💖YA ABIN YAKE? 💖
By Sawwama A.
Page 23.
Vote and follow me on wattpad @sawwama14
Ya dad'e yana tunanin yanda rayuwarsu ya kasance har sai da dare yayi sosai ya farga.
D'akin ummi ya lek'a ya samu tana bacci hankalinta kwance k'arasawa yayi har bakin gadon ya zauna addu'o'i ya tofa mata ya d'akko goran ruwan zamzam d'inta da aka jefa ganyen magarya aka karanta mata ayyatushifa a ciki.
Jikinta yabi ya shafe mata dashi kafin mannawa goshinta sumba ya ja mata bargo tsakar gidan ya nufa yana duddubawa ya rufe k'ofar gidan kasancewan gidan ba kowa momy ta tafi zamfara bikin k'awanta wajen sati guda kenan shi yasa ya kwashe yaran ya kai su gidansu kasancewar hutu ake.
Washegari da sassafe yuhaana da mariam suka fara shiri duk da yuhaana a k'ule take da ibrahim she is very disappointed in him ba ta xaci haka daga gareshi ba tayi tsamanin son gaskiya yake yi mata ashe ba abinda ke zuciyarsa ba kenan zata aure shi ne kawai yanzu dan kar ta mai da papa k'aramin mutum amma ba dan haka ba babu abinda zai sa ta aure shi
Alamun shigowan text a wayanta ya katse mata abinda take yi dubawa tayi taja tsaki dubanta mariam tayi tace "ke kuma da wa? Ba dai angon ba."
Kwali ta janyo tana zuba books d'inta a ciki tace "shine fah wai in yi hakuri he didnt mean all he said,ba wani Allah ne ya kamashi ya fad'i zuciyarsa dama can ba son gaskiya bane."
"Ah ah yuhaana kar kice haka dan kyautawa barrister bai kyauta ba amma ba hakane zai sa ki yanke mishi hukunci ba." Cewar maryam dake ware kayan yuhaana.
Shigowar kiran wayarsa ce ta hana yuhaana bata amsa wani tsakin taja tayi wurgi da wayan kan gado.
Mariam tace "in zamu wuce sai mu tsaya wajen haruna mu karb'i dinkunan mu ko?"
Dafe kai yuhaana tayi tace "kin ko san na manta ma da batun kayan Allah sa dai ya gama hidimar bikin ne ma bata gaba ns wallahi."Mariam na jan zip d'in babban akwatin yuhaana tace "yana ta kirana ya gama mu kawo mishi balance d'in mu karb'a nima ganin halin da kuke ciki yasa ban miki magana ba amma ya gama
Zama yuhaana tayi bakin gado tace "kinga ni na manta ma da balance dinshi gashi papa ya fita sai dai in mishi waya ya turo min ko transfer ne sai inyi wa harunan."
Gyad'a kai mariam tayi tace"hakan ma yayi,amm kin daure kinje kin gaida ummi kuwa?"
Rau rau yuhaana tayi da ido tace "mariam ina so inje amma tsoro nake ji bana son b'ata mata rai she makes it clear to me bata sona a kusa da ita,shi yasa kika ga na amince da tafiya zarian nan kuma baki ji papa yace in nesanta kaina da ita zuwa wani lokaci ba."
Haka suka cigaba da tattaunawa suna kintsawa..
Sunyi wanka suna sa kaya aunty yasmen tazo kaman yanda yuhaana ke kiranta barin su tayi su cigaba da shiri ta shiga d'akin ummi.Kwance ta sameta akan dogon kujeran palonta tana karanta hisnul muslim kaman yanda papa yace mata zama yasmen tayi a one sitter sai k'amshi ke tashi a jikinta..
Ko d'aga kai ummi bata yi ta kalleta ba murmushi yasmen tayi tace "hajara ya kike ya jiki?"
Murya ciki ciki ta amsa da "lafiya"
"Hmm hajara kenan nifa ba makiyiyarki bace ba kuma kishiyarki bace,gaskiya nake gaya miki akan d'iyar da ke kika haifeta...""Dakata yasmen ni ban d'aukeki kishiya ba ke kika d'aukeni a matsayin kishiya tunda na taka matsayin da ke baki taka na kad'aice da abinda kike so har da rabo,you can never change that babu abinda zaki iya yi akan haka na gaba yayi gaba yasmen!"
