Babi na 1

3.9K 193 1
                                    

Lab'e take a jikin d'aya daga cikin tagogin d'akin wanda ba marufi gareshi ba sai d'an ubansun kwalliyan da ke jikin shi kasantuwar cikin dare ne kuma wasu fitilu ne a kunne a gefe da gefen tagan ba kuma wannan tagar ne kad'ai ba har sauran ma haka suke, ginin gurin kuwa na k'asa ne amma me uban tsayi domin hawa hud'u ne da shi daga inda take ma kuma sannan shi kanshi wannan gini a cikin wani ginin yake abun dai ya k'ayatar da ka gani kasan masarauta ce babba ,domin ko ina zagaye yake da gagga - gaggan Fadawa masu ji da k'arfi a jika, gasu bak'ak'e ne na asali.......

"Ya zama dole mu raba Raheena da abunda ta Haifa dole!!! Domin kuwa muddin suka taso cikin wannan gida na alfarma toh lallai ba mu ba rawar gaban hantsi!!" Cewar d'aya daga cikin matan da ke zaune a d'akin kenan wanda kasancewar ta bak'a baka kallon komai na fuskarta se hak'oran ta domin ko Hasken ido bata da shi .
D'ayar kuma tace " eh wannan haka yake kin yi gaskiya Ubaidah!! Ai dole mu rabata da yaran da ta Haifa domin kuwa babu yadda za'a yi muda muka zo bamu zuba kwayaye ba sai wadda aka kawo ta a bayan mu! In muka yi wasa sarki duk zai tattara hankalin shi da tunanin shi ya bata mu kuma Mun zama gumaka !!"
Ubaidah tayi karaf tace " yo banda abunki Zulaikha ai aikin gama ya riga ya gama ! Mutumin da ya zama kamar tinkiya sai da tunanin ta fa yake tunani toh ai kuwa kinga bamu ga ta zama ba , dole ne mu d'au mataki! Ke nifa na ma kasa yin tunanin abu d'aya , shin bakya mamaki yadda ta haifo yaran nan duk farare sol kyawawa anya kuwa wannan harka mai martaba ba'a cuceshi da wani k'atulan mak'atulan d'in ba kuwa?"  Zulaikha tace
"yo toh wa ya sani ne abu a duhu? Ko da yake ita ai tsatson Indiyawa ce wata'kila kyaun ta suka biyo ko na iyayen ta!" Ubaidah ta murtuk'e fuska ga muni tace " kaji min Zulaikha da wata sabuwa ! Yo in ma hakan ne bakya tunanin wani daga dangin su Kedai kawai a bar kaza cikin gashin ta !!"

Duk maganganun nan da suke yi yana kunnen Shalini a yanda take a lab'en ta fara ja da baya a hankali hannayen ta biyu duk ta rufe bakinta da shi tana hawaye da gudu ta juya ta fita daga wannan 'bangaren ta nufi wani b'angare wanda shima duk irin wannan ginin ne ta banke wata k'ofa ta shige d'akin da gudu ta durk'usa gaban wani kyakkyawan gado wanda akayi shi da zinare da kuma azurfa sai zufa take yi jikinta na b'ari ,ta sa hannu tana shafa kan yaran da ke Kwance a kan gadon wanda basu wuce sati biyu da haihuwa ba ,kamannin su d'aya ne,babu abunda ya raba su.
"Y'ay'a na !! Na yi alk'awari bazan barku ku wulak'anta ba ni zan kula da ku in Allah ya yarda babu abunda zai same ku na cutarwa! Ta d'auke su duk ta rungume cikin sand'a ta fice daga wannan 'bangaren sai juye juye take yi har ta kai inda ake ajiye dawakai ta kunce guda daya ingarma fari da ruwan 'kasa jikin shi ,ta ajiye Yaron guda d'aya a 'kasa saida ta sab'a guda a baya sannan ta d'auki d'ayan ta haye dokin ta yi hanyar fita ba tare da ta bari mai gadi ko d'aya yaga fuskar ta ba...........

Gudu take tsakani da Allah har gari ya fara wayewa ta yi nisa sosai daga gari gashi kuma cikin HAMADA (DESERT) Suke tafiya bata ankara ba ta jiyo Hayaniyar dawakai daga chan bayanta sun cimmata ,tayi mamaki sosai yadda aka gano fitar ta har aka biyota kuma da ta lura da wad'anda suke zuwa sai taga ashe na hannun daman su Ubaidah ne.

GUGUWAR HAMADADonde viven las historias. Descúbrelo ahora