YAY page 21.

1.2K 134 9
                                    

💖YA ABUN YAKE? 💖






By Sawwama A.






Page 21.





Vote and follow me on wattpad @sawwama14.




Kallonta tayi cike da rashin yadda...gyad'a mata kai yasmen tayi tace "ki yadda dani yuhaana ina sonki,soyayyarki a cikin ruhina yake saboda wani babban dalili amma bani ce nahaifiyarki ba?"

Cike da rashin yarda yuhaana tace ",toh me yasa kalan fatar mu ya kusan zama d'aya sannan haka k'wayar idonmu?"

Murmushi yasmen tayi tace "yuhaana hak'ik'anin gaskiya naso ace nice mahaifiyarki da nafi kowa farin ciki dai wani baya haihuwat d'an wani and ai duk hasken fatana ban kai kj k'wayar ido kuma..."
Mirror d'in gabar motan ta saukar sannan ta saka yatsanta a cikin idanunta d'aya bayan d'aya ta cire blue din sannan ta juyo ta fuskanci yuhaana.

Zaro ido yuhaana tayi cike da al'ajabi duk da ta san wasu suna zaton eye lence take sawa amma bata tab'a zaton haka yake zama so natural ba.

"Yanzu kin yarda ni ba mahaifiyarki bace?

Sunkuyar da kai yuhaana tayi can ta d'ago tace "toh menene matsayinki a gidanmu menene dangantaka ta dake."
Hannunta ta me taushi ta saka tana share mata hawayen idanunta tace"ni auntynki ce k'anwar mahaifiya wacce take sonki fiye da yanda mahaifiyarki ke sonki."

Murmushi ne ya sub'ucewa yuhaana duk da halin da take ciki bata san lokacin da ta shige jikinta yau ta fara ganin matan nan amma taji wani irin soyayyanta a jininta rungumeta yasmen tayi had'e da runtse ido sosai take danne zuciyarta saboda ita d'in dakkakiyar macece.

D'an bubbuga bayanta tayi tace "ya isa haka." Ta raba jikinta da na ta.
Murmushu kwance a fuskanta tace"ki shiga gida haka i will come for you,ki cigaba da bin mahaifiyarki kina yi mata biyayya kinji ko d'iyata?"

Gyad'a mata kai tayi tace "toh aunty na gode,dai kinzo." Daga haka yasmen ta rankwafa ta bud'e mata k'ofar motan har ta sa kai zata fita yasmen ta ruk'o hannunta.

Juyowa tayi ta zuba mata ido fuskarta d'auke da alaman tambaya yasmen d'in ma ido ta zuba mata can kuma sai ta sakar mata murmushi "bye dear"
Murmushi yuhaana ma tayi tace "bye" da haka ta fita hannu suke ta d'agawa junansu har ta fita a layin.

Gefen titi ta samu ta yi parking kife kanta tayi jiki steering wheel ta fashe da wani irin kuka me tsuma rai.

Yau ganin yuhaana ya dawo mata da komi sabo
Shekaru kusan ishirin da biyu ya dawo mata kaman yau.
Wannan k'addara da ya shefesu su hudu koma fiye da haka.

Gani take babu wanda abun nan yafi shafa irinta ko ba komi yau Hajara da mukhtar sun mallaki juna  sun kasance a inuwa d'aya ita kuwa ta tashi a tutan babu.

Bata tab'a d'and'ana dad'in zama da masoyi ba bata san menene dad'in aure ba.
Yau ga yarintanta ya tafi a iska. Mukhtar bai kyautawa rayuwarta ba.

Sai da tayi kukanta me isanta sannan ta d'au hanyan zaria zuwa gida zata je ta samu mama ta sanar mata da halin fa da yuhaana take ciki a hannun mahaifiyarta duk da sun san cewa rashin lafiyar Hajaran ya sa tana gudun kowa tunda hasalima su suka sanar mata dalilinta kenan gida Nigeria.

Slow down tayi jin wayarta na ringing tattare giranta tayi ganin number mukhtar tana da numbobinsu dukka amma ba ta tunanin ta kira kowa da sabon layinta.

Amsa kiran tayi cike da sallama muryarta ya sanyaya
Rintse idonsa yayi tausayinta na ratsa zuciyarsa hakika har kullum yana tuna yasmen tana bashi tausayi yana ji a ranshi cewan bai kyauta mata.

"Hello mukhtar kana kan layin kuwa?" Ta tambaya.

Had'iye yawu yayi me kauri yace "eh Yasmen ina so mu had'u muyi magana ne dangane da yuhaana."

Ido ta zaro tace me ya sameta wani abu ne ya sameta?" Ta tambayeshu cike da tashin hankali

Da sauri yace "ah ah ba komi bane an sami change of plans ne?" Sauke ajiyan zuciya tayi hankalinta ya dan kwanta  "ka sameni a gidan mamah ina hanya." Daga haka ta kashe wayar.

Wayar ya tsurawa ido gidan maman yayi dan dama yana so ya sami maman shima yayi mata bayani.
Zuwan yasmen ya dan kwantar mishi da hankali yuhaana zata sami uwar da zata aurar da ita.

Kusan a tare suka isa gidan tana shiga bata jima ba shima ya shigo.
Gaisawa suka yi da mamah yace "mamah sai ga bakin cairo kuma?"

Tab'e baki yasmen tayi mama kam murmushi tayi tace "gata nan fa tana jin 'yar uwarta ba lafiya ta taho ba shiri sai kuma ta shigo tana mita da masifa akan mutuniyar tata."

Gyara zama papa yayi yace "wallahi fah mama nima haka naje na samesu suna fad'a bana ji ko gaisawa sunyi kuma duk akan yuhaana."

Girguza kai mama tayi tace "ai yasmen ta kasa yadda da ciwon Hajara gani take tsana ne bata san da ba haka mu'amalar su take ba,fatana Allah ya bawa Hajaran Lafiya kafin bikin yuhaanasun."

D'an zamowa daga kujerar da yake zaune yayi dan an tabo mishi inda yake mishi kaikayi yace"nima daman batun auren ne ya kawo ni."

Nan da nan gaban mama ya fad'i addua take Allah yasa ba wani mishkila aka samu ba yasmen ma  maida hankalinta kanshi tayi dan dama abinda take jira kenan tun shigowansa.

Kwashe abinda yake da shi yayi ya goya musu.
"Shi yasa nake so tazo nan ta zauna zuwa ranan d'aurin auren tunda ga yanda suke ita da mahaifiyarta ga kuma kwanakin k'ara k'aratowa yake babu wani shiri da ake yi har ita yuhaanan saboda jikin mahaifiyartata."

Cike da jin dad'i yuhaana tace "ai kuwa zanje in d'auko d'iyata zama bai ganni ba y'ata zata yi aure dole in shirya abata."

Dariya suka yi papa yace "kema ai ya kamata ki tsayar da miji kiyi aure yasmen girma fa ya kamaku ga y'arku na shirin shiga d'akin miji yasmen is high time."

Tamke fuska tayi kaman ba ita take dariya yanzu ba tace..........

Wai ya abun yake ne?


Sawwama Qawwama😘

YA ABUN YAKE?Where stories live. Discover now