💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 16.
Wani uban birki ya ja cikin hanzari kuma ya bude murfin motar ya fito bai damu da duhun daren ba haka yayi tattaki ya isa wajen yana kara bude idanunsa dan ya tabbata ita d'ince.
Salati ya saka sosai da ganin ita dince kuwa amma ko alamun nuna saninshi bata yi ba.
"Hajara! Hajara! Hajara!!!" Ko gezau bata yi ba wannan dalilin ya sa hannu a jikinta dan tayar da ita wan razanannan ihu ta saka ta tana tureshi wanda hakan yayi sandiyar janyo hankalin mutanen da ke wucewa da wanda suke zaune daga can gefe suna harkokinsu.
Taso mishi suka yi wani ne yace "malam ya dai me zaka yi mata kazo zaka kama mahaukaciya da daren nan."
Kafin yayi magana wani yace "dan zalunci da neman kudin bala'i ba za ku bar mutane sai huta ba toh yau asirin ka ya tanu kai kam."
Nan fa y'an shaye shayen kan titin suka fara ihu fa suna ba zasu yadda ba ba don wani tsoho dake wajen ba da ya shiga tsakaninsu da papa da tuni sun qadamar mai.
Tsohon ne yace "ku tsaya Ku saurara muji ta bakinsa "kai bawan Allah yaya akayi, me matar nan tayi maka ko kuma menene alkarka da ita?"
Sauke kanshi papa yayi zuciyarsa na mishi d'aci addua yake a kasan ran shi ba zai tab'a yafewa wanda ya sasu a wannan halin ba ko ma waye,dan da gani ba sai an fad'a maka ba ummi bata cikin hayyacinta.
"Bawan Allah kai muke sauraro ko baka da abin cewa?" Tsohon ya tambayeshi.
Ajiyar zuciya ya sauke yace "baba wannan baiwar Allah da ka ke gani matata ce da bayan la'asr aka nemeta aka rasa tun wannan lokacin muke nemanta sai yanzu ina dawowa daga gidan y'ar uwarsu na ganta a nan gefen bolan nan amma Hajara ba mahaukaciya bace."
Kad'a kai baban yayi yace "Allahu akbar kabeeran ashsha ashsha duniya ina zaki damu ne yaro kana da tabbacin cewa wannan matarka ce?"
Papa yace "eh"
Wani daga can baya yace "menene shaidarka da ba zamu d'auki mata mu baka ba bamu san gaskiyar magananka ba."
Wayarsa ya zaro ya danna nunmbern Hassan
A lokacin suna zaune hankalinsu ya ninka da tashi ganin har goma saura babu labarin papa bare ummi.Cikin rawar jiki Hassan ya d'au kiran papa cewa yayi "Hassan ka shiga gidan Alhaji sadi kace mishi nace ya taimaka ya kawoka kai da yuhaana nan kawo inda hali ya taho da uwar gidansa."
"Toh toh papa,bari inje" Hassan ya amsa cikin farin ciki dan zuciyarsa na bashi anga ummi ne
Nan da nan ko ya shaidawa yuhaana yanda papa yace ai kuwa basu tsaya b'ata wani lokaci ba suka kama hanya.Duk abin nan da ake yi ummi na rakub'e a gefe ba zaka ce dan ita ake tsayuwan ba jugum tayi kaman mai tunanin wani abu.
A wannan halin su yuhaana suka iso da alhaji sada motar bata gama tsayuwa ba yuhaana ta balle ta fito a d'ari ta nufi umminta tana kuka.
Runguma ta kaiwa ummi,tana fadin "ummi ina kika tafi ki barmu?" ita ko ta tsala k'ara ta tureta toh fa zuwa wannan lokacin papa ya fara tsorata wai shin me ke faruwa ne? Yuhaana kam sororo ta tsaya tana kallon mutane d'aya bayam d'aya ta kasa gane me ke faruwa.
A hankali tace "ummi nice fa, nice fa yuhaanarki" inaaa ummi b'uya take a bayan tsoho
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un ta mai da kallonta ga papa
"Papa me ke faruwa me ya sami ummi? Ya ummi take gudunmu,me ya sami ummina?"
Yuhaana ta jerowa papa tambayoyi tana kuka.
