Page 1

4K 159 1
                                    

💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA💅🏼





     BY HAERMEEBRAERH




*Assalamu alaikum, makaranta novels dina ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke, saqon gaisuwa ta a gare ku ba shi da iyaka. Kamar yanda novels dina suka gabata guda biyu, MUGUN MIJI, AURI SAKI, n yi su ne akan yanda mazan wannan zamani ke cin kasuwa akan matan su, cikin kwanciyar hankali, ba tare da an dau mataki akan su ba,ko kuma in an dauka din ba zai taba goge azabar da suka ma matan nasu ba, wannan novel din shima kusan akan maza ne zan yi shi, domin labarai ne da ya hada na mata kala2, amma inshaa Allahu zan taqaita shi yanda saqon da muke son mu isar zai kai ga mazaje, yana da kyau ku dinga sharing irin wadannan labaran, ba kiga wani shiririta ki ta sharing va kina barin abu mai amfanin da zai iya gyara rayuwar wani.*

*kamar kullum ina mai roqon ku da tara novel ko baki karantawa wata qila gaba zaki so bi, dan wadda nake tura mata mutane ma yau da gobe ta qi wasa kar mu lalata mata waya😄 and in an ga abu mai amfani a kwafe, a wani wajen, dan Allah banda tambaya ta pc, wayata nada matsala tayu na gani kan na amsa sai aga kamar na share ne, amma network ko riqewar ta ne yasa ba a ga amsata ba. Na gode*




Page 1:




Kidane ke tashi kamar wajen zai fashe, madaidaicin parlour ne wanda iya ganina kayan maye ne a kan center table din, wadan da tinda nake ma ban taba ganin su ba balle sanin sunan su,  mata ne matasa su uku, wanda naji suna kiran kan su bestis,  kowacce in zata kira dayar su da besty take kiran ta, biyun su masu matsakaicin kyau,amma farare tass, sai dayar su wadda ta fisu kyau, farin fatar ta bai kai nasu ba, kuma ta fisu cika, ga shin ta irin na hausa fulani, saboda gyaran da yake sha ya kwanta har kafadun ta, ta dan zubo da shi ta gaban goshin ta, a buge take kwance a kujera, ko bude idon ta bata iyawa, hannun ta take son dagawa amma sai ta maida shi yaraff,bakin ta na motsawa, da kyar ta yunqura ta miqe ta shige bandakin dake cikin parlourn.

Dariya dayar su tayi, tace,

"Besty, kinga Besty Samha yanda ta tipse ko tafiyar ma kamar a taya ta, yau fa ta hau network kowa zai maida ta gida? Dan dai ba zan je ba na hadu da wannan shegen mijin Yayar ta ta, mayan mata,"

Dariya tai dayar cikin maye itama ta furta,

"Malika besty ai sai dai ta kwana anan kawai, dan nima ba zuwa zan ba, kwanaki dana maida ta, dik da mun dawo hayyacin mu guy dinnan fa nema yake ya haye ni, baqin dan iska ne, mara misali,"

Daga sama suka ji maganar ta,

"Shegu me kuke cewa? Ina jin ku, ai ku bari kawai, Yah Suhail, ya mugun maida ni kamar matar shi, Allah ne kawai bai....."

"Dakata Besty, in zaki shekara rantsuwa ba wanda zai yarda wannan dan akuyan bai hauki ba, ko qur'ani zaki dafa kuwa,ke dai kawai ai sha'ani, Allah ya kyauta,"

Wani baqin ciki ne ya kama ta, babban abinda ke damun ta kenan, sanin cewar kowa kallon da yake mata kenan ya sa take qara jin baqin ciki, da tsanar Mijin Yayar ta da Yayar ta ta ma, amma ba komai, Allah na nan.

Tsaki tai, ta ja doguwar rigar ta ta dora akan riga da wandon dake jikin ta, ta shige daya daga dakunan, ta kwanta.

Ba ita ta farka ba sai wajen isha'i, da gudu2 ta shiga wankata fito, qawayen nata na ta bacci, ta shirya ta aje masu note ta fice,shigewa mota tai bata zame ko ina ba sai unguwar Zoo road, dake garin kano, a wani gida mai babban gate ta tsaya, wanda da gani kasan gidan kudi yaji ko ta ina, parking motar tai ta fita,kanta a qasa, irin ladabin nan na masu shaye2,dakin ta tanufa, dan bata ji motsin kowa ba,ta san auntyn ta na daki ta kwanta, saboda bata dadewa batai bacci ba, in ko ta dade to ana dadi da Yah Suhail kenan, tana koyarwa a makarantar secondary ta Gyadi2, dan haka take bacci da wuri, ga gajiya gashi tana son ta tashi da wuri.

Da sauri ta shige dakin ta,ta yi wurgi da jakar ta, ta fara qoqarin cire rigar ta, tana cirewa ta cire ta cikin da bra din ta, dan so take ta sauya kaya tayi sallah ta kwanta itama.

Cikin sanda ya fito daga toilete din ta da ya shiga ya buya, ta baya taji hannayen shi akan qirjin ta, wani wawan ihu ta sake, yai maza ya juyo da ita ya toshe bakin ta da nashi, a yunwace yake tsotsar vakin ta, ita ko sai qoqarin kwace qirjin ta daya manna hannayen shi kamar a wajen aka halicce su take, cikin sa'a ta kama lips din shi ta dasa mashi wani cizo, taqi saki, sai da ya saka ihu, taji alamun jini a jiki, sannan ta sake.


Kuka ta fashe da shi, tana bin shi da kallon tsana,da qyama, da Allah wadai, shi ko fuskar shi tayu jawur saboda baqin cikin abinda ta masa.

Bai bata lokaci ba wajen damqota da gashin kan ta, ya wurga ta gadon, tana ganin ya fara qoqarin cire wandon shi ta ja rigar ta ta fita wajen dakin a guje, a palourn suk ci karo da yayar ta ta, kallon yayar tai ta daka mata harara ta saka rigar ta tayi waje a guje, kulle su tai ta wajen, da wani qarfe, ta zauna a bakin qofar tana ta kuka, wannan wace irin masifa ce? Ina ma tana da wajen zuwa; da ta bar gidannan ta koma, in tace zata var nan ta koma zaman kan ta ta qara vata wa kan ta suna akan wanda take ciki yanzu,ina zata? Wani tinani tai da sauri naga tana girgiza kan ta.

"Inaaa ba zai yu ba, Ya Allah gare ka nake neman tainako, Allah ka taimaken😭"


"Samha, Samhaa, ki bude qofar nan, nace ki bude qofar nan, kar ki bari na bude da kaina,"

Hararar qofar tai tayi tsaki, ta juyar da kan ta, ta kifa kan a cinyar ta, hawayen ta na zuba ta gefen idon ta.




Yaya Amatullah kuwa tana tsaye jikin dinning tana kallon yanda mijin ta ke rikice akan qanwar ta, baqin cikin dake zuciyar ta bai da iyaka, zuciyar ta ta bushe ko hawayen takaicin da take ciki babu, idon ta yayi jawur, farar fuskar ta kamar garwashi, gashin ta dake sosa mata dokin wuyan ta ta debe ta fara tafiya daki dan ta kwanta.

A iya ganina na rasa gane da Samha da Amatullah wayafi wani kyau, banbancin su daya ta gashin kan su, Samha tafi gashi me kyau, akan Amatullah, kuma da dikkan alamu gyara ne yasa hakan ba komai ba.

Gajiya yayi da bugawa ya koma, daki ya shige, ya tadda Amatullah a zaune a bakin gado, a lokacin taci kuka itana ta gode Allah, tinani daya ne ya sata kuka, tinanin da ke damun Samha kenan har ya sata kuka, tinani ne na ina zasu su tsira daga hannun wannan azzalumin?

Da sauri ta goge hawayen ta, ta gyara zaman ta,a tsorace ta kalle shi, ganin abinda yake yi, yasa kamar baiwa ta fara cire kayan ta tana kuka, isa tai wajen shi, shi kuma ya kashe fitila,ina ganin haka nace to sa idon baida amfani kenan bari na fece😏

Kukan ta kawai nake ji, wanda ashe ba ni daya nake jiyowa ba har Samha dake waje tana jiyowa, itama kukan take, qanqame jikin ta tayi, kamar me jin sanyi, daga baya na ga ta miqe, ta zare qarfen da take rufe qofa in irin haka ta faru, dan maboya ta masa ta musamman.

Kitchen ta nufa direct, ta dakko wuqa, dakin Yayar ta ta nufa, ta bude qofar, ta kunna fitilar dakin, a yanda ta gan su bai hana mata yin abinda tai niyya ba,wuqar ta caka masa ta baya, wata qara ya sake, ya sulale a wajen...............






*Hummmmmm wannan abun akwai rikici faaaa*

*Iya comment din ku iya typing dina, kunsan ina typing da yawa innaji comment sun min kadan za a ga dan neman lalacu wallah, 🤣*

MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now