💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 17
Vote and follow me on wattpad @ sawwama14.
*slm dearies na dawo and inshaa Allah zan na posting kullum. Luv u lot loads*
Wasa farin girki duk yanda me karatu zai alakanta ciwon ummi ya wuce tunanin mutum
Cikin kwanaki uku kacal ummi ta dawo wani iri abin tausayi ta fige ta lalace bata iya cin komi sai ruwa haka yanda taga rana haka take ganin dare duk tayi figai2.
Anyi yawon hospitals da ita har dawanau na kano amma babu wani labari babu wani abu da ya nuna kwakwalwarta akwai matasala kuma ko anyi mata allurar bacci bata samu tayi haka idanunta za suyi luhu luhu amma ba zata iya yin baccin ba sai dai ta wahala.
Nan da nan labari ya bazu ummi ta haukace dangin papa da basu sonta masu murna nayi ana Allah shi kara yanzu haka wani mugun abun nata taje yi ya dawo kanta.
Amma fah duk wanda ya zo ya ganta sai ya tausaya mata.
Kuma har wa yau bata yarda da papa ko yuhaana har gwara papa da alhaji ya fara kawo mata ruwan zam2 da yayi addu'o'i a ciki ta daina ihu in papa yazo kusa da ita yuhaana ce dai bata isa ta zo kusa da ita ba.
Papa shi kad'ai ke hidima da ita ba yanda su mama basu yi ya mayar da ita gida ba yak'i.Gani yake duk wanda yake da hannu a cikin al'amarinta do yake ya rabasu shi kuma ba zai ba da wannan daman ba.
Yuhaana ta fige ta fice hayyacinta bata da aiki sai kuka so take taje kusa da umminta ba hali ko ruwa in zata sha in yuhaana ce ta kawo ba zata sha ba.
Haka aka kwashe sati ana fama.
Tunda abun ya faru sai yau ne ibrahim zai samu ganinta bayan zuwa da yayi gaishe da ummi.
Ba laifi ta d'an gyara jikinta amma fa kam rama ya fito sosai.
A dakin su Hassan taje ta sameshi yana baza k'amshi.
Rakub'ewa tayi can gefe kaman wata bakuwa. Shiru suka yi bayan sun gaisa.
"Yuhaana!" Ya kira sunanta a nitse ganin tana shirin fad'awa cikin tunani.
Nasiha yayi mata sosai yana k'ara bata hakuri ya nuna mata cewan wannan ba komi bane illah jarabawa ya dade yana mata nasiha me ratsa jiki babu abinda tace banda idanunta dake tsiyayar da hawaye.
Tissue ya bata ta goge fuskanta murya a dashe tace "barrister kayi min alfarma d'aya."
Idanu ya zuba mata yana tsoron amsa mata dan bai san da me ta zo ba."Ina so a d'aga bikin nan zuwa ummi ta samu sauki ta yaya za ace nan da sati 2 zan yi aure mahaifiyata bata cikin hayyacinta?" Ta fada wasu sabbin hawayen na zubo mata.
Shiru yayi ya k'ura mata ido a ranshi fad'i yake wani irin a d'aga biki zuwa ummi taji sauki an san ranan da zata ji saukin ne shi ciwon hauka an san ranan warkewarsa ne gaskiya ba zai yuwu ba.
"Sweetie am sorry i can't" a firgice ta d'ago tana kallonshi gyad'a mata kayi yayi yace " da gaske ba zan iya ba yuhaana i need you."
Cike da mamaki tace "haba barrister wani irin magana ne haka ummi needs me more than you do?"
Kallonta yayi sosai kafin yace " i am sorry to say this but she doesn't need you,she makes it obvious matan da ko kusa dake bata bari kije."
Cikin jin zafin magananshi tace "this same woman u re talking about is my biological mother and no matter what she needs me lalura ce ta sameta."
Wani murmushi kawai yayi yace "well sorry ba za a canza ranan aure ba
Takaici ne ya hanata magana sai hawaye da ya cika mata ido mik'ewa kawai tayi ta fice ba tare da tayi mishi sallama ba.
Lumshe ido yayi ya na ayyana ya san za a samu matsala,kawai dai ya lura yuhaana na neman hanya ne kawai.
She is giving him attitude amma ko ya za ayi ba zai bari a d'aga bikin ba.Yuhaana ko ta k'udurta zata sami papa a d'aga biki.
Gangarowa yake daga steps da sauri sauri turus yayi ganinta da ummansa suna hira suna ky'alk'yala dariya.
Alamu suka ji ana kallonsu suka jiyo a tare yaro zo kaji abinda wani fulani yayi wa k'awar Rafila.
D'an tattare giransa yayi so her first name is rafila.
"Yaro kaji min fa fulani me ruwa ne ya kaiwa kawartata ruwa sai ta bud'e mishi kofan baya ya tace ya zuba mata a randan toilet saboda tana laulayi sai ta koma ta kwanta a palo da fulani ya gama zuba ruwa a randa sai tace mishi ya zuba mata a farin bokiti, bafillatani sai zubawa yake can dai yace "hajiya bokitin fa yaki cika" tsam ta mike dab zuciyarta ya gama bata a toilet yake zubawa illai ko a nan ya zuba. Yaro kaji min aikin fulani fa"(me ruwa da matar yayana suka sha draman nan😁)
Murmushi yayi kawai dan ya san miss Adams just cracked the joke dan ta dai matsayi a wajen ummanshi.
Sumba ya mannawa umman a goshi yace "umma zan wuce office is getting late"
"Ah ah yaro ka tsaya kaci breakfast ga sinasir Rafila ta kawo mana." Kallonta yayi ta k'asan ido yace "umma kar ki damu zan sha coffee a office miss Adam d'in ma i guess ya kamata ta shiga wajen aiki by this time ya fad'a yana d'aukan brief case d'inshi."
Ta gefen ido yaga tana yiwa ummanshi magana ya san maganansa ne sai ji yayi umma tace "au yaro tsaya ka d'auki Rafilan tunda waje d'aya zaku."
Kallonsu yayi daya bayan daya kafin yayi magana Rafila tace "driver ne ya saukeni." Gyada kai yayi yace "umma na tafi" ya fara tafiya.
"Yaro!" Umma ta k'wala mishi kira cak ya tsaya kafin ya juyo a tsanake
Murmushi tayi tace "Allah yayi maka albarka ka dai samu lokacI kaje kaduna.""Amin umma inshaaAllah i promise u wannan weekend d'in zani" daga haka ya sa kaibya fice Rafila na bayanshi.
Yana fita Haruna PA d'inshi ya amshi brief case d'inshi sannan ya bud'e mishi mota ya shiga har aRafila ta shiga gaba yace ta dawo baya zasu yi magana jikinta na rawa ta dawo bayan.
Sai da suka d'au hanya sosai har ta cire ran zai mata magana kafin yace miss Adam daga yau i dont want u coming to my house balle kiyi tunanin bribing mom d'ina da dishes d'inki na nuna miki alamu tun da naga take takenki i dont like u,why cant u get it har sai kin sa na furta miki bani sonki salon ki ga na mikk wulakanci?" Ta sunkuyar da kanta wani kunya na lullub'eta.
Jikinshi ne yayi sanyi yace "am sorry miss adam i dont mean to be harsh kawai dai bana so inzo in hurting dinki ne tunda ba sonki nake ba u cant cope da halayyana,dole mace me hakuri ne zata iya zama dani,tell u what daga yau na mayar dake kawata kanwata tunda kin my lil sis is abroad sai ki dau matsayinta."
Murmushi tayi mishi idanunta cike da k'walla tace "thank you" kai ya gyad'a mata ya mai da kanshi jikin sit ya limshe ido is the least he can do for her.
Yinin yau anyi shi cikin farin ciki kasancewar ummi taci abinci kad'an har ma ta bud'e baki tayi magana duk da cewan ba a ji me ta fad'a ba.
Sannan ta daina ife ife da gudun mutane sosai magunguna musuluncin da ake karbar mata yake aiki sai dai wani tashin hankali da yuhaana ta kara shiga shine da zarar ta kusanci ummin zata janye jiki tana zabga mata harara wasu lokutan har da tsaki ta juyar da kai.
Wanna ya kuma sa yuhaana jin lallai fa sai an d'aga biki dan ta sasanta da mahaifiyarta wannan dalili yasa ta nufi papa da batun.
Shiru papa yayi yana tunanin amsan da zai bata saboda da yamman nan wan mahaifin yaron yaxo ya sameshi.
A wannan yanayin da ake ciki bai san wa zai fara tunkara da batun nan ba yuhaana had enough ba zai iya breaking mata labarin nan ba cikin wannan tashin hankali da ake ciki.
Yau ta kasance mishi ranan farin ciki haka kuma ranan bakin ciki wacce zai gayawa maganan ta taya shi bakin ciki bata gama sanin inda kanta yake ba.
Babu wanda zai gayawa maganan nan ya fahimce shi sai wanda ya san yanda abin yake.
Toh wai ya abin yake?🤔
Sawwama Qawwama😘
