Page 20

1K 52 0
                                    

💅🏼  MIJIN YA TA KO MIJINA  💅🏼







      BY HAERMEEBRAERH






Page 20:









Washegari suka tashi a tare suka shiga kitchen, suka taya Umma abinci, sunayi suna hira,anan suke bata labarin yanda suka hadu dikan su, ta tausaya masu sosai, kuma ta qara basu gudummawa sosai na yanda zasu qara nesanta kan su da shaye2, saboda matsalar da ake samu masu shaye2 zuciyar su na fara sanar da su, tinda suka fara fa ba zasu iya bari ba, kuma da dama basu samun goyon baya da kulawa daga wajen dangin su, sai kyara da tsangwama shike sake maida su ruwa.


Sunji dadin shawarwarin su sosai, bayan sun karya, Anwar ya tafi gidan shi, Fahad ya gyara inda yaji ciwo, bakin shi ya kumbura baya son ayi abin dariya, Maleeka data kula da haka sai tai ta labarai na abin dariya, ya riqe vakin shi yana yarfe hannu, nan ita da yaran zasu hadu suyi ta mashi dariya.

Sin yi qoqari suka maida yara makaranta tare da vada hakuri, sosai kan a yarda a karbe su.

♡♡♡♡♡♡♡




Amarci ake sha sosai a gidan Suhail, wata iriyar soyayya ce mai tsafta take wanzuwa a tsakanin su, ya sauya layin wayar shi saboda matan dayake hulda da su na yawan neman shi, ko turo masa hotunan su marasa kyaun gani, da sunan jan hankalin shi dan ya koma masu, Amatullah yanzu kawai yake gani.

Kwance suke da safe, kowa a cikin su yana jin qiwar ya fara tashi, in tace ya tashi ya bata abin karyawa yunwa take ji sai yace  ta ina zai tashi ta danne shi.

Tashi tayi, ta miqe, cikin ta ya dan turo gwanin sha'awa, hannayen ta ta dora akan qugun ta, tana masa kallon ka tashi ko wani abun ya biyo baya, sake jan pillow yayi, ya rungume, jikin shi rabi a rufe rabi a bude, kallon ta yake qasa2, qafarshi daya datake lilo ta jawo, sai da yaji ya kusa fadowa ya kame jikin shi,



"Tsaya2 dan Allah tsaya zan tashi, me za a dafa maki gimbiya?"

"To tashi, ni so nake na ci danwake da mai da yaji, da koko, mai dan tsami2,"

Zaro ido yayi, shi bai iya dama koko ba, kuma bai iya danwake ba,ya fada yayi laifi,

"To an gama, yanzu ki zauna,naje na dawo, amma bari na dan fara wanke baki kan na fita,"

"Dan Allah kayi sauri, ji nake kamar zan suma dan yunwa, kuma su nake so na fara ci,"

Fasa shiga bandakin yayi ya fice, yaje ya samu mai share2n parlourn su, ya roqe ta in ta iya danwake, ta tabbatar masa ta iya, roqon ta yayi akan ta koya masa, sannan ta tsaya ya kwaba ta gani in yayi, haka kuwa akai, a kan idon ta yayi komai, sai ga danwake ya hadu, ba laifi yayi kyau, ya soya mai, ya dakko kwalbar da yaji take, ya zuba mata a mazuban da suka dace, koko ne bai san ya zai ya samu ba, kai mata danwaken ya farayi, kamar wata tsohuwar mayya haka yawun ta ke tsinkewa, ta zauna a qasa, ta bude qafa ta fara ci, cema yayi yana zuwa, ya koma wajen megadin su, ya tambaye shi ina zai samu koko, ko kamu ya dama da kan shi, cewa yayi bari yaje ya siyo, kowanne aka samu zai kawo, Suhail ya jaddada masa yafi son ya siyo kamun.

Wajen minti goma,ruwa ya tafasa, har ya fara qasa dan bai saka da yawa ba, maigadi ya dawo, dauke da kamu a kwanon da Suhail ya bashi, nan da nan me aikin ta koya masa yanda zai dama,bayan ya dama yayi guda, saka abun burga miya tasa yayi na qarfe ya burge shi, nan ya yi daidai, ya dau madara d sugar ya nufi dakin, duk ya gaji, a lokacin da yake aiki. Sai jinjinama mata yake, amma a haka mata ke girki kala2, dan kawai su faranta ma maza, amma basu birge wasu mazan, gwanda shi dama yakan dan taya ta watarana, yu kam shi yayi dika, danwake kadai yayi, amma ji yake kamar yayi aikin gidan dika.

MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now