💖YA ABIN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 24.
Vote and follow me on wattpad @sawwama14
Habibullah ne da musbahu suka shigo da gudu "an d'aura an d'aura! An d'aura auren aunty yuhaana da yaya Hassan!"
Abinda suke ihun fada kenan,momy ce ta fito daga d'akinta a kid'me dan ta san k'ullaliyar da suka k'ula tace "kai kai me kuke fad'a haka auran wa da wa aka d'aura."
Cikin hakki musbahu yace "wallahi mama auran yaya Hassan da aunty yuhaana ne!"
Pap ta buge bakinshi duk da kasancewar sa d'an lelenta "kai daina gaya min wannan k'anzon kuregen shi alhajin karen hauka ne ya cije sai da zai aikata wannan d'anyen aikin in kuwa cutar matarsa ce ta shafeshi na tab'in k'wak'walwa ba za ayi wannan haukan da ni ba yaje can ya nemarwa y'ar sa mata amma ba d'ana ba dudu nawa Hassan d'in yake?"
Wata mak'ociyarsu ce tace "haba maman Hassan ki dinga maganan masu hankali mana a wani addinin ne kika tab'a ganin an had'a y'an uwan jini aure ko dai ba mahaifinsu d'aya bane?" Ta tambayeta cike da son jin tsegumi dan suma y'am anguwan sun dad'e suna hasashen yuhaana ba y'ar gidan bace.
Wannan hayaniyar da ake yi ne yasa su yuhaana fitowa daga d'akinta suka tsaya cirko cirko suna sauraronsu cike da al'ajabin me ke faruwa banda aunty yasmen dake k'ok'arin mai da yuhaana cike dan ta cigaba da shiryata.
Momy na shirin yin magana papa da Hassan suka shigo sun sha manyan kaya iri d'aya farare tas dukkansu da babban riga fuskar nan tasu kaman gonan audiga hannunsu sark'e da na juna abinda yayi sanadiyar fad'uwar gaban yuhaana da wasu daga cikin mutanen dake cikin gidan.
Yuhaana fizge hannunta tayi daga cikin hannun yasmen ta nufi papa tsaye tayi a gabanshi bakinta na rawa tana son tayi magana amma ta tabbata babu kalmar da zata iya fitowa daga bakinta kuka ne zai kubce mata.
Ganinta papa da Hassan suka yi saurin tarbanta suka sa ta a tsakiya har lokacin fuskar Hassan d'auke yake da murmushi sab'anin papa da ya d'an sassauta fara'arsa yana kallonta yace "yuhaa am sorry" hawaye ne ya gangaro mata shikenan yau ta faru ta k'are yau papa ya tabbatar mata ba shine mahaifinta ba amma me yasa ba tayi farin ciki da sanin abinda ta dad'e da son sani ba the sad look on papa's eyes said it all. Tambayanta a nan wai Hassan? Ina Ibrahim papa zai d'aura mata aure da Hassan ko shima ya fasa ne papa ya yanke shawaran had'ata da d'ansa tunda ya san ba zata auru ba bata da asali ko ita d'in wacece ya abi...
Momy ce ta katse mata tunani "papa wai me nake ji ne haka wani d'anyen aiki ka aikata, akan me zaka had'a wanna abar aure da d'ana a wani hujjan?"
Zaro ido Hassan yayi jin batun momy sai kuma ya fashe da dariya wai ko momy kanta d'aya ta yaya za a had'ashi aure da sistern shi wani sa'in gani yake momy ne ke da damuwa a brain ba ummi ba oh shit sun confusing dinshi da mijin yuhaana ne lallai ma toh ko da sunan yazo d'aya ai kamata yayi su fara tunanin wani Alhassam din ba wai su jumping into conclusion ba duba da dangantakarsa da yuhaanan.
Hannun yuhaana papa ya rik'o zai fara tafiya momy tasha gabanshi ta rik'e qugu tace "nifa...."
Wata uban tsawa papa ya daka mata yace "ke dallah gafara can wani irin k'walk'walwa ce gareki baki da hankali ne ta yaya zan had'a y'ay'ana biyu aure sai kace kafirai ko kafiran ma basa wannan jagwalgwalan haba dan Allah ayi mutum babu tunani."
Da haka yaja hannun yuhaana da kanta ya k'ara shiga duhu in ba da Hassan aka d'aura mata aure ba toh da waye kenan papa dai shine mahaifinta? Allah ya shiryi zuciyarta me jajibe jajiben tunani.