💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 10.
Vote and follow me on wattpad @sawwama14
Yau satin yuhaana biyu da dawowa daga asibiti ta ware tsab muryarta ma ta fito.
Ko da wasa ba a k'ara tayar da abinda ya faru yanzu kam son tafiya zaria shi yake d'awainiya da ita sosai tayi kewan mutanen wajen tana son ganin y'an kakanninta.
Tana shirin mik'ewa ta tafi wajen papa wayarta ta hau ringing murmushi tayi ganin me kiran,shi dai baya gajiya da kiranta .
Assalamu alayka" ta mishi sallama cikin nutsuwa.
Lumshe ido yayi wani dad'i na ratsashi hak'ika yarinyan ta shiga ranshi sosai.
"Amin wa alayki assalam babyna" dariya tayi tana rufe bakinta da hannunta shima dariyar yayi yace "ya akayi ne? Me ya baki dariya ko kalmar babyn ne ya baki dariya."
Yanzun ma sai da ta dara tace " oh ni Allah ya had'ani da lawyer rabin hirarmu dai tambaya nake sha." Sassanyan murmushi ya saki yace "toh naji na daina although gwara ki saba fa... Yuhaana!" Ya kira sunanta in a serious tune
Jiki a sanyaye ta amsa
"Yuhaana kamar ko da yaushe ina k'ara sanar miki ni sonki nake ba kuma da wasa ba ki bani dama in turo magabatana ak'alla ko sadaki a yanke min dan ni bana so a d'auki lokaci ban mallakeki ba please ki amince min."Ajiyar zuciya ta sauke tace " ibrahim ba wai ina k'inka bane amma ina so ka gane gaggawa aikin shed'an ne yaushe akayi daren da har gari zai waye? Bana tunanin munyi cikakken sati biyu da had'uwa da har kake wannnan batu na kawo sadaki."
"A wannan al'amarin babu batun gaggawa yuhaana me zamu jira shi doguwar soyayyan nan ba wani amfani gareta ba,in fahimtar juna ne a sannu zamu fahimci juna sannan duk dad'ewarki da saurayi ko dadewar saurayi da budurwa basa tab'a sanin dukkannin halin juna har sai sunyi aure,pls ki bani dama baby." Ibrahim ke magana a marairaice.
Lumshe ido tayi maganganunsa na tasiri a cikin zuciyarta cikin sanyin murya tace " shikenan ibrahim zan baka dama amma ka bari inje zaria in dawo tukun."
Da sauri yace "zaria kuma? Yaushe zaki zaria,yaushe kuma zaki dawo?" Dafe kanta tayi tana dariya tace "ni kam da d'an jarida da lawyer ban san wanda yafi wani iya tambayan k'ure ba,yanzu wannan jerarrun tambayoyin wanne zan fara ansawa?"
Murmushi yayi yace " eh naji kuma dukka zaki ansasu d'aya bayan d'aya "
"Toh shikenan gobe nake so in tafi dama ya kamata ace na tafi tuntuni toh amma kuma sai na kwanta rashin lafiya amma inshaaAllah gobe iwar haka ina jikin tsohuwar kakata." Ta fada cike da murna.
Sosai muryarsa yayi sanyi yace "yanzu baby gobe zaki zaria and you didnt bother telling me haba haka soyayyar tamu tace miki? When are you even coming back kwana d'aya dai zaki yi?" Kwalalo ido waje tayi tace "tqb ai sai an gani in na tafi wallahi ka san rabona da can kuwa."
Yace "toh shikenan nima kullum ina hanya kenan tunda ba yanzu zaki dawo ba amma gaskiya kafin ki dawo za a zo a sami papa daga gidanmu."
A haka dai suka d'an tab'a hirarsu suka yi sallama ido ta ware had'e da dafe bakinta ganin yanda lokaci ya gudu ashe dare yayi bari ta gani in ummi bata tafi d'akin papa ba taje ta sameshi.
Allah ya taimaketa taji motsin ummi na wanka. Direct dakin papa ta nufa sallama tayi had'e da turo k'ofar da sauri papa ya tura hoton hannunsa kasan pillow yana goge hawayen idonsa a fakaice.
Sararo tayi tana kallonshi amma sai ta basar ganin yanda papan yake k'okarin boye hoton hannunsa da damuwar dake kwance a kwayar idonsa.
Dakewa tayi kaman bata ga halin da yake ciki ba ta k'arasa kusa dashi ta zaune.
Hanunsa ta riko tace " papa barka da gida" bata bari ya amsa ba tace "papa tunda naji sauki gobe in tafi zaria?" Murmushi ya k'ak'alo yace " hmm yuhaan papa Allah ya kaimu goben sai ku tafi da Hassan shima tunda zai koma gobe." Tsallen murna tayi ta rungume shi.Murmushi kawai yayi idanunsa na kawo k'walla lokacin da ta juya ta tafi cike da murna.
Zaro hoton yayi ya cigaba da kallo motsin shigowa ya kuma ji har zai hanzarta k'ara b'oye hoton amma sai yaga ummi ce da sauri ta k'araso ganin damuwa a fuskan mijin nata amma me tana k'arasowa taga hoton hannunsa sai ta tamke fuska tace " yanzu inda yuhaana ce ta shigo fa?" Ta tambayeshi ranta a had'e.
Bai lura da yanayin fuskanta ba yace "yanzu ta fita." K'walo idanu tayi tace "ban gane yanzu ta fita ba,kana nufin taga hoton kenan?" Girgiza mata kai yayi yace " bata gani ba na b'oye kafin ta shigo."
Cikin b'acin rai da takaicin da ban san na meye ba tace "gaskiya papa ka dinga kiyayyewa ni banga ma amfanin fitar da hoton nan ba in banda tarin b'acin rai ka tisa hoto a gaba kayi ta kuka haba? Gaskiya ni kar wannan sakacin naka yasa yuhaana ta ci karo da hoton nan kuma kai sanin kanka ne ganin hoton nan na dai dai da tonuwar asirinmu."
Hannunta ya rik'o cikin sanyin murya yace " Hajara har kullum bani da bakin baki hakuri ban san da wani kalma zan baki hakuri saboda irin yanda muka kuntata miki ba tare da baki dama ko shawara dake ba ki yafe mana amma ki sani kaman yanda nake gaya miki a ko da yaushe ban tab'a dana sanin abinda muka miki ba musamman in na kalli yuhaana sai naji wani sanyi ya rastani farin cikina na raguwa ne a lokacin da na tuna ni kad'ai nake jin dad'in nan ba tare da other half...." Fizge hanunta tayi tace "other half indeed."
K'ara matsota yayi yace " kiyi hak'uri hajara kin san akwai shak'uwa me tsanani tsakaninmu shi yasa a wasu lokutan nake gagara controling kaina soyayyarmu da shak'uwarmu me k'arfine daga Allah Hajara ki dinga yi min uzuri sannan ki sassauta fushin nan a garemu ko dan darajar yuhaana."
Jikinta ne yayi sanyi wanda hakan ya sata kwantar da kanta a jikin mijinta abin alfaharinta ko me papa yayi mata duk girman laifinsa a wajenya yafaffene saboda soyayyar da suke yiwa juna saboda kyakyawar zuciyarsa.
A wannan daren yuhaana ta gagara samun bacci nagartacce da ta rufe ido fuskan papa take gani cike da damuwa ga hawaye na sintiri a idonsa sannan ta rasa me papa yake b'oyewa da ya ganta.
Tsaki taja a fili tace " toh me ke damun papa ne? Me papa ya ke aikatawa da bai son a sani? Damuwar da yake ciki fa? Oh ni Yuhaanasu rabbi ka kawowa zuriyarmu farin ciki me d'orewa."
Sawwama Qawwama😘