YAY page 15

1.2K 139 9
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖







By Sawwama A.






Page 15.





Follow and vote for me on wattpad @sawwama14


*Sarah you are bae*

Sai dai me ringing din wayan taji a kan kujera wayar tana cikin d'akin.

Fita suka yi suka fara shiga mak'ota duk da cewar ummin ba mai shige shigen makota bace.
Balle da wannan yamman.

Amma sai me? Babu ummi babu labarinta cikin gidan suka shigo da sauran yaran gidan kowa yayi cirko cirko hatta momy tasha jinin jikinta yanzu.

Hassan ne ya shigo ya gansu cirko cirko tattare giransa yayi yace "ku kuma fah lafiya kuke tsatsaye kan zakaru?" Yuhaana bata iya bashi amsa ba dan ita duk ta rasa tunanin da zata yi k'wak'walwan ta ya tsaya cak.

Mus'ab ne yace "ummi ce bamu gani?" Tsaki ya ja wanda ya sa yuhaana ta d'ago da mamaki tana kallonshi sai cewa yayi "wani maganan banza ne haka ummin ce kuma ba a gani ba sai kace wani object ko yarinya,kai wata ummin ma tukun?"

Jidda ce da k'iris ta ke jira ta fashe da kuka tace "ummina" sororo yayi yana kallansu mai da kallonsa ga momy yayi yace "wai momy me ke faruwa ne?" Hannunta ta dan watsa tace "ni ina zan sani shigowata kenan suka ce min basu ga Hajara ba."

Wayarsa ya zaro ya danna kiran papa ya kora masa bayani.

Suna nan zaune tsakar gidan babu wanda ya iya shiga d'aki minti sha biyar ya kawo papan dan dama yana hanya dan yazo yaci abinci da iyalinsa.

A gigice ya shigo gidan yuhaana na ganinshi taje ta fad'a jikinshi tare da fashewa da kuka sai lokacin taji kuka ya zo mata.

Tab'e baki momy tayi ta kau da kai d'ago yuhaana yayi daga jikinshi yace "yuhaa wai me ke faruwa ne?"

Cikin sheshek'a tace papa nima ban sani ba kawai...... Nan dai ta mayar masa da abinda ya faru.
Hulan kansa ya cire kafin yace wani abu momy ta fara magana cikin b'acin rai.

"Haba dan Allah Hajara fa ba yarinya bace ba za kuma a shigo gidan nan a sace Hajara yuhaana na cikin gidan a barta ba ko kuma ace bata ji motsi ba kawai wata kila tayi nata wajen ne."

Kallonta papa yayi cikin sanyin murya yace "Jamila abun dubawa a nan shine Hajara ba mai yawo bace duk inda hajara zata biyar yayi mata a gida,sannan fita ba da izinina ma ba halinta bane,balle a wannan lokaci na dare."

Tura dan kwalinta tay gaban goshi dan ganin take gugar zana yake yi mata.

Yanda kan Yuhaana ya k'ulle bata iya tunanin komi sai kuka haka na papa ma gabaki d'aya ya rasa ina zai fara dosa toh ko zaria ta tafi? Toh amma a bisa wani dalili? Ummi ba mai yaji bace tsawon shekarunsu a tare bata tab'a zuwa gida dan b'acin ba ko ba da saninsa ba har a wancan lokacin da abin ya faru bata je gida ba me ke faruwa ne? Ya abun yake ne?" Yayi kansa tambaya amma sam bashi da amsa.

Wayar yuhaana ne ke ta ringing ba kakkautawa amma ko kallon wayan bata yi ba haka ya ankarar da papa ya zaro wayarsa dan ya gwada kiran zaria yaji.

Number mama ya kira kai tsaye.

"Salamu alaikum" mama ta ansa wayar da sallama ahiru yayi dan bai san ma ta ina zai fara ba.

"Salamu alaikum hajara kina jina?" Bamm zuciyarsa ta buga ya san bata zaria mama tayi zaton ummi ce dan in dai aka kirata da wayan papa a wannan lokacin toh ummi ce.

"Wa alaiki salaam mama ina jinki an wuni lafiya?" Ya daure ya amsa mata
Gaisawa suka yi sannan ya kashe wayar tunaninsa ya tsaya cak.

Salamu alaikum sallaman mariam da ummanta ne ya katse shirun da yake cikin gidan amsawa suka yi sannan suka shigo

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now