Page 14

1.1K 60 0
                                        

💅🏼  MIJIN YA TA KO MIJINA. 💅🏼










             BY HAERMEEBRAEH






Page 14:







Da sauri Maman ta ta je ta rungume ta, tana murna, sai qoqarin riqe kwallar dake barazanar balle mata take, Ladeefa kuwa kuka take sosai na farin cikin kasancewa da mahaifiyar ta,

"Mama ina Babana?"

"Baban ki na ciki,"

Da sauri ta saki Maman nata tayi hanyar dakin Mahaifin nata, a hanya sukayi karo, bai zato ba kawai yaga gudan jinin nashi, da sauri ya jata jikin su, ya rintse ido,


"Ji nake kamar bazan sake ganin ki ba a rayuwa ta, ashe da rabon zamu gana,nayi kewar ki matuqa, naso na bi ki qasar taku tinda kin maqale kullum sai waya, da alqawarin kina nan tafe amma shiru,"

Cikin kuka take magana,

"Babana na dawo ke nan ba zan sake komawa ba sai da izinin ka,"



"Habaaa bana yi sn kai ba ai kuma na hana ki bin mijin ki, zaki koma a duk sanda yaso,"

Sunkuyar da kai tayi, a zaton shi na kunya ne,janshi tai suka nufi parlour,inda kowa ke zaune, mahaifiyar ta ta kasa rife bakin ta saboda murna, Sammani kuwa a ranshi ya qudurta ba zai yi abinda suka shirya ba,dole zai fadi gaskiya, ko ba komai,a yanzu qungiyar su tayi qarfin da ko ina aka kaishi aka daure sai ya fito, (daurin mutum ba Sammani, amma ka sani daurin Allah na Allahn ne, ba mai fidda ka sai Allah din,dan haka ka tuba d kai da masu irin halin ka, ko Allah ya muku rahama ya sassauta maku, ko ya yafe maku baki daya).



"Lallai da dikkan alamu kina biyayyar aure, domin dik wannan sabbin abubuwan da kk gani gidannan Mijin ki shine ya ke mana har Hajji sai da ya kai mu, na ma zaci zami gan ki can, amma bamu gan ki ba sai da shi da abokin shi ne sula samu zuwa, yace makaranta kk, yanzu kina mataki na nawa kenan?"


Kuka take sosai saboda wannan dik qarya ne ai, amma still taji dadin yanda ya kula da mahaifan ta,



"Baba ina matakin qarshe, a bangaren medicine, ni da qawaye na, kasan karatun medicine bai da sauqi ko kadan, sai a wajen Allah, zaman mu waje daya bama yawace2 shine babban taimakon mu, yanzu haka.muna matakin qarshe, ba zai yu na zauna anan ba zan koma makaranta daya ce take da dauran shekara biyu,"



"Masha Allah, lallai ashe babbar likita muke magana da ita,"

"Inshaa Allahu, thanks tu Maleeka, da yayan ta,"

"Wace ce hakan?"

"Qawata ce Baba,"

"To Allah ya muku albarka dika, Allah ya saka ma ta da alkhairi,"

Daga nan Sammani ya gyara zama, ya yi gyaran murya tare da sa hannu shi wajen bakin shi, kamar mai shirin goge wani abun,



"Ammm Malam, kai mutumin kirki ne, haka yarinyar ka mutuniyar kirki ce, da dikkan alamu bata watsar da dikkan tarbiyyar da kuka mata ba, a qashin gaskiya ni da yarinyar ku bamuyi zaman aure ba, bamu zauna tare ba, tana garin kano tana karatun ta da qawayen ta, guda biyu, ta bar gidana ne tin lokacin data gano ni din maza nake bi,ma'ana ni din dan LUWADI ne, kuma har aure garen, ga shi nan, Sadam, shine wanda na aura a ranar da aka daura mana aure da  Ladeefa, Sadam shine wanda ya bude mata gida ta fita ba da sani na ba, munyi neman ta har mun gaji, kullum da Sadam kuke magana a madadin ta, kullum akan neman ta nake, ban same ta ba, bai shekaranjiya da ta ganmu a Mall ta bi bayan mu, yarana suka dakko ta na gan a she ita ce, na dakko ta yanzu.na dawo maku da yarinyar ku, ban taba dora mata idda ba, dan ban kusance ta ba, na sake ta saki uku ga ta nan, dan ko na zauna da ita ba abinda zata iya min, ko da nayi auren ne dan kare suna na, amma a yanzu danae tare da manyan qasar nan, ba wanda nake tsoro, ko ina za a je ina nan a kan bakana, bana son mata sai maza, na gode da qaunar da ka nuna min da fari ka auramin yarinyar ka daka fi so,"



MIJIN YA TA KO MIJINAWhere stories live. Discover now