💖YA ABUN YAKE?💖
By Sawwama A.
Page 2.
Follow and vote for me on wattpad @sawwama14
Washegarin ranan d'aukacin zuriyar gidan ke zaune a babban palon gidan suna breakfast har da aunty bilki k'anwar papa da ta zo.
Tsilip yuhaana ta mik'e papa ne ya d'aga ido ya kalleta yace " yuhaa ba dai wai har kin koshi ba?" Girgiza kai tayi ta had'e hannuta biyu a baya tace "papa abu zan d'akko a kitchen na manta nayi mana source na shredered beef ne shine zan je in d'akko."Gyad'a mata kai kawai yayi ya cigaba da cin abincinsa kasa kasa momy da aunty bilki ke wurga mata harara har taje ta dakko ta dawo papa ta fara zubawa sannan ummi, plate d'in aunty bilki ta nufa cikin wani irin sauri ta janye wanda hakan yayi sanadiyar zubewar miyan a k'asan carpet cikin b'acin rai papa yace "bilkisu yaya haka? Me zai sa ki janye kwanonki tana k'ok'arin zuba miki abu?"
Turo baki tayi tace "nifa yaya wannan yarinya baka san yanda bani son wani abu ya had'ani da ita bane,kwata kwata ban...." Wani tsawa ya daka mata wanda sai da kowa a wajen ya tsorata "dakata haka nan bilkisu ni zaki kalli k'wayar idona kice ba kya son y'ata lallai yau na kara tabbatar da baki sona dan duk wanda zai k'yamaci jininka ba,kuma tunda har baki son ganinta ki tattara ki kama hanyanki ki tafi naki gidan uban ko gidan mijinki dan nan gidan uban Yuhaana ne."
Ya mik'e cikin k'unan rai ya tallafo yuhaana dake zube jikin ummi tana hawaye tun sa'ilin da aunty bilki ta fara magana duk da inda sabo ta saba da irin wannan wulakancin sai dai basa tab'a yi mata a gaban papa hatta momy da take gidan bata mata tijara gaban papa sai in baya nan amma yau a gabansa. D'akinsa ya nufa da ita yana lallashunta har da yi mata alqawarin turare.
Aunty bilki kam kukan takaicin yayanta da y'arsa ne ya sark'eta haurawa tayi ta tsallake ummi kaman zata takata ta wuce d'akin momy baki momy ta tab'e tace "Hajara dai anyi asara na son raba yan uwa toh wallahi burinki ba zai tab'a cika ba uffan ummi bata ce mata ganin yara a wajen ko da yake ko babu yara ummi ba tanka mata take yi ba.
"Aunty jameela wai ni yau yaya ke kora a gidansa saboda wancan abar? Ni yaya yake cewa in bar mishi gida intafi gidan nawa uban? Toh yau ba gobe ba yanzu ba anjima ba zan tafi gidan ubana Alhamdulillahi Allah ya horewa ubanmu gida yau da nayi kukan bak'in cikin da yafi wannan."
Dafata momy tayi tace " amma bilki ke sakarai ce wannan yarinya ne zata yi sanadin da zaki bar gidan dan uwanki? Har yaya muktari ya haifi y'ar ko d'an da zai rabashi da y'an uwanshi ai wallahi ba a haifeta ba."
"Ah ah wallahi aunty jameela gwara in kama kaina tun yaya bai min rashin mutuncin da yafi wannan ba kan wancan kod'add'yar yar tasa da matarsa ni na rasa me yasa yake son yarinyan nan fiye da kowa a yaransa,ko dan ya ga duk tafi sauran yaran kyau ne yake tunanin zai samu arziki da ita oho. Aunty jamila *ya abun yake ne?*"
Murmushi momy tayi tace "toh ke in kin rasa dalilin da yasa yake sonta... Me yasa ke kika tsaneta? Watsa hannayebta tayi tace "haka nan na taso bisa tsananta ganin yanda kowa ya tsaneta ita da uwarta" ta cigaba da had'a kayanta da na d'anta ba tare da jiran komi ba ta kama hanyan gidansu.Rarrashinta papa yayi sosai ya bata hak'uri battroom ya shiga dan ya watsa ruwa,hakan ya bata daman tashi da sauri ta nufi gaban mirror dinshi hair brush d'inshi ta ta d'auka cikin ta fara bubbud'ewa cikin sa'a kuwa ta samu k'ananan gashinsa zazzara tayi ta damk'e a hannunta da sauri tayi hanyan fita karo suka ci da ummi sanadiyar hakan zuciyanta ya buga da k'arfi tana fatan Allah yasa bata ganta ba.
Ganin bata nuna alamun ta ganta bane yasa ta rab'a ta gefen ummin ta wuce ido ummi ta bita dashi sannan ta girgiza kai ta k'arasa cikin d'akin.
D'akinsu ta wuce direct zuciyarta na bugawa tana tsoron kar abinda zata tono wani hanky d'inta ta samu ta adana k'wayoyin gashin papa da ta samo sannan ta cusa cikin handbag d'inta ajiyan zuciya ta sauke a fili tace zaura na ummi.
D'akin ummim ta nufa drawer d'in kayan kitson ummin ta nufa ta janyo d'an tsaki taja ganin ta duba duk jikin combs d'in ummin babu alamun gashi dama ta san za a rina kasancewar ummin me tsafta ce sosai ta tura drawer d'in kenan ummin ta fito daga toilet firgita tayi sosai da ganin ummin.
Kallon tuhuma ummin tayi mata tace"ke kuma fa? Lafiyarki?"
"Emm emm ummi dama zuwa nayi in miki oiling kanki? Ta tsinci kanta da fad'ar haka? Ido ummi ta zuba mata can tace " yuhaana kaina yayi datti ba sai an oiling ba wankewa zanyi in na tsefe." Janyo drawer d'in ta kuma yi ta d'akko comb da kibiya dan ta riga ta kudurtawa ranta sai ta wanke kokonton dake cikin zuciyanta.
"Ummi toh bari in tsefe miki" ta nufi inda ummin ke zaune ta zame mata d'ankwalin kanta kwata kwata ummi bata yi yunkurin hanata ba zama tayi ta tsefewa ummin kai har da taje mata sannan ta mik'e hannunta rik'e da gashin da ta cire a jikin comb d'in
"Ina zaki kai min gashi kuma?" Cewar ummi gabanta ne ya bada damm abinka ga mara gaskiya.Cikin ina ina tace"amm zan je in yar ne?" D'an tattare giranta ummi tayi tace " ki yar kuma? Kema ai kin san bana yar da gashi sai dai in k'ona"
"Toh toh ummi bari inje in k'ona" gyad'a mata kai ummi tayi kawai ta fice rolling idanunta tayi bayan ta fita sai da taje ta addana shi cikin hanki sannan ta sauke ajiyan zuciya "phewwww that was so close" tace shiryawa tayi da nufin taje ta aiwatar da kudurinta sannan ta fito ta nufi d'akin ummi."Ummi zani gidansu mariam wai zan rakata kasuwa" ba tare da ummin ta kalleta ba tace "ah ah yuhaana bani son d'an banzan yawo baki tashi fad'a min zaki fita ba sai da kika shirya ga me zaman kanta ko? Toh gwara ma kije ki canza kaya dan yau bani son in ga ko k'wayan datti a store din gidan nan so da yawa ina gaya miki in zaki d'iba abu ki dinga d'iba with care amma ah ah sai an zubar maza kije ki kintsa manashi."
Ba tare da ta amsa ummin ba ta juya cikin takaici dan ta katse mata hanzarinta kuma tunda tace ba zata fita ko tana yaya ba zata barta ta fita ba store d'in ma ai momy ke b'atawa haka ba dan ta so ba ta sauya kayanta ta tafi gyara store d'in ta barwa gobe kudurinta dan sanin ya abun yake.
Tana shiga cikin gidsn ta fashe da kuka had'e da fad'awa jikin hajiyarsu kamata hajiyar tayi tace " ah ah auta ke kuma fa? Ke da wa? Me yayan naku ya miki ko ke da matansa ne?"
"Hajiya! Hajiya!! Wai ni yau yaya muktar zai kora a gidansa?" Dafe k'irji hajiya tayi tace " na shiga uku ji fad'imatu a wani dalilin k'alu innalillahi" hancinta bilki ta ja tana kunce goyan adnan tace " hmmm hajiya baki ji me ma yace min ba wai in tarkata in tafi gidan ubana nan gidan uban yuhaana ba gidan ubana ba dan haka ba zan zo in takura masa 'ya ba."
"Hakk'un yayi gaskiya zancensa ba wai kuma ina tare dashi har kullum."
A tare suka juyo dan ganin me maganan nan duk da sun san muryan waye kai ko basu san muryan ba sun sani kap dangin mutum d'ayane zai yi wannan furucin......
Sawwama Qawwama😘
