💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA. 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
*HHHHH niyyata yau na dan maqale nima, tinda Ayusha taqi bamu JALILAH amma ba yawa zan maqale in ba a turo ba yau ma*
Page 9:
"Kallon shi naga Amatullah tayi ta sadda kai qasa, kama hannuna tai, ta kama akwatina zata kaini dakin da zai zama nawa ne, da qarfi ya fizge hannun ta, cike da fushi ya kalle ta,"
"Wai Amatu wannan wanne irin wulaqanci ne? Ya na cika maki alqawarin ki ke kin kasa cikan nawa, inq miki magana ma kina kama qanwar ki zaku wuce ku barni tsaye?"
"Cikin rawar jiki, da murya Amatullah tace,"
"Haba dan Allah, ka bari na kaita dakin ta mana, ko a nan zan cika maka alqawarin ne? Kuma dai ai bama wuce mu bar ta anan a tsaye ba ko,"
"Wani kallon da ban gama gane na meye b ya bini da shi, yana lashe lips din shi, sannan yace,"
"Dan taji meye? Ai ko bata fara ba yanzu gaba zata sani ne, muje, ke Samha, kinga wancan dakin? Shine naki, maza ja akwatin ki ki shiga, ki sake abin ki nan gidan kine kema, kamar yanda yake na yayar ki kinji?"
"Daga masa kai nayi, bai bamu damar zama da Amatullah ba ko mu shiga ta nuna min abubuwan da ban sani ba, dan tinda muke bamu taba shiga gida mai kyau ba musamman kamar wannan, haka na ja akwatina nai dakin, ban jima da shiga ba sosai, dan inajin ko minti biyar ban cika ba na fara jin kukan ta, naso na je naji ba'asi, amma na kyale; tinawa da nai nan fa gidan ta ne, kwantawa nai na rufe ido ina tinanin irin rayuwar da zamu yi a wannan gidan, sannan na dinga hango rayuwar da mukai a baya, fatana na samu na ci gaba da karatu na, inna karanci bangaren aikin asibiti wataqila zan fi samun kudi, ba irin tinanin da ban ba wanda zai kawon kudi inna kammala karatuna, daga baya na miqe na tura qofar dakin sosai dan na daina jiyo kukan Amatullah, ina gama tura qofar na shiga bandaki, na cire kayana na tattaba inda naga alamar pampo ne, na kunna ruwa, a sink, ya taru a kofin bandakin a haka na dinga wanka na na gama, nayi alwala, na fito, sauya kaya nayi, na ninke wancan, na zauna jiran ta ta shigo, ta nuna min gabas, ina zaune na zuba tagumi, naji an bude qofar, da sauri na kalli wajen, ganin shi nai yana wani murmushi cikin nutsuwa da jin annashuwa,"
"Kije yayar ki na neman ki, ni na fita,"
"To,shine abinda na iya furtawa, dan mamaki nake,shi yana murmushin jin dadi ita tana kuka,me kenan? Da sauri na fita, har yayi gaba naga ya dawo ya nuna min dakin, da sauri na isa, ina shiga na ganta daidai a gado, in ban bata gani ba, tsirara take, kuma cikin wani irin yanayi, da sauri na kulle idona nayi baya kadan, tana jin muryata na kira sunan ta ta ja mayafin gadon, da sauri,ta rufe jikin ta, umarni ta ban na fita, na so na mata musu amma na fita, dan ko ba komai na gane me ya faru,(a wannan lokacin ai yara qanana ma ba abinda ba su sani ba balle yar secondary),"
"Ina fita naji ta fashe da kukan takaici, jingina nayi a jikin bangon dakin, na rintse idona, ina jin zafin yanayin dana gan ta, ya gama abinda zai da ita ya five ya barta, Allah na nan,"
"Dakina na koma na zauna ina tinanin ina ya kamata ya zama gabas, ina ganowa na fara sallolina, bayan na idar na zauna ina addu'a, ban jima da zaman ba naji motsin qofar dakin da nake, idon ta ya kumbura ya yi sintim, fuskar ta tayi jawur,ga shatin yatsu nan manya, a kuncin ta, sai kaucewa take karna gani, d sauri na rungume ta ina shafa bayan ta, sake jikin ta tai a nawa tana kukan dake dukan qirjina ya tabo zuciyata nima hawayen nake, ba qaqqautawa,"
"Samha kar ki kuka, nima rashin sabo ne, kowacce mace sai ta wuce wannan siradin, fatana kawai dik abinda mike nema mu samu a wannan gidan, bana son ki saka kan ki a dikkan abinda zaki ji ko ki gani a gidannan, kome ke faruwa ki zama kurma ki zama makauniya, fatana kiyi karatu maruqa, ki jajirce tinda ni ya ce ba zai bari ina fita ba, so zan dora rai a kan ki, zaki iya min alqawarin tsayawa tsayin daka kiyi karatu, dan mu fita daga quncin da muke ciki?"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.