YAY page 13.

1.2K 182 17
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖






By Sawwama A.






Page 13.





Follow and vote for me on wattpad@sawwama14.




*sorry for the short chappy I am also here busy entertaining myself*
*Ni dai a iya sanina comment dinku kaman wani interaction ne tsakaninmu domin sanin ra'ayinki ba Ku karanta ba kuyi likimo also kuma wattpadians it doesn't take a lots for u just to punch the vote button pls duk a gyara Allah bar kaunar dake tsakaninmu amin.*



Bayan tafiyan Ibrahim yuhaana taje ta sami mama ta fad'a mata yanda suka yi dashi
"Yauwa hakan yayi ni zan kira ita Hajaran in yaso sai ta sanar da papan naku ko?" Cewar mama

Gyad'a kai tayi cike da gamsuwa tace "eh hakan yayi mama."

Layin ummi mama ta kira ta kora mata bayani  sosai ummi taji dadi ta tabbatarwa da mama papa na shigowa zata sanar dashi in yaso sai su zauna cikin shiri.
Ko da papa ya dawo ummi ta sanar mishi da batun jugum yayi tabbas yayi farin ciki amma zuciyarsa fal yake da tsoron mai zai je ya dawo yana tausayin yarinyan yana so yaga ranan da zai aurar da ita sai dai yana tsoron shiganta wani hali duba da yanda al'amarin aurenta ke lalacewa in akayi duba da banbancin halittansu sai ayi kokarin sheganta masa y:a.

"Shikenan Hajara zan kira yuhaanan ta bani details kan yaron zan yi bincike kansa kaman yanda na tabbata ba zasu zo neman auranta ba har sai sunyi bincike." Papa ya sanarwa da ummin haka.

Cikin sanyin murya tace "toh papa Allah ya jiyar da mu alkhairi amin."

Haka ko akayi papa ya kira yuhaana ya mata tambayoyi kan ibrahim ta sanar dashi iya abinda ta sani ya gamsu sosai shi da kanshi ya binkita iyayen ibrahim da shi kansa ibrahim din kuma ya gamsu da abinda ya samu sannan hankalinsa ya kwanta ya kuma sanarwa da ummi.

Sati d'aya da maganan magabatan Ibrahim suka zo babban gida papa ya turasu inda zasu sami alhaji da sauran yan uwan papan maza.

Hannu bibbiyu aka karb'esu kasancewar alhaji na wajen,bayan gaisuwa da bude taron da addu'a wan mahaifin ibrahim ya gabatar da abinda ya kawosu na neman auran yuhaana.

Su tabbatar musu da cewan su ba da wasa suka zo ba dan dama abinda suke jira kenan d'an nasu ya kawo matar aure,saboda haka sun zo da kudin gaisuwa har da sa rana ma in an amince za a basu yarinya.

Alhaji ne ya kira papa ya sanar dashi k'udurinsu papa yace ba komi duk abinda alhajin ya yanke daidai ne.

A bisa wannan dalilin Alhaji ya aminta dasu aka karbi kudin gaisuwa da sa rana inda suka nemi a saka wata d'aya alhajin yace "ah ah sai dai zai iya musu adalci a sa wata biyu saboda suma su samu su kintsa da kyau.

An sa rana wata biyu masu zuwa inda suka ba da dubu d'ari kudin gaisuwa dubu dari da hamsin kudin sa rana kasancewar ba kayan sa rana suka kawo ba sadaki kuma sai ranan daurin aure inda alhaji yace su kawo dubu hamsin.

Nan da nan baba Hamisu yaji ranshi ya b'aci wai wannan yarinyan da suka tsana ne aka kawo mata wannan dukiyar,babu abinda yake yi sai gyad'a kai.

Kallon Elsaan yayi bayan ya sauke wayan yace "sorry babana ke magana,yanzu kace kana so kayan da muke supplying muku ya zama ninkin na da?"

Elsaan bai amsa tambayan papa ba sai dai ma shi da ya watsawa papa tambayan da bai shafeshi ba
"Alhaji mukhtar aurar da diyarka zaka yi ne?"

Murmushi yayi yace "eh Elsaan diyata nake shirin aurarwa."

Da mamaki Elsaan ke gyad'a kai yace "lallai ban yi zaton kana da babbar d'iya haka ba,shekarunta nawa?"

Gyara zama papa yayi dan shi in abinda ya shafi sanyin idaniyarsa ne baya gajiya da batun "shekarunta ishirin on the 5th of next month zata cika 21."

Waro idanu Elsaan yayi yace "lallai alhaji mukhtar tsoho ne kace ka kusan rike jika." Dariya papa yayi yace "alai elsaan ina tsufan kawai dai anyi aure da wuri ne ina da shekarunka yuhaana ta kai 12 lokacin,kaima its high time ya kamata ka ajiye iyali haka nan Elsaan,dukiyan nan ana ta tarata babu masu ci sai al'umman gari."

Sosa goshinsa Elsaan yayi yana murmushi kasa kasa dama shi haka ne im dai za ayi mishi maganan aure sai ya tsinci kanshi da jin kunya,shi matsalar sa daya matan ne ko wacce da kalan rashin kunyan da take zuwa dashi.

"Haka ne alhaji mukhtar Allah dai yayi mana zabi,matan ne sai a slow."

Gyara zama papa yayi ganin Elsaan din ya sake ya bashi dama har suna irin maganan nan dashi yace "alhaji Elsaan with your status,arziki da kyaun suffa uwa uba hali babu macen da zata ki ka na tabbata akwaisu da yawa that are throwing themselves over you."

"Thats the point ban so mace ta soni dan wani abuna sai dan Allah wannan na d'aya dga cikin dalilan da yasa ban yi aure ba har yau, alhaji mukhtar zan gaya maka abinda ko mahaifiyata bata sani ba,ummana tayi fadi tashi kaina da kanwata ta tsaya tsayin daka ta kare mana dukiyarmu wannan dalilin yasa kaga ina tsoran auro wacce zata zo ta shiga tsakanina da mahaifiyata ko k'anwata."

Gyada kai papa yayi yace "kana da gaskiya dan wasu matan basu da amana Allah dai ya tayaka zabi,kai dai ka kau da idonka ga muggayen aiki duk da cewar duniya ta shede ka a wannan zamani samun matashi kamanka mai ji da lafiya ga arziki kuma bai aikin asha sai daidaiku,ka cigaba da kare kanka a kuma yi kokari a saukewa jiki hakkinsa."

Murmushi kawai Elsaan yayi ba tare da yace komi ba suka cigaba da tattaunawa akan harkar business.








Sawwama Qawwama😘

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now