YAY page 11.

1.4K 125 6
                                        

💖YA ABUN YAKE? 💖






By Sawwama A.





Page 11.





Vote and follow me on wattpad @sawwama14.



*This chapter is for you masu bibiyar labarai ne a duk inda kuke na gode ina alfahari daku I luv u xoxo💓* 



Da wannan tunani cike fal a zuciyanta bacci b'arawo ya saceta.
Zuwa safiya kuma d'okin zuwa zaria ya mantar da ita dan hak'ikanin gaskiya dangin mahaifiyarta na sonta suna ji da ita shi yasa wasu lokutan take jin dama ace sune dangin mahaifinta.

Tun goma Yuhaana ta gama shiri,shi kuma Hassan yace" nifa babu yanda za ayi ki sani inyi sammakon tafiya makaranta kaman ana korata."

Marairaicewa tayi tace "haba hassan haba dan Allah ba sai mu tsaya a gidansu mama ba zuwa yamma sai ka tafi." D'an tattare giransa yayi yana tura hannu a cikin aljuhu yace "toh bari di in gani yanzu ki bari inje shago in k'arasa wani d'inki sai in zo mu tafi."

"Hass.."
"Meye? Ba dai cewa zaki yi in barwa mutane aikinsu anjima ace teloli ba amana,ba a musu uzuri ko a gida ake hanasu daman aiwatar da abinda ya kamata." Yana magana yana wani zazzare mata ido sannin da yayi ba zata ce komi tunda lallabashi take.

Ilai ko ba tace komi ba sai ma sunkuyar da kai da tayi kaman shine babban itace k'arama sai kuma tausayinta ya kamashi.
Da sauri ya nufi hanya fita a d'akin yace"bari in yi sauri kar ki damu had'awa kawai zanyi." Gyad'a kai kawai tayi tana k'unshe dariyarta dama ta san abinda zata yi kawai kenan ta samu yanda take so,bayan papa in akwai wanda bai son b'acin ranta toh Hassan ne dan ko ummi ba wani nuna mata damuwarta take yi ba,duk da irin son da take mata amma tana barin abun a cikin zuciyarta.

Cigaba tayi da hidimominta dan tuni ta gama shiri Hassan ko bai shigo gidan nan ba sai azahar lokacin tana waya da ibrahim.

"Mine ka ganshi sai yanzu yake shigowa fa, jakarsa kawai zai d'auka mu tafi dan mun gama shiri." Hassan ne ya zauna kusa da ita yana hararar ta bai ji abinda Ibrahim din yace ba sai ji yayi yuhaana nacewa "ah ah ba wani rana wallahi.... No ba sai ka zo ba yanzu zamu wuce kawo." Alama yayi mata da ta barshi yazo ta girgiza kai tana harararsa .

"Mine ba fa haka bane ummi ma ba zata bari ... Haba kai kuwa kar muyi haka da kai mana don't be upset,toh babu wanda zan bari ya kalleni.... Ok nima hka" dariya tayi tace "Hassan na kusa fa" sannan ta kashe wayar..

Ta fuskanci Hassan dake ta faman banka mata harar"ni ban harareka ba kai zaka zo ka sani a gaba kana hararata a bisa wani dalili?" Ta wurga mishi tambaya

Gyara zamansa yayi a bakin gadonta yace "yanzu dan ciki black za a zo a kaimu ki hana ko tausayinmi ba kyaji zamu fita a tsakar ranan nan kin ki bari rana tayi sanyi sannan ance za a kaimu kin hana,mtsww wallahi halin mata sucks."
Hmmm kawai tayi bata ce mishi komi ba,shima ganin ba zata tanka ba yasa ya tashi ya shiga d'akin ummi dan karb'an yajinsa da sauran tarkacensa.

Tana nan zaune yaje ya shirya ya fito turus yayi ganinta a zaune ta tisa kayanta a gaba har da yafa gyale alamun shi kadai take jira,shi abin ma dariya ya bashi aiko sai da ya dara yace "ni dai bani son zaria wata ko in zata kaman wacce zata makkah haka take jinta bata ce mishi komi ba har ya shiga dakin momynsa ya fito itama mik'ewa tayi ta shiga dakin momyn da sallama.
Ciki ciki ta amsa sallaman had'e da kau da kai gefe.
"Momy ni zan wuce zaria sai an kwan biyu in dawo." Yuhaana tace murya a sanyaye.

"In kin ga dama ma.kar ki dawo da hakan ya faranta min rai fiye da tunaninki alak'ak'ai kawai" momy ta fad'a a harzuk'e da sauri yuhaana ta fita daga d'akin dama shi yasa bata shiga tare da Hassan ba dan bata so ya rabu da mahaifiyarsa cikin sabani dan ganin Hassan a wajen ba shi zai hana momy ci mata fuska ba shi kuma ba shiru zaiyi ba k'arshe kuma su haura kowa zuciyarsa ta b'aci.

YA ABUN YAKE?Donde viven las historias. Descúbrelo ahora