YAY page 5.

1.4K 134 17
                                        

💖YA ABUN YAKE? 💖




By Sawwama A.






Page 5.






Vote and follow me on wattpad @sawwama14






Mai napep d'in na tsayuwa ta fita bashi kud'inshi jikinta na rawa ko tsayawa karb'an canji bata yi ba ta shige gidan.

Cikin sa'a bata samu kowa a tsakar gidan ba hakan ya bata daman kutsawa ciki d'akinsu zama tayi a bakin gadon jikinta sai karkarwa yake ga wani tsoro da yake ratsata.

Tsintar kanta tayi da fashewa da wani irin kuka yarfa hannunta take yi tana fad'in" innalillahi wa inna illaihi raju'un wayyo Allahna" da kyar cikin wani irin dauriya ta janyo papers d'in guda biyu da yake d'auke da k'addaranta.

Har a wannan lokacin hawaye bai bar sintiri a kan fuskarta ba haka nan jikinta ya jike jagab da gumi rintse idanunta tayi tana ware paper d'in dake kunshe da DNA test da taje tayi dan tabbatar da papa da ummi da papa mahaifanta ne na gaskiya ko aka sin haka.

A hankali a hankali take bud'e idonta har tayi nasaran bud'e idanun tarara a bisa takardar ky'afk'yafta idanunta tayi da sauri ta janyen wannan domin duba d'ayan.

Sakinsu tayi ta damk'e bakinta da hannu biyu wasu dunk'ulalun hawayene ke zubo mata masu sanyin gaske tashi d'aya taji jikinta kaman wacce aka zuba mata ruwar k'ank'ara.

Dariya take yi da kuka a lokaci guda ta rasa a wani irin yanayi take tsantsan farin ciki shi yake d'awainiya da ita da ita tsam ta mik'e ta fuskanci gabas ta d'ora goshinta a k'asa domin nunawa ubangiji godiyarta.

D'aukan result d'in tayi ta k'ara duba inda aka tabbatar mata da DNA dinta dasu ya matching tayi tsintar kanta da daddanawa wajen da aka rubuta POSITIVE kiss tayi tsaban farin ciki

Nannad'ewa tayi taje ta bud'e drawern kayanta tayi musu kyakyawan b'oyi.

Alawla ta d'ora tazo ta d'au al-qurani cike da farin ciki take rera karatunta k'asa k'asa har sai da taji an kira sallar magrib ta mik'e ta gabatar da nata sallahn sannan ta fito tsakar gidan ummi ta gani tana yiwa su muhsina fad'an suje suyi sallah.

"Sannu da gida ummi" ta gaishe da ummin harara ummi ta watsa mata tace "sai yanzu kika ga daman ki sanar da dawowanki.

Zuwa tayi ta rungume mahaifiyarta cikin tsantsan farin ciki tace " ummi am so sorry ba zan k'ara ba." Da mamaki ummin ke kallonta peck ta manna mata tace " ummi i love you,you're the best mother in the world." Ta kuma maida kanta jikin ummi.

Tsaye ummi tayi kaman mutum mutumi kafin tace zata bud'e baki tayi magana muryar papa tayi sallama.

Da sauri ta saki ummi ta nufi k'ofar gidan da papa yake shigowa shiga jikinsa tayi tace "papah welcome" zagaye hannunsa yayi a jikinta yace "thank you yuhaan papa wannan murnan fa? Whats the occasion?"
Dariya ta saki tace "babu komi papa just happy and feeling happy to have you as a father ina sonka papa." Rik'e kanta yayi idonsa cike da k'walla yace " nima ina sonki yuhaanasu we are also proud to call you our daughter Allah ya albarkaci rayuwanki da na sauran y'an uwanki amin."

Uhm uhm akayi gyaran murya daga bayan papa sannan aka fara magana"aiyo dama kalan soyayyar da ake yi kenan in bana gidan nan shi yasa aka turani wata duniyar"

Lek'awa tayi ai ihu ta saka ta saki papa ta nufi d'an uwanta ta cakumo shi girgiza kai papa da umni suka yi suka wuce babban palon gidan inda momy ke can tana cika wai ranan girki papa yaje ya tsaya da ummi da diyarta.

"Alhassanul basariy saukan yaushe" ta tambaye shi suna shiga gidan b'ata rai yayi yace "malama zamu b'ata fa bani son rashin d'a'a" zungure kanshi tayi tace "k'aniyanka wa ke yi maka rashin d'a'a kaji min yaro da rashin kunya bar ganin kayi gansameme i am still the  eldest."

Kwalarsa ya gyara yayi doro yace "yarinya dan kin ban shekara d'aya kawai? Ko kinki kin so nine babba nine fa babban d'a namiji." Tsaki taja ta wuce shi ta shiga palon dan dama sai dai basu had'u ba sai sunyi fada akan girma.

HASSAN kenan babban d'an momy tsakaninsa da yuhaana shekara d'aya ne tare suka gama makarantar secondary ko da suka zana jamb shi yaci yuhaana bata samu admission ba  tana kan nema yanzu haka yana shekararsa ta biyu a BUK ta jahar kano duk yanda momy taso y'ay'anta suk'i ummi da yuhaana hakan ya gagara saboda ummi me kyakyawan zuciya ce kuma papa yayi tsayin daka akan tarbiyan gidansa.

Daren ranan ummi ta samu bacci isashe me rahama ganin finally ta shawo kan matsalan yuhaana.
Yuhaana baza ta tab'a sanin ya abun yake ba matuk'ar ba lokaci ne yayi wata k'ila kuma har abada.



_wai masu karatu ya abun yake ne? Shin kun gamsu papa da ummi sune mahaifanta ko kuwa ya abun yake?_






Sawwama Qawwama😘

YA ABUN YAKE?Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang