💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*Aunty Rumaisa Allah ya raya Baby ya sa albarka, Allah ya qaro masu albarka, ba labarin ciki sai haihuwa🤣🙊 Allah ya raya Little Rumaisa❤💃🏻*
Page 23:
Bilkisu ce ta fito da murna, ta yi wanka tayi kwalliya da wata atampa mai adon ja da fari, bakin nan ya sha janbaki, an yi daurin zamani, tayi kyau sosai dan itan ma kyakkyawa ce barakallah, kamar iyayen ta da yayan nata, da gudu taje ta maqale shi, kamar zai koma, dariya sukai tayi,
"Yayana sannu da dawowa, kai dai ba za a ce maka ya hanya ba sai dai ya gajimare,"
"Hhhhh haka ne, gajimare na can na gudo na bar shi, ni da na koma kuma zan dan dade, inshaa Allahu,"
"Yah me yasa?"
"Bari su Abba suzo zakiji me yasa,"
Matsawa tai ta kai kunnen ta wajen bakin shi,
"Dan Allah dan fara fadamin kan su zo,"
"Kana fara fada mata munyi fushi bama.son ji, haka kuke sai ance abu sirri ne ko sai an hadu a fada kan mu zo ita ta sani,"
Tashi yayi tsaye cikin girmamawa, yana dariya yana sosa qeya, ya nufi mahaifin nashi, wanda na kasa gane tsufan shi, sannan Imaam waya dakko a tsakanin su, dan suna kama da shi shidin ma,mahaifin shi ke nuna masa ai da bai taso bama ya ci abincin shi, amma ya dafa kafadar shi, sannan ya shafi kan shi, ya dan rungume shi ta gefe, tare da sa masa albarka,
"Toh muna jiran muji me za a sanar damu ake hada asambili haka,"
Dariya sukayi shida Bilkisu, sannan ya dan sunkuyar da kai alamar kunya,
"Abba dama ina son na sanar daku cewar ammmm... immm... naaa yi mata inshaa Allahu,"
Tsalle Bilkisu tayi, sannan ta rungume shi, tana murna,
"Masha Allah, masha Allah, Allah mun gode maka, gaskiya mana yau murnar tafi ta kullum dan Abba,"
Sake sunkuyar da kan shi yayi, Abban na shafa qeyar tashi, dan ya hutar da shi, tinda ya zama masa kamar dabi'a, musamman in yana gaban mahaifin nashi.
Maman nashi shiru tayi, ba zaka gane meye afuskar ta ba, murna ko akasin haka, kula da hakan ne yasa suka kalle ta, kowa na tambayar ta dalilin shirun ta, wannan abun murna ya samu.
"Na maka murna sosai dana, Allah ya tabbatar da alkhairi, Allah kuma ya sanya albarka a ciki, nayi matuqar mamaki da ka fadi ka samu mata saboda na san yanda ka qi kowacce mace da muka zaba maka ko suka nuna suna son ka, saboda munyi burin kayi irin auren mu auren wuri, ga ka nan kaida Abban ka in ba wani ya sani ba zai ce kudin yaya da qani ne, ni kuwa ba mai cewa na haifi kamar ka, kuma gashi muna tare cikin so da qauna"
"Hakane Mama ai yanzu gashi na samo maki suruka kyakkyawa kuma mai ilimi, dan kuwa karatun likita take, tana qoqarin zama cikakkiyar likitan mata, inshaa Allahu,"
"Kaji abinda ya bata raina kenan, na taso da kai cikin kulawa da tattali, ina tsoron ka yi auren da ba za a daraja ka ba, ba zaka samu kulawa ba, ka auri mace me zuwa aiki ai kaga bamai kular min da kai, musamman in bata samu tarbiyya mai kyau ba, a dik sanda na tina zakayi aure hakan ta faru ina shiga damuwa,"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomantikLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.