao in fita daga duhu ne."Numfashi yasmen ta sauke ganinta wanki hula zai kai ta dare cikin dauriya da dakakkiyar zuciya lokaci d'aya kuma cikin sanyin murya tace "yuhaana darling na rantse da wanda ya halicceni bani ce mahaifiyarki da ta d'au cikin wata tara ta haifeki ba......."
Sawwama Qawwama😘
