💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA. 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 8:
"Anya ba kiran sallah nake ji ba?"
"Kiran farko ne tabbas, ya kamata mu hakura haka muyi sallah sai mu dan taba bacci, in yaso in muka tashi sai mu ci gaba, ko ya kuka ce? Dan so nake na kwana biyu ban je gida ba,ba zan sake taya ta yin abincin da za a kai ma wannan banzan ba,"
"Hakan yayi, amma kan a kira a suba ki dan ci gaba mana,"
"Noooo ina son na gavatar da nafila, sannan na danyi karatu, lokacin ai baida yawa,"
Duka Samha ta dasama Ladeefa a karo na biyu,
"Tashi, daga cewa lokacin sallah yayi har kin fara bacci,"
"Wai ni me yasa kk raina ni a gidannan ne, ba zan kuma dan rintsa ba?"
"An raina kin bayan na girme ki, baccin me zaki kuma lokacin sallah yayi?"
Gyara kwanciyar ta zatai Samha ta miqe taja qafafun ta har qasan gado, sai da ta kaita bakin qofar fita a dakin ta sake ta ta ja qofar tai waje da gudu, kwafa Ladeefa tai ta miqe tana kade jikin ta, tana surutun zata kama Samha ne, zata gane bata da wayo, Maleeka dariya kawai take masu, ta raba ta gefen ta ta wuce alwala itama.
Sai da sukayi sallar asuba suka shiga kitchen dan dafa abin karyawa, dankalin hausa ne, suka fede samha ta yanka da dan girma,ta tafasa da gishiri, ta tsame, ta kada kwai ta saka masa attaruhu albasa da garlic, sai maggi da sauran kayan qamshi, ta dinga tsoma wannan dankalin a ruwan kwan, ta soya a cikin man da ta fara soya shi da albasa, nan danan gidan ya dau qamshi, Ladeefa mayyar nama, naman kaza ta diba ta wanke, ta zuba albasa mai yawa da garlic, ta dora, sannan ta zuba attaruhu, da ta jajjaga, da kayan qamshi, ta saka maggi, ta dora, daga Maleeka kuma ta hada masu Tea daya sha kayan qamshi sosai, kafin su gama Samha ta dora akan labarin nata, inda ta ci gaba da basu kabari.....
"Cikin qanqanin lokaci zance ya karade gari Amatullah zata auri mai kudi, gidan Inna ya sa aka sake katanga, aka qara dakuna a gidan, ya sa mata kujeru da kayan kallo, Kawu kuwa Allah kadai yasan iya kudin da ya ci a wajen Suhail, dan haka a kullum a qara zuga Amatullah yake akan ta yarda ta aure shi dan ta huta kowa ma ya huta, sannan yana qara tsorata ta da in a nan gidan zamu ci gaba da rayuwa irin zaman quncin da zamu ci gaba da fuskanta a hannun su, ba a bar Inna ba wajen sa ma Amatullah auren Suhail, sai da ya kai Inna ta fara nuna mana halin da bamu san ta da shi ba na kyara dan muji mun matsu ayi auren ne na tabbata,"
"Ba a jima ba Amatullah ta bada cikakkiyar yardar ta akan ayi auren kawai, aiko kamar wadan da suke jira su rabu da qaya ko auren bazawara,a kwana hudu aka kawo lefe, mai akwati sha biyu, nawa shida, wai yasan tana ji dani, nan da nan ba a rufa wata daya cikakke ba, aka fara shiryen daurin aure, Inna ta dage wajen gyara Amatullah, da farko dai haka naga tana tafasa ganyen garahuni, da ganyen gasaya, da magarya, da lalle kadan sosai ba mai yawa ba lallen, sai ta tafasa su in sun tafasa sai ta tace, ta zuba ruwan kal farin ta sa ta zauna a ciki, sannan in ta fito ta bata musk farin ta shafa,"
(Masu neman maganin infection ga wannan, tested and trusted, yana da kyau in mace tana gama al'ada tayi wannan hadin saboda magani ne sosai kuma yana dawo da darajar mace, dan Allah dan Allah banda magana ta pc, wallahi wayata ke da matsala, in aka min magana tayu na gani ban amsa a lokacin dana gani ba a ji haushi, in an sa'a ne nake amsawa direct ya tafi wasu sunce network ke sa hakan whatever dai ayi hakuri a tambayi wani a group ko a gida, na gode)
"Sannan Inna na dafa kabewa tai laushi ta dame da ludayi ta zuba dakakken citta da kaninfari, wataran ta saka su guda ta dafe in ta dahu sai ta cire su, ta dama ta saka madara, da zuma da garin ridi ta ba Amatullah, nima Amatullah ta ragen na sha, abun da dadi, musamman na dabino da ake hada mata, a cire kwallon a wanke a jiqa ya kwana biyu, a saka gero daya kwana a jiqe a markada, a saka madara da zuma, a bata ta shanye, gaskiya Inna tayi qoqarin gyara Amatullah, kamar mahaifiyar ta na raye indai ta nan ne, qawayen Inna sun kawo magunguna na ciyayi da ganyayyaki amma ta qi bata tace bata son ta ba ta su su lalata mata rayuwa da wuri, gwanda ta sha abubuwan gida,"
"A tare akai mana qunshi da gyaran gashin mu, lokacin bamu taba sa mai ba, dan haka lokacin da aka saka yayi kyau sosai yayi tsaho kuma da ban sha'awa, gidan mu ya cika da 'yan uwan su Maman mu na nesa dana kusa, akai ta koka rashn ta, har suka samu kuka,"
"Amatullah dani mun sakankance tare za a tare, saboda mun san alqawarin da mukai ma juna mu, dan haka muka sake jikin mu,kowa sai raqashewa yake dan Suhail ya sake bakin aljihu ana ta biki mai cike da ciye2 da shaye2 na kayan dadi,"
"Inna da Kawu ne suka tara mu, suka sanar damu, su suka ma Amatullah kayan daki, wanda sai da suka siyar da gadon su sannan suka hada kudin, ashe Suhai ne y yi komai, nan mukai ta kuka muna masu godiya"
"Yau aka daura aure, zuwa yamma za a kai amarya gidan ta, aiko ba qaramin kyau tai ba, kayana na hada nima, Inna da wasu 'yan uwan su suka mana bayani ba fa inda za a dani, sai amarya ta kwan ta hantse gidan ta, wata qila sai ta huta gidan miji, cike da tashin hankali muka kalle su, me sike fada, tabbb za a yi ta maga yanda za a raba mu yau, Kawu na gefe ya kallemu da gudu ya shiga tsakiyar mu yana haki,"
"Kar ku kuskura ku bar su su hade jikin su, in kuka bar su suka manne ko gum bai fisu mannuwa ba, ba wanda ya isa ya raba su, ku ja Babbar ai mota da ota ai masi daukam Amaryar dama an gama da su an basu ita sai tafiya,"
"Manyan matan unguwar dake unguwar mu na yanzu sune a matsayin 'yan uwan ango da suka zo daukan amarya, kuka muke ta zabgawa kamar dayar mu ta mutu, kukan rabamu da juna da akai muke, muna tinanin anya zamu sake haduwa kuwa?"
"In taqaita maku sai da mukao sati biyu bamu ga juna ba, ni kam harda qarin ruwa, ita kuwa taqi amincewa da shi saboda rabamu da akai,kullum tace in ta rufe ido gano ni take Kawu na son haike min, dan haka sai ta kasa zaune ta kasa tsaye."
"Ina zaune mun dawo asibiti, ina cin ayava, Suhail ya shigo cikn fushi, ya dakan tsawa, ko gaida Inna bai ba,"
"Ke hada kayan ki mu wuce, ki min saur kuma,"
"Lafiya dai ko Suhail"
"Inna ina fa lfy, Amatullah ta na can ba lfy wai na maida mata da qanwar ta, na rasa meke min dadi ni,"
"Ai ina jin zai kai ni wajen ta na shige daki na hada kayana, sauri2, na fito, bakina har kunne, ko ya taya ni daukan kayan mai nauyi haka ya wuce, na bude boot na.saka kayan na shiga gaba bayan ya bude, haka muka wuce sai gidan Amatullah, da suhail,"
"Muna shiga mukai arba da juna mu muka rungume juna muna murna harda kukan dadi,"
"Suhail ba kunya ya janye ni, ya kalle ta, yace ina alqawari na? Sauke kai naga tayi tana kallo na qasa2, nima kallon shi nayi ina neman qarin bayanin wanne alqawari kuma?..........
*pls manage this page, nayi ne dan cika alqawari amma wallah baccin yamma na son kama ni, a ban chocolate na sha na wartsake🤣, Thanks all for ur comments i love u all❤ dan Allah banda tambaya ta pc, ko da tambaya dan Allah a yita group, hakan ba wai wulaqanci bane kamar yanda wasu ke dauka, ni din ba kowan kowa bace ya dillaliyar ayaba, amma ina gudun kar ban amsa ba saboda wasu dalilai aga nan ma nayi shiru, thanks all*
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.