YAY page 18

1K 133 6
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖








By Sawwama A.






Page 18.





Vote and follow me on wattpad @sawwama14.





Shiru tayi tana jiran amsan papa,sai da ya d'au lokaci me tsawo yace "toh yuhaanasu zamu duba magananki in me yuwuwa ne zan sami mahaifan yaron."

"Toh papa na gode Allah ya k'ara girma amin" daga haka tayi mishi sallama ta tafi dan yanzu babu wannan sakewan da suke yi da papa dan duk basa cikin sukuni.

D'akin ummi ta shiga inda ta sameta zaune bakin gadonta sauk'i ya samu sosai ummin na ganinta ta ja wani uban tsaki ta tashi ta shige bathroom.

Jugum tayi tana tunanin me tayiwa ummi haka hawayene ya gangaro mata bata san papa ya shigo ba sai jin hannayenshi tayi a fuskanta yana goge mata hawaye "ki k'ara hak'uri yuhaana _innallah ma'assabirin_ " gyad'a kai kawai tayi ta fita a d'akin dan kukan da yake shirin kubce mata.
Kan gado ta fad'a sai da tayi me isanta kafin ta tashi dan neman mafita wajen rabbi.

Zaune papa yake a cikin office d'insa ya had'e hannayensa waje guda yasa a k'asan haba.
Yau kwana uku kenan da wannan zance amma ya rasa wanda zai tunkara da maganan ko alhaji ya kasa gayawa.

Bai ji shigowan Elsaan ba yayi zurfi cikin tunani har sai da Elsaan d'in ya d'an buga table d'in

Firgit yayi ganin wanda yake gabanshi ya saka shi yin yak'e "ah ah haji elsaan yaushe a gari?"

Zama elsaan yayi a d'aya daga cikin kujerun cikin damuwa yace " jiya na shigo nan family house d'inmu shine nace bari in lek'o mu gaisa."

Wani yak'en papa yayi yace "lallai kuwa ka kyauta ya kuke? Ya umman taka? "

Numfashi ya sauke yace "lafiya lau alai mukhtar,ya ilayi?"
"Lafiya lau Elsaan naji dad'in ziyarar nan" cewar papa.

Shiru suka yi na wani d'an lokaci kafin Elsaan yace "ale mukhtar na ganka cikin damuwa ina fatan ba wani babban matsala bane?"

Numfashi papa yaja ya fitar daman neman wanda zai amayar masa da damuwarsa yake kuma ya san zai iya yarda da Elsaan.

A hankali ya warwarewa Elsaan labarinsa tun daga farko da halin da ya shiga a baya da wanda yake ciki a yanzu.

Sosai Elsaan ya shiga tashin hankali ya ji a duniya yana son taimakawa alhaji mukhtar wannan wani irin rayuwane me cike da rud'ani.

Shiru office d'in ya d'auka na wank lokaci kafin Elsaan yace.....




Sawwama Qawwama😘


I know is short buh I already promise u guys so I have to keep my word.

YA ABUN YAKE?Où les histoires vivent. Découvrez maintenant