💅🏼 MIJIN YA TA KO MIJINA 💅🏼
BY HAERMEEBRAERH
Page 5:
"Qarfe tara nema ashe yanzun na zaci dare yayi , tinda bamu tipse ba zan dora da labari na kawai, dan gobe gaskiya dole na hau.network,"
"Allah ya shirye ki besty,"
Tafawa sukai, suka dunguma suka shiga daki, Samha ce ta fara yo alwala, ta tada sallah, tana idar wa ta juya ta gan su suma sallar suke, bayan sun idar ne suka sauya zuwa kayan bacci,suka haye gado,
"Tabb yau a matse zamu kwana kenan, dik wadda ta makan qafa mintsini zai tada ta bacci"
"Dan Allah kar ki mintsinen i am allergic to mintsini,"
Dariya sukai, dan Ladeefa itace me abin dariyar cikin su, wai she is allergic to mintsini🤣 wayaga mero🙊
Bayan sun kwanta ne Ladeefa tayi serious, ta fara da ba su nata labarin.
"Besties kamar yanda kuka san suna na Ladeefa, to sunan Babana Alhaji Salis shu'aib, mahaifina dan boko ne,kuma yana da ilimin addini, yana aiki a jami'ar dake zari'a, mutane na girmama shi sosai, kamar sunga waliyyi, kullum suna tare da wani abokin shi Malam Sammani, Malam Sammani tuzuru ne babba, bai da mata, daga shi sai ran shi, kullum yana tare da Babana, suna abota ne kawai amma Babana ya girme shi nesa ba kusa ba, dan kuwa za a saka shi a sahun matasa, amma Baba abokin shi yake kiran shi, kuma in suna tare zaku yi shaidan abokan ne"
"A da da ina qarama ban san meke faruwa ba ban san so ba, amma na kan ga irin kallon da Sammani yake min, kamar yana nazari na in ya gan ni, yana yawan min kyauta, yana son yayi hira dani, a haka har shaquwa ta shiga tsakanin mu, Ummana bata hana ni zuwa wajen shi, Ummana Subai'a tana da kawaici da kunya, bata da shigemin, nima ni daya ce a wajen su,ta haifi wasu maza biyu kafin ni basu tsaya ba tin suna jarirai, dan haka wani sa'in dangin Babana da Kyauta suke kirana, dan dai bana so ne na san daya bini🙄"
"Ana haka na girma na kai matakin aji shida na secondary, Baba ya so na shiga jami'a nima kan ya min aure, amma Sammani na fada masa yana so na, ya janye wannan qudirin na shi, saboda yana son yaga abokin nashi ya yi aure, lokacin danaji na ji dadi sosai,kamar zan me, saboda nima a lokacin ina son shi sosai, muna ta murna, kamar wasu qananan yara dani da shi,cikin qanqanin lokaci aka saka ranar bikin mu, na sha gyara na amare ko ta ina, na sha kayan mata daga wajen dangin mahaifiya ta, ba na wasa ba, dan a ganin su za a kai ma tuzuru mata sai ta Allah,sai da ya zamana ina zaune zan dinga jin kamar motsi a qasana tsabar tsumuwa danai, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na je gidan miji,"
"Ranar biki an sha biki nera tai kuka, dangin Babana sunyi qoqari wajen taya Babana murnar aurar dani, sun kashe dukiya a gidan d aka kaini, ni da Umma munyi kuka sosai, na rabuwa da juna, kowa bai zaci zatai kuka a gaban kowa ba,saboda kunya da kawaicin ta,sai ga shi tana ta kuka, ana riqe ni ana riqe ta,haka aka kaini gidana mai matuqar kyau, sanda na shiga naga kyaun gidan sai na manta da kuka, na bude baki kallo, cikn raina ina yi ma iyaye na addu'ar alkhairi,"
"Bayan kowa ya watse nayi ta zuba ido ko zan ga ango, naji shiru, yau zai shogo, gobe ne, Allah masani, ganin bai zo ba kawai na cire mayafina nayi alwala nayi sallah, nayi addu'a na shafa, na nade abin sallah, na sauya kayana na haye gado na kwanta, na rufu har kaina saboda tsoron da nake ji, na kai qarfe daya idona biyu, ban san sanda bacci ya dauke ni ba,"
"Ban sani ba ko sai da nai baccin ya shigo ko ya jima da shigowa, amma dana farka na ga fitila a kashe, cikin sanda da tsoro na fita parlour, magana naji a wani daki na maza guda biyu, dan haka ban wani bata lokaci ba na bude qofar,a bakin qofa na yi karo da su, Sammani ya riqe masa hannu, daya dayan hannun na shi na qasan rigar shi, suna kallon juna,abun ya ban mamaki, meye haka, suna ganina suka ja baya da sauri, suna kame2, meke faruwa kenan hakan? Hakuri na basu na ja masu qofar, na koma, kaina ya daure sosai, me maza keyi da sassafiyar nan a daki daya kuma a wannan yanayin? Me ya hana ango kwana a dakin shi da matar shi sai da wani? Maza na ce subhanallah Allah ka yafeni, zato zunubi, wata qila ma dan uwan su ne ko abokin shi, ba irin uzurin da ban kaw m raina ba, dan n gujewa zargi,"
YOU ARE READING
MIJIN YA TA KO MIJINA
RomanceLabari ne da ya qunshi mata guda uku, wanda suke da tabo mai qona zuciyar su, da zuciyar mai karanta abinda ya faru da su a rayuwar su😢.