💖YA ABUN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 6.
Vote and follow me on wattapad @sawwama14
Yuhaana ta saki ranta fiye da tunanin me karatu ta riga da ta yarda Allah na halittan bawansa a yanda ya so,ta watsar da duk wani tunani da ya dad'e yana yawo mata a kwanya tun bata san kanta ba.
Sannan duk wani k'i da dangin mahaifinta ke yi mata ya daina damunta tafi alk'anta hakan da suna taya momy kishi ne da ta kasance y'ar uwarsu shi yasa suka tsaneta ita da momy,shi yasa yanzu suma ta watsar da al'amarinsu duk da abin na damunta dan da UBA ake ado dangin uba sune danginka.
Zaune take a tsakar d'akin tana tattare takardunta na islamiya da ta gama dubawa dan yau suka yi hutu shi yasa ta zauna ta ware wanda zata tafi dashi zaria dan soyayyar ganin tsohuwar kakarta ne ya motsa.
A firgice ta d'ago jin mutum ya d'aga labulen d'akin nasu a hankali sanin ita kad'aice a gidan duk mutanen gidan suna gidan mama rabi yar mahaifiyarsu inda take aurar da y'arta ta uku.
Dak'uwa ta sakar mishi tace "ubangiji Allah ya yafe maka Hassan,shiga waje ba sallama sannan cikin sand'a... Wallahi babu kyau tsoratar da musulmi." Dariya ya kece da sannan yace "dallah can matsoraciyar kawai ace wai mutum tun shigowana baki ji motsi ba."
Harara ta sakar mishi had'e da mik'ewa tsaye taje ta d'ora jakar islamiyarta bisa drawer kayanta "naji,me ya dawo da kai gidan nan ina ce shirin tafiya dinner ake yi yanzu?" Jingina yayi jikin k'ofar d'akin yayi tsaki yace "duk ba ke bace da fi'ilinki na k'in zuwa gidan bikin,papa ne yace inzo ince ki shirya in d'auke ki in kaiki wajen ga nan anko ya saya miki a wajen aunty murja dan d'aurewa biki gindi wai har da dinkekken anko ake sayarwa ga wanda bai samu yayi ba."
Rolling idanunta tayi tace "seriously? Ohhhh me yasa papa zai min haka ne nifa wallahi ba son shiga cikin mutanen nan nake ba,shi yasa gwara inyi zamana a gida."
"Hell no! Papa yace k'afana k'afarki baki ga har motarsa ya bani ba dan in d'akko ki oya ungo ki shirya yanzu mu tafi." Ya wurga mata ledan kayan" turo baki tayi ta marairaice,rufe idonshi yayi ya kau da kanshi yace " ki daina wani kallona da cat eyes dinkin nan you're westing time gwara kije ki shirya mu wuce" yasa kai ya fice.
Haka nan ba yanda ta iya dole ta tashi ta saka kayan jin dad'inta d'aya light blue ne ankon sai pitch head powder kawai ta saka sannan ta saka nude lipstick sannan ta saka kwalli ta fito.
A mota ta sami Hassan yana jin kid'a ya tokare hula a goshi ga k'asumbar nan ta kwanta a fuskarshi kai kace wani babbane shiga motar tayi ta zungure kanshi tace "shegen kaya y'ammata suna cin uwasu da k'arya ka ajiye wani uban gemu kaman wani babba."
A kaikaice ya kalleta yana yiwa motan key yace "wallahi yuhaa ki fita idona ke kin san yanda yammata ke folawa suna dayawa saboda ni kuwa? Yarinya shigo BUK kiga yanda nake jan babes" yana magana yana wani shafa gemunshi galala ta saki baki tana kallonshi sai ji tayi yace " yah? Ki shigar dani wajen k'warkin nan mana mariam."
"Kut... Hassan k'aniyarka k'awata zan yi maka hanya? A matsayin yayarka fa take?" Tsaki yaja yace "toh sai me ba dai kuna zaune baku samu admission ba ina gama service zan faso sai dai bata ganni da y'ar motata ba." Tsabar takaici ma rasa me zata ce mishi tayi wayarta ta d'auka tana dannawa.
Da isansu wajen har an fara kasancewan ba a so ayi dare a wajen,gabanta ne ya fara fad'uwa sanin da tayi in bata yi da gaske ba sai an tozartata a wajen.
Kallon k'ofar wajen take cike da al'ajabi ganin hakan da Hassan yayi yasa ya damk'o hannunta ya d'an murza, juye da kanta tayi tana fuskantar sa gyad'a mata kai yayi yace "everything is gon be ok i won't let anyone hurt you" mai da k'wallan da ya cika mata ido tayi tana murmushi itama ta gyad'a mishi kai kafin ta zare hannunta a cikin nashi ta bud'e murfin motan,shima a nashi b'angaren bud'e motar yayi ya fito suka jera kai kace wasu couple ne kasancewan yafi ta tsayi sosai,ba za ma ka tab'a cewa sun had'a wani abu na jini ba saboda banbancinsu.
Wani ikon Allah suna shiga wajen hankalin kowa ya dawo kansu sai jin tashin "wow" "kai" "mashaaAllah" "ya subhanah ji wata me kyau" abinda yagi sanidiyar tunzurar da amaryar akan me on her day mutane zasu dinga yabon kyan yuhaana ba ita ba yafito k'anwarta tayi tayi mata magana a kunne murmushi suka sakarwa juna.
A d'add'are Hassan ya sama mata waje ta zauna kafin ya tashi yin wani sabgarsa.
Tun shigowarsu idonshi ke kanta hakika ta tafi da duk wani tunaninsa bai tab'a cin karo da mace irin ta ba a k'asar Hausa sai dai da alama tana da abubuwan aro a tattare da ita duk da kasancewarta fara kuma me kyau,abubuwan aron da ta mallaka yasa yake fatan Allah yasa farin fatar bana aro bane shima duba da yanda ta tuntume gashin da yake zaton ta k'ara domin a cuci maza da k'wayar idon da yake tunani eye lence ne kawai ta saka dan ado amma ba wai halittanta ba sannan yanda shape d'inta ya tafi kana kallo ka san wannan sakawa akayi ba wai nata bane tsaban tsaruwarsa amma duk da wannan aibin da yake tunani tana dashi bai hana muguwar soyayyarta kamashi ba.
_Toh masu karatu kunji fah... Wannan bawan Allahn yana zaton tauraruwar taku kayan aro gareta,sannan me amarya da kanwarta suka shiryawa tauraruwar taku?_
Sawwama Qawwama😘
