💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 8.
😂😂 *yau baba sa'idu ya ga bone wajen masoyan yuhaana, ni dai sawwama babu ruwanaruwana* 🏃🏾♀
K'ara ta k'wala tana mishi magiya "baba sa'idu kayi min rai ka taimakeni kar ka keta min haddi,baba sa'idu kai me kare min mutuncina ne a matsayinka na uba a gareni k'anin mahaifina na rok'eka kayiwa Allah ka dubi matsayina a wajenka kar ka aikata aikin da na sani."
Baba sa'idu kam bai ma san tana yi ba k'ok'ari yake yaga ya sada hannunsa da fatar boobs d'inta sai gurnani yake kaman zakin da yaga fresh meat etoh fresh meat d'ince.
Ihu take da iya k'arfinta wanda hakan ya tunzurashi ya wankawa bakinta mari,sanadiyar da yasa jini ya fara tsiyaya daga bakin nata, bai ko damu ba sai ma kokarin cusa kanshi cikin hijabinta da yake yi.
Papa na tsakiyar jama'a a can babban gida wato family house d'insu yaji zuciyarsa na wani irin tsinkewa haka nan jikinshi ya bashi ba lafiya ba,dole something terrible is going to happen to him or someone close to him tsam ya mik'e ya zari mota ya nufi gida,har zuwa lokacin jikinshi bai bar b'ari ba zuciyarsa tana cigaba da tsinkewa.
A waje ya parking motar ya fito hannunshi har b'ari yake yi wajen bud'e k'ofar gidan kakari yake ji had'e da sautin kuka sunan Allah ya fara kira ya nufi d'akin ummi inda yake jin kakarin
Innalillahi wa ina ilaihi raju'un ya furta da k'arfi lokacin da ya d'aga labulan d'akin yayi mugun gani ya gani da har ya koma ga mahallicinsa wannan hoton ba zai d'auke masa ba,k'aninsa da suke ciki d'aya uwa d'aya uba d'aya yake k'ok'arin haik'ewa y'ar cikinsa?.
Wani duhu ne ya gilma masa wanda ya kusan kayar dashi har sai da ya dafa k'yauran d'akin.
Masu karatu zaku yi mamakin cewan baba sa'idu fa bai ma san papa wai ya shiga ba saboda yanda ya shagala da tsotsan nonon yuhaana yayin da ya tokare mata wuya da hannu d'aya baya tunanin hakan na iya janyo ta rasa rayuwarta sosai ta fita hayyacinta wanda ban da harbe harbe da take yi da k'afa da k'ok'arin k'wace kanta ba abinda take yi duk kuwa da yanda k'arfinta ya k'are.Wani kukan kura papa yayi ya yo kan sa'idu ya finciko shi kumm ya had'ashi da bango,dukkanshi yake ta ko ina yana kuka yana fad'in "ashe sa'idu zaka iya kwanciya da y'ar cikinka? Diyar dan uwanka ban taba sanin dabbancinka ya kai haka ba, me nayi muku ne kuke k'ok'arin ganin bayana d'iyata kake k'okarin ketawa haddi sa'idu "zuwa lokacin baba sa'idu ya galabaita papa ko kuka yake kaman ransa zai fita a wajen ya durk'ushe yana wani irin kuka mai cin rai yayinda baba sa'idu ke kwance a tsakar d'akin yana fitar da numfashi da kyar.
Yuhaana ce ta cukuikuye jikinta cikin hijabin tayi k'okarin jan jikinta zuwa inda papa yake durk'ushe yana rera kuka kaman d'an yaron da uwarsa ta mutu.
Da k'yar take jan jikinta saboda yanda kirjinta yake mata wani irin zogi ga numfashinta kanshi da kyar take fuzgoshi saboda yanda baba sa'idun ya mak'ureta, hawaye ma ya gagara fitowa daga idonta dafa papan tayi magana take son yi amma abin ya gagara k'arshe ma sai sulalewa tayi a wajen ta sume.
A gigice papa ya mik'e yana kiran sunanta had'e sa jijigata amma shiru bata motsa ba rasa yanda zai yi yayi k'arshe dole ya sunkuceta ya fita da ita a gidan a bayan motarsa ya kwantar da ita ya k'ara gyara mata hijabin jikinta dan k'ara suturtata kafin ya shiga motar yayi ribas a d'ari driving yake ya na kukan tausayin kanshi da d'iyarsa,hak'ika sa'idu ya cuceshi ya ci amanarsa.
Hospital mafi kusa ya mik'ata inda aka karb'esu da gaggawa ganin cewa patient d'in bata cikin hayyacinta.
Ana shiga da ita d'aki ya fara neman layin ummi sai da wayar ta kusan tsinkewa ta d'aga ko sallamar da take kwararo mishi bai amsa ba yace "ki sameni a garkuwa hospital yuhaana ba lafiya" bai jira abinda zata ce ba ya katse kiran cikin tashin hankali ummi ta zari mayafinta a yanda taji muryan mijin nata kaman yana kuka shi tsoratar da ita ko sallama bata yiwa kowa ba ta fita tuni hawaye ya fara sunturi a fuskanta tsoronta d'aya Allah yasa ba wani mummunan abune ya sami yuhaananta ba a cikin wannan tashin hankali ta isa hospital d'in inda hankalinta ya ninnka da tashi ganin halin da papa ya shiga lokaci guda ya zabge ya fita hayyacinsa.
K'arasawa gareshi tayi tana tsananta kukanta "papa ina yuhaanan? Me ya sameta ni dai lafiya k'alau na fita na barta tana shan baccinta,MUKHTAR ka gaya min abinda ya sami diyata" ta rike rigarsa tana k'ara sautin kukanta.Rungumeta yayi a jikinshi yana bubbuga bayanta kalma d'aya ya kasa fitowa daga bakinshi abinda ya k'ara d'aga hankalin ummi ya tsoratar da ita,lallai duk abinda ya sami yuhaana ba k'aramin abu bane.
Doctor ta fito daga d'akin da yuhaana take kwance abinda ya sa papa sakin ummi kenan ya rik'o hannunta suka bi bayan doctor d'in.
Kyakyawan doctor dake zaune a gaban wani k'awataccen table duk da kasancewarta visting doctor a hospital d'in a bisa table d'in an d'ora wani kyakyawan frame dake rubuce da sunan doctor d'in wato DR ZAKIYYA
Gyara farin glass d'in idonta tayi ta fuskancesu gyaran murya tayi tace " yarinyanku ba wani abu ke damunta ba illa shock da ta samu sannan wuyanta da aka strangling shima zai d'an yi mata ciwo saboda yanayin shak'an amma bayan wannan bata d'auke da wani damuwa kuma Alhamdulillah Allah bai bawa azzalumin daman yiwa rayuwarta illa bai samu galaba ba.
A yanzu haka ta farfad'o amma munyi mata alluran bacci domin zuciyarta da k'wak'walwanta su sami hutu,sai a kula a sa ido akan rayuwanmu mu y'ay'a mata saboda rayuwarmu da tarbiyarmu tana cike da had'ari ne sai da taimakon Allah da kuma sa idanu na iyaye komi na rayuwar y'a mace ke tafiya daidai. Allah ya kiyaye gaba amin."
"Sannan please ayi k'okarin samar mata suturu dan yanzu ma rigar asibitine a jikinta" amsawa suka yi da toh had'e da yi mata godiya.
Sosai jawabin yarinyan ya burge ummi amma tsananin tashin hankali da ta tsinci kanta najin labarin da d'mautata ya gigitata "wani azzalumin ne ya nemi ketawa d'iyata haddi" ummi ta jefowa papa tambaya bayan fitowarsu daga office d'in doctor.
Kafin papa ya kai ga bata amsa wayarsa ta hau ringing "Hajiyarmu" shike haskawa a kan screen d'agawa yayi had'e da sallama.
"Muntari ka taho gida ka sameni yanzun nan cikin gaggawa mara mutuncin yaro" ta katse kiran rintse idonsa yayi kafin ya bud'esu a kan fuskan ummi
Cikin dashewar murya yace "Hajara jeki samarwa yuhaa sutura da abinda zata iya sha in ta tashi,ni bari inje hajiya tayi kirana." Zata bud'e baki tayu magana yace " Hajara ki adana duk wasu tambayoyinki har inje in dawo dolene in warware miki abinda ya samu d'iyarmu.
Gyad'a mishi kai tayi suka lek'a d'akin da yuhaana ke kwamnce tana bacci sai ajiyan zuciya take saukewa dukkansu sai da k'walla ya taru musu na tausayin d'iyarsu.
Sai da papa ya fara sauke ummi a anguwan sarki inda gidansu yake kafin ya wuce unguwar dosa gidan mahaifansa.
Ummi tayi mutuk'ar mamaki ganin palonta a wargaje amma mamakinta ya kau lokacin da taga towel a wulle a gefe duk yanda aka yi a palonta aka sha artabu dan har da d'iso d'ison jinin sa'idu sama sama ta kintse palon dan hankalinta na wajen d'iyarsu.Kallon mamaki papa ke bin hajiya yaya rabi yaya Hamisu da sa'idu sai alhaji dake zaune yana jijjiga kai yana murmushi jin yanda aka juya abun da ky'ar ya iya tattaro yawun bakinsa yace " haba hajiya haba hajiya ta yaya za ayi ace yuhaana ita ta nemi sa'idu alhalin yana a matsayin k'anin mahaifinta,asalima ni d'iyata me kamun kai ne da tarbiya sab'anin...."
"Aiyo nawa d'iyan shine mara kamun kai ko? mara tarbiya? Lallai muntari wuyanka ya isa yanka ni uwar da na baka tarbiya kake cewa diyana bashi da tarbiya."
Wani irin sarawa kanshi keyi yace "hajiya Allah ya huci zuciyarki ni ba nufina ba kenan kawai dai ina ganin ya kamata ayi bincike kafin a zartar da hukunci a bawa mai gaskiya gaskiya a hukunta mara gaskiya.""Wani bincike za ayi mukhtar bayan yarinyan nan jiya a wajen dinner sai da ta nuna halinta k'iri k'iri a idon mutane ta rungume mijin yarinyan nan idan ba mara kamun kai ba wa zai yi haka."
Cewar yaya Rabi.Carab hajiya ta cafe "yoh ke kuwa rabi ba dole ba ai dama dole ayi haka ta yaya barewa zata yi gudu d'iyanta tayi rarrafe in yahanasu ba tayo halin.....
"HAUWA'U! " alhaji dake zaune yana jinsu tun farko bai tofa komi ba ya dakawa hajiya tsawa da ainihin sunanta abinda yaran nasu basu tab'a cin karo dashi ba tsawon rayuwarsu.
Tirk'ashi!
Sawwama Qawwama😘