YAY page 14.

1.2K 124 19
                                        

💖YA ABUN YAKE? 💖




By Sawwama A.






Page 14.




_vote and follow me on wattpad @sawwama14_

*Meela Adeel my dear daughter I am using this page to thank u for all the love and concern and also an apology ko baby amm😊*






Yuhaana bata san me ake ciki ba suna kitchen ita da ramlatu wayar ta dake aljuhun sweater dinta ya fara ringing.
Fita a kitchen din tayi tana amsa wayan.

"Babe guess what?" Dan tura baki tayi kaman tana gabanshi tace kaima ka san ni bani wani son canki cankin nan just tell me what"

Lumshe idonsa yayi ya rik'e wayar da kafad'arsa yana k'okarin zare gown din dake jikinshi kasancewar yanzu suka fito wani shari'ar da ya winning ga kuma d'addadan labarin da ya samu abbansa ya tura masa a wayar.

"Baby yanzu kin zama mallakina kad'an ya rage kawai ince ke din tawa ce ni kad'ai."

Murmushi tayi tace " ha'an kaji my barrister kuma,dama ai ni taka ce ba wai saura kad'an bane,amma me ma ya saka nishad'i haka ko duk murnan zuwa tambayan ne?"

Sai da ya cire goran swan da ya kafa a bakinsa sannan ya amsa ta "you wont believe abinda zan gaya miki".

Fad'awa tayi kan gadonsh kafin tace "try me."

Zama yayi kan kujeran office dinsa yana d'an jujjuyawa yace "babe nan da 2 months mun zama mata da miji babu wani shamak'i a tsakaninmu."

Zaune ta tashi tana zaro idanu tace "mene? Barrister kwata kwata yaushe muka had'u just a month fa,how comes?"

Cikin rikicewa yace" baby ban gane ba aren't happy ko har yanzu kina kokonto a kaina ne,ko kinfi so muyi dogon soyayya mu d'au lokaci mu k'arar da soyayyan a waje? Babe i assure you this is for the best duk wata soyayya muyi ta a gidanmu,ko baki gama gamsuwa da hallayena bane?" Ya tambayeta cikin rauni.

"No haba barrister kaima ka san da ban yarda da kai ba babu ta yanda za ayi in turaka gidanmu,Allah ya tabbatar mana da abinda shine alkhairi,i am so happy."

Kafin yayi magana taji mama na k'wala mata kira, da sauri ta kashe wayar tana amsawa d'an kwalinta ta zaro ta fita da sauri.

A d'aki ta sami maman da waya a hannunta ita da Ramlatu murna ne a kwance a fuskarsu tana ganin hakan ta san suma sun sami labarin kenan.

Zama tayi tana murmushi.
"Ke yanzu mamanki ke bani wani labari me dad'i" sunkuyar da kai tayi tana murmushi duka ramlatu ta kai mata tace "shegiyas har ya fesa miki kenan?"

Mama tace "madallah ai sai mu fara shiri gashi lokacin da suka d'eban kad'an."

Ramlatu kuma tace "bari mu gama girki in kirashi inji wani shagali za a had'a mana muji dad'in fidda anko (ni kam nace Allah yasa kar yawan kudinsu ya hanaki bacci kaman yanda na zeezee yake hanani)😰

Gadan gadan aka fara shirin biki inda mama ta fara gyara jikar tata a hankali Ramlatu ko tunda ya zayyana mata event d'in da za ayi suka fara yawon kasuwa ita da mariam dake shigowa zarian musamman dan ankon.

Watanta biyu a zaria ta fara shirin komawa Kaduna saboda papanta ya matsa ta dawo ganin lokacin biki na k'aratowa a halin da ake ciki biki saura sati uku da kwanaki.

Kamar had'in baki ranan Hassan ya dawo dan ya gama exams d'inshi dariya tayi da ganinsa tace"yaushe ka dawo?"
Yana k'okarin ciro kayanta a keke napep yace "ko awa banyi ba."
Tace "lahhh mun tafi a tare mun dawo a rana d'aya."

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now