💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA. 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 11:
A baya2 suka dinga bin su, ba tare da sun gane bin nasu suke ba, can nesa da su suka tsaya, ganin sun tsaya a bakin gate din wani gida, mai gate irin mai qarafunan nan, unguwar ta manyan masu kudi ce, manya2n gidaje ne a wajen, ga shuke2, bayan sun shiga gidan, sukuma suka bi su da gudu, suna zuwa bakin qofar suka tsaya dn ba yanda za ai su iya shiga gidan, ba tare da an san d zuwan su ba, ta wajen suka karade gidan, suna leqe, can ta bayan gidan suka hango, maza kala2, da masu shigar 'yan daudu da qananan kaya, da masu wando kawai, sai wanda suka saka boxers suna ta yawo, kamar tsirara, Samha kam ta ga tashin hankali ganin maza haka kamar tsirara,har wani jiri taji na dibar ta, Maleeka ce ta kula da hakan, tace,
"Ya isa haka yanzu mu tafi mu zauna a mota mu dan jira, in basu fito ba muje gida mu yi shawarar yanda zamu tafi da lamarin cikn sauqi,"
Ladeefa kuwa kuka take sosai, dan ko ba komai har yanzu tana son Sammani, dama za a ce zai daina wannan abun ba abinda zai hana ta yafe masa su ci gaba da zama, amma da dikkan alama ya dade yana yi, tafya suk farayi, tsabar waiwaye da Samha take yi ta gurda qafa, qara ta saka mai qarfi, ta kama qafar ta ta, Maleeka ce ta toshe bakin ta, kusan a tare suka zaro ido, da sauri suka kama ta ta kafadun ta suka fara gudu, kan su kai hanyar barin wajen, wasu maza masu six packs sun leqo, suna ganin su Maleeka suka nufi wajen su, ba su tsaya ba suka diba da gudu, mazan na biye dasu, mota suka fada, Maleeka ta wuga Samha ta baya, ta bude gaba ta shige mazaunin Driver, tana ma Ladeefa ihun ta shige, cikin rashin sa'a kuwa suka riqe ta ta hannun riga, ihu ta sake, kan lokaci mai yawa mazan nan sun qaru, wasu sun.fito, Ladeefa na ganin haka ta ce ma Maleeka,
"Maleeka kuje zan zo ba abinda zasu min, kar ki bari a kama mu dika ba zan taba yafe maki ba kk bari suka kama ku, kije kawai i will be fyn,"
Cikin firgici da rashin sanin abin yi Maleeka ta taka motar zata wuce, maza uku suka tsaya gaban ta, a zaton su ko zata tsaya, yi tai da motar ta cikin su suka rabu kowa ya kauce, ta sa gudu, suka bar wajen da Samha, Samha na ta mata ihu akan kar su bar Ladefa a wajen,
"Shut up ! I said shut it up !! Ya kk so nayi? Na tsaya su kama mu dika? Kina ganin in suka kama mu dika akwai wanda ya san ina muke ne? Wa zai kawo mana dauki, plssss let me concentrate"
Shiru Samha tai bata taba jin ihun Maleeka cike da bacin rai irin na yau ba, nan da nan ta fara kuka, saboda kawai hango mazan nan take sun saka Ladeefa a gaba, Maleeka zuciyar ta tayi laushi, rasa ya zatai tayi, suna isa gida Maleeka tace ma Samha ta fito, nuna mata qafar ta tayi, kallon qafar tayi, ta kama qafar zata ja Samha tai ta ihu, amma haka Maleeka ta ja qafar, tana gama ja mata taji dama, ba kamar da ba, ciki suka shiga, Maleeka ta dakko mata doguwar riga ta saka, itama ta saka, nan suka yafa mayafin suka sake fita, wajen 'yan sanda suka nufa,daga kwatancen unguwar da gidan suka sallame su, wai ba zasuje ba, gidan da yaran manya da kuma manyan kan su ba abinda zasu iya yi.
Har dare suna yawo ba wanda ya taimaka masu, a lokacin har Maleeka kuka take, domin rashin sanin abin yi, gida suka kma,Maleeka ta roqi Samha akan ta taya ta kwana tsoro take ji.
Haka kuwa akai anan ta kwana.
♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Bayan tafiyar su Samha, mazan nan suka dauki Ladeefa kamar kaza suka shiga da ita gida, mazan dake ciki sunyi cirko2, suna jiran suji me ke faruwa, Sammani da budurwar shi suna can baya sosai, amma sai da Sammani ya gane ta da sauri ya dinga ratsa mutane yana zuwa inda yake hango Ladeefa.
![](https://img.wattpad.com/cover/171021441-288-k176848.jpg)
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.