YAY page 7.

1.5K 133 24
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖





By Sawwama A.






Page 7.






Follow and vote for me on wattpad @sawwama14


*wata sabuwa kuma 😂wasu sunce Yuhaana fa da Hassan ta dace masu karatu hala kun manta da wanene Hassan a wajen Yuhaana ne?  Toh muje zuwa dai dan sanin ya abun yake*




Tunda Hassan ya sada ta da mazauninta bata k'ara hango k'yallinsa,gaba d'aya a takure take a wajen saboda idon mutane da suka yi yawa a kanta,harara ko tasha shi yafi cikin trailer a wajen y'ammatan wajen mussaman k'awayen amarya dan ganin zata yi musu karan tsaye a al'amarinsu lura da suka yi hankalin abokan angon duk yana kanta.

Zamanta a wajen ko maza sama da biyar sun dumfareta amma ko kad'an bata d'aga kai ta musu duba biyu baya ga sallamarsu da take amsawa wannan ma domin ya zamar mata dole ne.

Ganin hakan da samarin suka yi yasa kowa d'an shakkanta sai suka kame kansu gudun suma karta yarfasu.

An d'au lokaci ana gudanar da taron har aka buk'aci da amarya da ango su fito su taka rawa sannan filin na k'annen amarya ne suzo suyi mata manni.

Amarya da ango sun fito hannunsu sak'ale da na juna suja fara takawa a hankali yayin da k'annen amarya suka fara tururuwar zuwa musu lik'i.
Yuhaana na zaune tana kokontan taje ne ko ah ah dan ita sam Allah ya gani ba wai son lik'in nan take yi ba dan ta d'aukeshi a almubazzaranci gashi papa har da bandir d'in 20 20 naira ya basu ita da Hassan.

"Ke ba zaki je kiyi musu lik'i bane dan nuna musu ki na taya su farin ciki?" Muryar saudat y'ar gidan baba shehu ya katse mata tunani. Daga kai tayi tana dubanta ga mamakinta murmushi saudat d'in ke dokanta dashi sab'anin sanin da tayiwa y'ammatan familynsu da in sun ganta harara,tsaki har dasu tofar da miyau shi ke had'asu, babu mamaki duk murnan bikin ne.

Itama murmushin ta k'ak'alo tace "yanzu nake shirin tashi." Da fad'in haka sai ta mik'e suka jera da saudat d'in bandir d'in kud'in ta fidda daga cikin purse d'inta ta b'are ta fara lik'e amaryar da shi gudun kar ta lik'awa ango tayi laifi duba da irib hararar da amaryar ke watsa mata.

Tana gab da gama lik'a mata saudat dake bayanta ta hankad'ota sai jikin ango shi kuma ya sa hannu biyu ya tarota gudun kar ta fad'i wani kuka amaryar ta fashe da shi,nana k'anwarta ce ta k'araso ta finciketa daga jikin ango ta watsa mata wasu tagwayen marurruka dama da hagu.

Kuka ta fashe dashi ta durk'usa a wajen hayaniya suka fara yi mata a kai hankalin mutanen wajen gaba d'aya ya tashi.
Amaryar ce ta fara magana"burinki ya cika kin b'ata min biki kaman yanda kika d'au alwashi toh ta Allah ba taki ba muguwar yarinya." Daga gefe aka ce wai ba k'anwar amaryar bace (saboda yanayin ankon jikinta na kannen amarya) aunty bilki ce da daman tana da cikinta tace "Allah suturi bukui wagga abin za a had'a da zuriyarmu y'ar mak'ota ce me mugun shshigin tsiya tana bak'in ciki d'iyar mu na aure ita bata samu miji ba sai d'an banzan bin mazan bala'i shine tsabar kwartanci har a cikin mutane ma sai kin nuna ke karuwa ce, nana maza ku fitar da ita tayi kad'an da b'ata mana biki,biki yanzu aka fara,kai salmanu rik'e matarka ki koma ku zauna a cigaba da gashi."

Figanta su nana da sauda suka yi suka fitar da ita a hall d'in kuka take kaman ranta zai fita wannan irin Tozarci haka da me yayi kama? Yau ita ake dangantawa da karuwa,me yayi zafi haka?
Tafe take tana kuka, ko neman Hassan bata yi ba  ta kama hanya tafiya kawai take amma ita kanta bata san inda take jefa k'afanta ba.

Wata benz ce ta slow down a gefenta tana tafiya dai dai ita ganin haka yasa ta k'ara saurinta,zuge glass d'in motan yayi yace "bai dace ba kina y'a mace mai daraja ki dinga tafiya haka a k'asa kina kuka ba,komi yayi zafi maganinshi Allah,ki riki sunan Allah a bakinki zaki ji sassauci game ga abinda kike ji." Gyad'a mishi kai kawai tayi ba tare da tace komi ba.

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now