💖YA ABIN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 22.
Vote and follow me in wattpad @sawwama14.
*kuyi hakuri last page da wannan are full of errors bana jin dadi ne pls bear with me*
Tace"mukhtar kafi kowa sanin ba zan iya auran wani ba,zuciyata da gangan jikina ba zata amince min ba na sha gwada hakan amma abun ya faskara ina ga ni kam haka zan mutu ba aure matukar ba samun *abinda raina ke so* nayi ba which ni da kai mun sani ba samu zan yi ba ko mukhtar? K'ila sai dai wani ikon Allah ko wani babban rabo which i doubt hakan zai tab'a faruwa"
Gum papa yayi dan bashi da abin fad'a mama ce tayi karfin halin cewa "ubangijin Allah ya yaye miki yasmen,amma ba laifinki bane laifin mahaifin naki ne da ya zuba miki ido kike zaune mishi a gida ba a aure shi ya sa sam ban goyi bayan komawanki hannunsa ba."
Mik'ewa yasmen tayi ta shige uwar d'akin mama dan bata son ma a tsawaita maganan su sun kasa ganewa cewan zuciyanta ya ginu akan son mutum d'aya ne wanda yayi mata nisa he is out of her reach thanks to her cousin sister Hajara.
Sallama papa yayiwa mama ya tafi amma kafin ya tafi sai da ya nemi Ramla ya rok'i alfarman ta k'ara kwantarwa da yuhaana hankali in tazo ramlatun ta tabbatar mishi zata yi iya bakin k'okarinta.
Daga Zaria gidan su mariam k'awar yuhaana ya nufa nan ma d'an tak'aitatan bayani yayiwa iyayenta kafin aka turo mishi mariam d'in.
Yuhaana na kwance a d'aki tun bayan tafiyan yasmen a safiyar ranan,tsoron zuwa ga umminta take sannan kuma so take taje gareta she misses her.
Me yasa ummi tace "ita burden ce a gareta,me yasa ta gaji da ita anya ummi mahaifiyarta ce kuwa,dama can tana danne soyayyarta a zuciyarta ne tunda yanzu kumq ciwonta ya sa ta fitar da abinda ke ranta? Ya abun yake ne? Ita kanta ya d'aure me yasa rayuwarta yake cike da rud'anine a gaskiya itama zata nemi black eye contact ta dinga sawa ko hakan zai rage mata wasu kallon da ake mata ko ita take yiwa kanta domin ita kanta ta fara kokonton asalinta.
Anya anya kuwa anya ba adopting dinta aka yi ba? Toh ko ita d'in d'iyar papa ce zallah ba ummi ba ummi rik'eta kawai take yi wata k'ila shi yasa momy da sauran dangin papa suka tsaneta wata k'ila ba ta hanya me kyau aka sameta ba.
Kai ba don aunty yamen ta rantse ba ita ta haifeta ba da babu abinda zai hanata yarda cewan papa da yasmen sune iyayenta.
Toh soyayyar da su mama ke mata fah? Menene matsayinta a wajensu? Dafe kanta tayi dan yanda take ji kaman zai tarwatse kullum k'ara shiga duhu take duk ta hanyan da ta biyo danbta gane yanda abunke sai ta samu babj ma b'illa ma'ana duk tunaninta bata fita a duhu sai dai ma ta k'ara dulmayawa cikin wani bak'in duhun things a getting more and more complicated.
Rik'e kanta tayi tana jujjuyawa wa zai fitar da ita wa zai fahimtar da ita yanda abin yake?
Jijjigata mariam tayi sosai tana kiran sunanta a firgice ta sauke hannunta tana kallon mariam da mamakin yaushe tazo itama mariam d'in kallonta take yi cike da tausayi.
Da k'yar ta tattaro yawun bakinta murya a dashe tace "mariam yaushe kika shigo?"
Zama mariam tayi a gefenta bisa kan gadon ta dafa kafad'anta tace "lokacin da kika yi zurfi cikin tunani har kina neman zaucewa ki fita a hankalinki,anya yuhaana kina yiwa kanki adalci kenan so kike wata cuta ta kama miki da k'ananan shekarunki? Cuta fah ba mutuwa bane Allahn da ya d'aurawa ummi cutan nan shi zai yaye mata ku dawo kaman da. Me yasa kike abu kaman mara ilimi ne ki gwadawa Allah jinyan ummin ma ba baj tsawaita ba kuma dama shi sauki a hankali yake samuwa ciwo ne ke shiga farar daya haba yuhaana ki zama me tawakkali mana."