💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 3.
Follow and vote for me on wattpad @ _sawwama14_
Tamke fuskanta hajiya tayi had'e da kau da kai gefe "kulu ki kau da kai gefe amma bashi zai hanani gaya miki gaskiya ba kamar ko yaushe, ruwanki ne in kin d'auka ko kin zubar."
Numfasawa yayi had'e da dogara hannunsa jikin k'ofan da yake tsaye kafin ya cigaba da fad'in " ni na rasa aibin yarinyan nan da kuke gani me ta aikata muku haka? Kuma koma menene bana jin yarinyan nan ita ta muku laifi,ba laifinta bane zuwanta duniya ta hanyan da baku so ba dan meye bazaku rungumi k'addararku ba kaman ko wani musulmin k'warai? Ku godewa Allah da ya azurta ku da yarinya kaman Yuhaana,me nutsuwa,hankali,hak'uri da hangen nesa."
Tab'e baki hajiya tayi tana k'ara kau da kai gefe girgiza kai baba yayi kawai yace "Allah ya kyauta" kafin ya juya sawunshi har ya kusan fita daga gidan ya juyo kaman ya san tambayoyin dake kunshe fal a bakin Bilkisu yace" kulu kamar ko da yaushe ina k'ara jaddada miki dake da y'ay'anki da suka sani duk wanda ya fitar da maganan nan wanda har yayi sanadiyar da yarinyan nan taji yanda abin yake toh a bakin aurenki kuma ba zan tab'a yafewa kowaye ba matuk'ar ba shi mukhtar bane ya fad'i da bakinsa." Kallonshi tsohuwar take cike da takaici ganin hakan yasa ya kuma cewa " ko da kuwa ko bayan raina ne ban yafe ba.... Kuma ni nan da kike gani ina bayan me gaskiya ne ba wai ina bayan mukhtar ba." Sannan ke kuma ya juyo kan bilkisu "ki tattara ki koma gidan mijinki bakuntan ya isa haka tunda fitina kika zo tayarwa toh maza na baki kwana biyu ki kimta ki bar garin nan domin ita mace in ta wuce zama gidan ubanta to tabbas bata da inda yafi gidan mijin dan haka baki da waje a wannan gidan matsawar kina da aure,masu gidan uba.... shashan yarinya kawai"
Yasa kai ya fice ya barsu da cizon yatsa k'wafa hajiyar tayi ta mik'e ranta a cushe ta shige uwar d'akanta zuciyarta cike da k'in yuhaana.
Wunin wannan ranan Yuhaana bata samu kanta ba sai yamma lis domin tana gama gyaran store d'in ummi ta bata wani aikin haka ummi tayi ta saka ta aiki na ba gaira ba dalili taso ace ko aikanta tayi da sai tayi amfani da wannan daman ta aiwatar da uzurinta,amma Allah cikin ikonsa ko gate bata je ba wunin ranan.
Daren rana suna zaune duk a babban palon gidan suna cin abinci kaman ko yaushe dan haka papa ya tsara so dole hakan ake yi duk da zuciyoyin mutane da yawa basu son haka.
Baka jin k'aran komi sai cokala sai kuma muryan tv da yake tashi papa ne yace "au habibullah d'auko min ledar da ka shigar min d'aki." Da sauri yaron ya mik'e dan tunda yaji haka ya san ta samu kenan bare yaji ledan da d'an nauyi.
"Papa gashi nan" gefenshi papa ya nuna yace "yauwa ajiye shi a nan." Yaron ya ajiye papa bai k'ara bi ta kan ledan ba sai da aka gama cin abinci aka zauna kallo. Duk yaran gidan sun mai da hankalinsu ga tv yayin da yuhaana na can gefen palon tana chatting da mariam k'awarta ummi kam ta wuce d'akinta yayi da momy ta kafa ta tsare tana jiran jin meye a ledan.Can papa ya janyo ledan turarrurka ne a cikin ledan me yawa ware wasu guda uku yayi designers ne sauran kuma ya dinga kiran yaran gidan yana basu d'ai d'ai sai da ya gama basu kap sai tsallen murna suke kafin ya fito da wasu guda biyu iri d'aya flavor daban daban momy ya mik'awa d'aya tayi godiya ciki ciki dan idonta na kan guda uku da ya ajiye a gefe,ya bawa habibullah d'ayan yace ya kaiwa ummi. Sauran yaran gidan ma duk fita suka yi don su nunawa ummi palon ya rage daga yuhaana sai papa da momy da ta tsaya ganin gudun ruwar mijin nata.
"Yuhaan papa! Zo nan" tsam ta mik'e daman jmtuntuni jira take a iso kanta dan masoyiyar kamshi ce,tsugunawa tayi a gabanshi ya turo mata k'waya uku da ya ajiye a gefe yace "toh mamana ga alk'awarin mu" cikin tsananin murna ta kwashe tana shirin bud'e baki tayi magana taji ance "kutumar.... Alhaji wannan wani irin rashin adalcine ta yaya zaka d'auki turare masu tsada har uku ka baiwa wannan yarinya alhalin ka had'a yaran da me arha ko mu matan ka kwara d'ai d'ai ka bamu amma ita ka dauki har uku ka bata kuma masu tsada fiye da na mu?" Cikin b'acin rai yace "saboda y'ata ce kuma abin da nayi niyya shi zan bata."
Wani dariyar rainin hankali tayi tace "hehh y'a fa kam... To su sauran a bola aka samosu ko kuma yaran abokinka ne?" Basuji mik'ewarsa ba sai saukan mari da suka ji a fuskan momy
Dafe kuncinta tayi shi kuma ya nunata da d'an yatsa yace "salamatu ko da wasa! Ko da wasa kar ki kuskura k'ara kwatanta abin da kika yi yau idan ba so kike in tsinke igiyoyin aurena dake kanki ba." Rik'e hannunshi yuhaana tayi tace" papa ya isa haka please kayi hak'uri." Cikin kunan rai momy tace " rufa min baki munafuka kai kuma ka cigaba da gwada rashin adalci ka siyo mata turare har uku saboda matar so ta samu daman fesawa." Fuuuu ta wuce kaman kububuwa girgiza kai yayi ganin kuma inda ta koma.D'akinsu da k'ananan k'annenta mata ta nufa bayan ta gama bawa papansu baki. Tana shirin shiga wayarta ta hau ringing murmushi tayi ganin sahibarta ce.
"Babe sorry kinji ni shiru ban miki reply ba ko?"
Daga can b'angaren maraim ta amsa
Tace "ai ke iskancinki yawa gareshi, ko kunyi waya da sadam d'in ne ko kuwa?"Cike da damuwa tace "ina fah amma yanzu in mun gama magana zan k'ara gwadawa Allah dai yasa lafiya fiye da kwana uku banji daga gareshi ba"
Hummm mariam ta sauke numfashi tace "toh Allah dai ya jiyar damu alkhairi amin,in kun samu kunyi magana sai ki sanar dani" da haka suka yi sallama mariam na tausayin k'awarta dan ita ta san dalilin shirun sadam yaso ita ta isar mishi da sak'onshi ta nuna mishi bazata iya ba.
Yuhaana na ajiye wayan kiran sadam na shigowa gado ta hau tana doka murmushi cikin siririyar murya tayi mishi sallama a maimakon taji muryarsa cike da shauki kaman ko yaushe ah ah wannan karon sai ta jita a cunkushe.
Cikin tashin hankali tace "habibi me ya faru me ya sameka?"
Murya k'asa k'asa yace " sweetie i am sorry ba zan iya aurenki ba."
Blue eyes d'inta ta zaro tace "mene? Sadam me kake shirin fad'a min me na aikata maka haka da zaka min wannan mummunan hukunci?"
Rintse idanunsa yayi yana jin zafin duk kalman dake fito daga bakinta
"Yuhaana baki yi min komi ba... Amma iyayena sunce basu yarda ba basu amince ba in auri yarinyan da bata da ASALI ba da fari sun yarda amma daga baya sunce sun gane baki da asali saboda haka bbasu yarda ba."
Cak komi na sadarwanta ya tsaye da kyar ta k'ak'alo yawun bakinta tace "sadam wani irin magana ne wannan,baka gaya musu cewa a gaban iyayena ka ganni kake sona ba,baka gaya musu cewa kaga ummina da papana ba har da k'annena ba?" Ta fad'a cikin tsananin kuka.
Cikin rauni yace " ah ah yuhaana kema sanin kanki babu mutum d'aya da kika yi kama dashi a cikin gidanku wanda hakan nima ya tabbatar min wanda kike cewa iyayenki ne ba iyayenki bane,kuma manzon Allah (SAW) yace ku auri mace dan asalinta saboda haka yuhaana kiyi hak'uri na janye akan maganan aurenki ki gayawa papa iyayena baza su zo nema min auranki ba" daga haka ya datse kiran ya barta da waya a hannu.
Ta kai tsawon minti biyar a haka kafin ta juya a 360 tayi d'akin ummi cikin kuka tace " ummi ki yiwa Allah ki gaya min inane asalina" wani irin bugawa zuciyar ta tayi ta d'ago tana dubanta cike da tsoro.
"Ummi su waye iyayena? Su waye suka haifeni? Me yasa kuke b'oya min asalina? Wai kam ya abun yake ne?"
D'au ummi ta d'auke da mari.Sawwama Qawwama😘
